Za a fara kada kuri'a a zaben gwamnan jihar Anambra

An wallafa

Idan an jima kaɗan ne, za a buɗe rumfunan zaɓe 326 a krmr hukumar Ihiala ta jihar Anambra a Najeriya, domin kammala zaben gwamna da aka yi a karshen mako.

Jami'ar tattara sakamaon zaɓe, Farfesa Florence Banku Obi ta dakatar da aikin bayyana dan takarar da ya yi nasara a zaɓen gwamnan na jihar Anambara na ranar Asabar.

Har sai an kammala zaɓen ƙaramar hukumar Ihiala, wanda hukumar zaben INEC, ta gaza yi saboda wasu dalilai ciki har da batun tsaro, kamar yadda ta ce.

Sakamakon da ta rigaya ta sanar a ranar Lahadi ya nuna cewa ɗan takarar jam'iyyar APGA, Farfesa Charles Soludo ne ke kan gaba da ƙananan hukumomi guda 18.

Sai Mista Valentine Ozigbo na jam'iyyar PDP da ya samu ƙaramar hukuma ɗaya, yayin da Sanata Ifeanyi Ubah shi ma ke da ƙaramar hukuma ɗaya.

A ranar Lahadi aka sa ran za a sanar da sakamakon zaben baki daya da dan takarar da ya yi nasara, to amma daga bisani hakan ba ta samu ba.

Mai Magana da yawun hukumar Hajiya Zainab Aminu ta shaida wa BBC cewa matsalar tsaro ta janyo ba a yi zabe a karamar hukumar Ihiala ba.

''Hukumar zabe ta samu damar tattara sakamakon zaben kananan hukumomi 20 cikin 21 da ake da su a jihar Anambra.

Kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin kasa da na dokokin zabe, to dole a bai wa duk dan Najeriya da ya kai shekaru da cika ka'idojin zabe damar kada kuri'a dan haka muka ga dacewar a bai wa mutane damar kada kuri'a a wanna karamar hukuma guda daya wato Iyala mai runfunan zabe 326, domin su yi zaben nan.''

Tun da fari wasu rahotanni sun ce an dakatar da sanar da sakamakon zaben baki daya, saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba.

Amma Hajiya Zainab ta ce, babu wata matsala da aka samu, an dai tafi hutun minti 30 ne kamar yadda aka saba kafin a koma a ci gaba da sanar da sakamakon.

Daga nan ne a cewarta sai kuma batun rashin sakamakon karamar hukuma daya ya taso da dole a dakata har sai an samu cikakken sakamakon kananan hukumomi 21 kafin hukumar zabe INEC ta ci gaba da sanar da sakamakon da ayyana dan takarar da ya yi nasara.