Me ya sa ake samun rikici tsakanin tsoffin gwamnoni da wadanda ke kan mulki a Najeriya?

Sanata Danjuma Gobe da Gwamna Muhammadu Innuwa
Bayanan hoto, Sabanin da ake samu tsakanin tsohon gwamna da magajinsa kan kai matakin da ba sa ga maciji da juna
An wallafa

Rikicin siyasar baya-baya nan tsakanin gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa da tsohon gwamnan jihar Sanata Danjuma Goje ya sake tayar da tambayoyi ko mahawara tsakanin mutane a kan yawan sabanin da ake samu tsakanin tsofaffin gwamnoni da kuma wadanda suka gaji mulki daga hannunsu.

Ko da ya ke sabanin da ake samu tsakanin tsofaffin gwamnoni da wadanda suka gaji mulki daga hannunsu ba sabon abu ne a Najeriya, amma yana kawo cikas ga cigaba jiha da kuma mulkin dimokuradiyya , a cewar masu sharhi.

Ziyarar da tsohon gwamnan Gombe ya kai jihar ta haddasa rikici wadanda dukkan bangarorin biyu suka ɗora alhakinsa kan ɗaya ɓangaren.

Lamarin ya yi sanadin mutuwar akalla mutum biyar abinda da masu sharhin siyasa suka danganta da kokawar neman iko daga ɓangarorin biyu.

A baya an samu wasu tsofaffin gwamnonin da suka samu saɓani da waɗanda suka gaji mulki daga hannunsu, har ya kai matakin da ba sa ga maciji da juna.

Waɗannan jihohin sun hada da Kano da Kwara da Sokoto da Zamfara da Kaduna, inda tsofaffin gwamnonin suka raba gari da wadanda suka miƙa wa mulki.

Sai dai abin mamaki shi ne yanwacin gwamnonin da ke mulki yanzu a baya tsofaffin gwamnonin sun kasance iyayen gidansu a harkar siyasar cikin gida ko ta jiha.

'An ɗauki gwamna tamkar sarkin sarakuna'

Wasu masu sharhi sun ce wannan rikici ba abin mamaki ba ne, kuma sun alaƙanta matsalar a kan wasu abubuwa.

Dr Tukur Abdulkadir, malami ne a sashen kimiyyar siyasa a Jami'ar jihar Kaduna kuma ya ce an mayar da siyasar jiha ta gwamna, inda wasu suka ɗauki gwamnan a matsayin sarkin sarakuna watau Emperor.

A cewarsa, "Gwamna ya mayar da jiha jiharsa ce kawai, gidansa ne, kayansa ne kuma a ƙarshe wanda yake so shi ake bai wa tikitin jam'iyya kuma daga ƙarshe zai yi wahala ba shi yake cin zaɓe ba".

Masanin harkokin siyasar ya ce: "Saboda haka idan ɗan siyasa ya ɗauki jiha ta zama gidansa ko masauratarsa zai yi wahala a ce kuma daga ƙarshe ya ce zai iya haƙuri idan yaronsa da ya ɗora a kai ya yi ƙarfa-ƙarfa ya samu mulki sun wanye lafiya, saboda abin ba yaƙi ne na aƙida ba ko kishin kasa ko kuma burin yi wa jama'a hidima ba."

Masu sharhi kan harkokin siyasa saun ce babban burin tsofaffin gwamnonin shi ne su ci gaba da karfa-karfa da babakere a harkar siyasar jihohinsu "da su da 'yayansu da surukansu da kuma wadanda su ke shafafunsu da mai".

Wadannan abubuwa su ne suke haddasa matsaloli tsakanin 'uban gida da yaronsa' kuma masana sun ce zai yi wuya a daina idan ba a kawo ƙarshen siyasar uban gida a Najeriya ba.

Wannan layi ne

Mummunan sakamako

Sai dai duk da cewa babu illa idan ya kasance an bi ƙa'ida shugaba ya kasance yana aiki da na ƙasa da shi musamman idan wanda ya yi aiki da shi ne a baya kuma ya san ƙwarewarsa.

Masu sharhi sun bayar da misali da jihar Borno inda duk da yake Kashim Shettima ne uban gidan Gwamna Babagana Umara Zulum, amma kusan a fili a iya cewa ya kawar da kansa daga sha'anin mulkin jihar tun da ya sauka.

Amma a lokuta da dama bambance-bambancen da ake samu tsakanin uban gida da yaronsa a harkar siyasar jiha kan rikide zuwa tashin hankali, abin da kan janyo asasar dukiyoyi da rayuka.

Dr Tukur Abdulkadir ya ce: "Idan ana yi abin domin Allah, idan wanda ka goya mishi baya ya bijire maka, to shi ma abin da ya yi maka, za a zo a yi masa."

Mafita

Masana harkokin siyasa dai na ganin mafita ga wannan matsala ita ce a tsaftace hanyar da ake bi wajen fitar da ƴan takara musamman a harkar siyasar jiha, domin hakan ne zai sa a iya dawo da martabar siyasar cikin gida, ko da yake sun ce sai an yi da gaske idan ana son a samu ci gaba.

"Matukar 'yan siyasa masu mulki ba su dawo daga rakiyar sai da da bazar wane za a iya rawa ba to gaskiya ba za a samu ci gaba ba," in ji Dr Tukur.

Ya kara da cewa wannan matsalar za ta yi ƙamari yayin da zaɓen shekarar 2023 ke ƙara matsowa kusa, ganin cewa wasu iyayen gidan na siyasa za su so yin katsalandan a harkokin jihohinsu.

Wannan layi ne