Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Iran ta amince ta koma teburin sulhu don tattauna yarjejeniyar nukiliya
Iran ta amince ta ci gaba da tattaunawa a wannan watan kan batun farfaɗo da yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa a 2015. Wannan ce tattaunawa ta farko tun bayan da aka zaɓi shugaban ƙasar mai tsatsauran ra'ayi Ebrahim Raisi a watan Yuni.
Babban jami'in Iran ɗin wanda ke wakiltar ƙasar wurin tattaunawar Ali Baqeri Kani ya bayyana cewa gwamnatinsu ta amince a soma tattaunawar a ranar 29 ga watan Nuwamba.
Amurka ta janye daga wannan yarjejeniya ne tun a lokacin mulkin Shugaba Donald Trump, sai dai dama Amurkar ta ce akwai yiwuwar ta sake komawa domin cimma yarjejeniyar.
A halin yanzu dai gwamnatin Shugaba Joe Biden ta ce za halarci zaman wanda za a yi a Vienna tare da sauran waɗanda suka sa hannu a yarjejeniyar baya da suka haɗa da China da Birtaniya da Faransa da Jamus da Rasha.
Ned Price, wanda shi ne mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa za a yi saurin cimma wannan yarjejeniyar idan wakilan Iran da gaske suke yi.
Sai dai ya ƙara da cewa Amurka za ta so a ci gaba daga inda aka tsaya a tattaunawar da aka fara inda Amurkar dama ta janye jikinta ne bayan tattaunawa ta shida.
Ana sa ran Shugaban Iran Ebrahim Raisi zai ɗauki matakai masu tsauri kan yarjejeniyar.
Ƙasashen yammacin duniya sun shafe watanni suna kira ga Iran da ta koma kan teburin sulhu, inda suka rinƙa gargaɗin cewa matakin ci gaban da ƙasar ta samu a Inganta makamashin nukiliyarta ya wuce yadda aka ƙayyade mata a asalin yarjejeniyar da aka cimmawa.
A ƙarƙashin yarjejeniyar da aka cimma a 2015, Iran ta amince da taƙaita inganta sinadarin Uranium ɗinta wanda jama'ar ƙasa za su iya amfani da shi kuma za a iya amfani da sinadarin wajen haɗa makamin nukiliya, haka kuma an ƙayyade mata adadin Uranium din da za ta iya ajiyewa da kuma irin na'urorin da za ta iya amfani da su wajen inganta shi.
Haka zalika Iran ɗin ta amince da batun masu sa ido kan nukiliya na ƙasa da ƙasa su rinƙa zuwa dubiya, wanda hakan ya ja aka cire mata wasu takunkumai.
Sai dai Mista Trump ya fitar da Amurka daga wannan yarjejeniya a 2018 tare da saka sabbin takunkumai kan Iran ɗin bayan da Amurka ta kasa shawo kan Iran ɗin kan jingine shirinta na gwajin makamaki masu linzami da kuma shiga da Iran din take yi tsamo-tsamo a rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya.
Tun bayan da Amurka ta sake saka waɗannan takunkuman, Iran ta kasa samun cirar biliyoyin dalolinta da ke ajiye a bankunan ƙasashen waje.