Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Habasha: MDD ta yi kira a tsagaita wuta
Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kira da a kawo ƙarshen rikicin da ake yi a Habasha tare da kira ga dukkan ɓangarorin su kiyayi kalamai masu tunzuri.
A wata sanarwa da kwamitin ya fitar, ya kuma yi kira da a bayar da kariya ga fararen hula.
Wasu daga cikin mambobin kwamitin da suka haɗa da China da Rasha na kallon rikicin da aka shafe shekara guda ana gwabzawa a matsayin rikicin cikin gida, amma sun saka hannu kan wannan sanarwar inda suke buƙatar duka ɓangarorin su hau teburin sulhu su tattauna domin a tsagaita wuta.
Kwamitin ya kuma yi Allah-wadai da abin da ya kira tunzuri da kuma rabuwar kai.
Jakadan Mexico a Majalisar Ɗinkin Duniya Juan Ramon wanda a yanzu shi ne shugaban kwamitin tsaro na majalisar ya ce an ɗage tattaunawar da aka shirya yi a ranar Juma'a kan batun zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afrika zuwa ranar Litinin.
''Mambobin kwamitin tsaro sun nuna damuwa matuƙa kan ƙaruwar arangama da soji a arewacin Habasha. Mambobin wannan kwamitin sun nuna damuwa ƙwarai kan tasirin wannan rikici ga jama'ar da ke zaune a Habasha da kuma zaman lafiyar ƙasar da kuma yankin baki ɗaya."
Ƙarƙashin wata sabuwar dokar ta ɓaci da aka saka a Habasha, hukumomin ƙasar sun ce sun cafke mutane da dama da ke goyon bayan ƴan tawayen Tigray.
Wasu daga cikin ƴan Tigray ɗin na ƙorafin cewa ana yi wa iyalansu ɗauki ɗai-ɗai inda suke cewa ana yi musu hakan ne saboda ƙabilanci -amma gwamnatin ƙasar ta musanta hakan.
A halin yanzu ƴan tawayen Tigray ɗin na ci gaba da kusantar Addis Ababa babban birnin ƙasar. Yan tawayen Tigray din da wasu ƙungiyoyi takwas sun bayyana cewa sun yi wata haɗaka ta musamman domin hamɓarar da gwamnatin Firaiminista Abiy Ahmed ko ta halin ƙaƙa, wato ko da sulhu ko da ƙarfin tuwo.