Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Article 370: Me ya sa ake samun ƙaruwar masu zama ƴan bindiga a yankin Kashmir na Pakistan?
- Marubuci, Daga Aamir Peerzada
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC a India
- An wallafa
A kullum Bashir Ahmad ya ga jini a bango, yakan tuna daren da aka halaka ɗan uwansa ɗan sanda a yankin Kashmir na Indiya.
A watan Yuni ne, Bashir yana ƙoƙarin yin bacci ya fara jin ƙarar harbin bindiga daga makwabta. Ya tashi ya daga kan gado ya bincika.
Amma ashe zai shiga wani yanayi - sai ga gawar ɗan uwansa kwance a ƙofar gidansa. Matarsa da ƴarsa a kusa da shi, jina-jina. Daga baya suka mutu.
"Wadannan harsasan cikin minti ɗaya suka tarwatsa faranni," in ji Bashir. "Mene ne laifinsu? babu komi."
Ƴan sanda sun ce ƴan tawaye ne suka kashe su. Jami'ai kamar ɗan uwan Bashir, Fahaz Ahmad Bhat sun sha fuskantar hare-hare a Kashmir, waɗanda suka addabi jami'an tsaron yankin.
"Waɗannan ne mutanen da wani ɓangare ke kiran ƴan sanda masu kwarmata bayanai," in ji Ajai Sahni, shugaban wata cibiyar nazarin tsaro a Delhi.
Ya kuma ƙara da cewa "iyalansu, sun fi fuskantar barazana da hatsari."
A ranar 5 Agustan 2019, Indiya ta janye ayar dokar 370 a kundin tsarin mulki, ta ƴancin Jammu da Kashmir da ta tabbatar. A wancan lokacin Firaminista Nerendra Modi na jam'iyyar BJP ta Hanidu mai mulki ya kare matakin inda ya ce ya zama dole domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki.
Amma bayan shekaru biyu, rikici ya ci gaba da ƙamari a yankin, inda jami'an ke cewa matasa na rungumar makamai.
An dade ana rikici kan mulkin Indiya a yankin Kashmir a 1989.
Amma masana na ganin tirjiyar na ƙara ƙarfi.
Yaki da rikici ya ɗaiɗaita yankin Kashmir tsawon gomman shekaru.
Dukkaninsu Indiya da Pakistan suna iƙirarin iko da yankin amma kuma suna iko da wasu sassan yankin. Ƙasashen masu makaman nukiliya sau biyu suna yaƙar juna kan yankin.
A tsawon shekaru, Indiya na zargi Pakistan da tursasa dubbam mayaƙa zuwa sassan iyaka domin haifar rashin zaman lafiya a yankunan da Indiya ke iko na Kashmir. Amma Islamabad ta musanta zargin.
Dangantaka tsakanin ƙasashen biyu ta daɗe da yin tsami amma sun kai wani matsayi lokacin da Delhi ta yi watsi da matsayin yankin a 2019.
Nerendra Modi ya tabbatar da matakinsa mai cike da ce-ce-ku-ce, yana mai cewa matsayin Kashmir ke ƙara rura wutar mayaƙa.
Ministoci daga ɓangaren gwamnatin BJP sun jaddada iƙirarinsa. Wasu sun kira matsayin Kashmir a matsayin babbar matsala, yayin da wasu suka jaddada cewa yanzu akwai zaman lafiya a Kashmir ba kamar shekarun baya ba.
Amma an ci gaba da kai hare-hare a yankin duk da jami'an tsaro sun ƙara ƙaimin yaƙar mayaƙa.
Tun 2019, gwamnati ta sauya ƴancin ƙadarori ga ƴan yankin, wanda ya haifar da zargi daga mutanen yankin. Mazauna yankin suna tsoron sabbin dokokin zasu sauya yankin da ke da yawan musulmi.
An dade Kashmir na adawa da yaƙin adawa da mulkin Indiya, kuma masana na ganin sauyin siyasar da aka samu ya ƙara fusata mutane.
Wani babban jami'in tsaro, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa daga cikin mayaƙa 200 a yankin, 80 daga cikinsu daga Pakistan ne kuma sama da 120 mayaka ne daga yankin.
"Tsakanin Janairu zuwa Yulin bana, ƴan Kashmir 76 sun ɗauki makamai kuma adadin na ƙara ƙaruwa," in ji shi.
Ya ce babu wani daga ƙasar waje da aka ƙara a cikin mayaƙan a Kashamir a bana.
Ba dukkanin mayaƙan da ke ɗauke da makamai ba suka fito daga ƙungiyoyin da aka sani. Wasunsu ba su da horo, wanda ke sa ake kashe su a artabu da jami'an tsaro.
Tun Janairun bana, mayaƙa 90 aka kashe a ɓarin wuta a Kashmir, kamar yadda alƙalumman gwamnati suka nuna. Yawancinsu mayaƙa ne daga yankin da ba su kai shekara 14 ba.
Masana tsaro sun ce faɗan kan iyaka mataki ne na korar mayaka zuwa tsaunikan yankin
Kakakin sojan India ya ce ba a rusa tsagaita wuta ba tun watan Fabrairu, saboda haka kuma shige da ficen kan iyaka ya yi sauki sosai.
Amma Bashir ya kasa samun kwanciyar hankali
"Dukkanin India da Pakistan suna wasa da rayuwarmu," in ji shi. "Ya kamata a samo mafita don bai kamata ana kshe ƴan Kashmir."