Boji: Karen da ke karakaina a motocin haya a Istanbul ya yi farin jini a intanet

Boji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jirgin kasa da ke bin birnin shi ne ain hawa da Boji ya fi son amfani da shi
An wallafa

A kwanakin baya-baya nan masu amfani da jirgin kasa da ke zirga-zirga a Santabul na son su yi tozali da karen.

Karen titi kuma sunansa Boji wanda yake son amfani da sufurin jama'a a birnin mafi girma na Turkiyya.

Karen na son hawa motocin bas, jiragen ƙasa da jiragen ruwa.

Babu wanda ya san yadda ya koyi tafiya a tsarin sufurin jama'a. Sai dai wani direban motar safa wanda ya saba da Boji, ya ce halinsa na ladabi yayin hawa mota ya kamata ya zama abin koyi ga dukkan fasinjojin mutane.

Ya na son hawa jirgin kasa

Boji a jirgin kasa da ke Istanbul .

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Boji a cikin jirgin kasa

Boji ya ci gaba da jan hankalin mazauna Istanbul, yayin da kuma ya sa mutane da yawa mamakin yadda ya dauki dabi'ar tafiya ta wannan hanya.

Aylin Erol da ke aiki da kamfanin Metro Istanbul, ya ce bayan ganin hotunan karen da aka saka a shafukan sada zumunta, sun yanke shawarar sanya masa wata na'ura da ake kira microchip don gano ainihin inda ya je.

Sai dai karen ya ba su mamaki bayan da suka gano cewa Boji yana wucewa ta tashoshin jiragen kasa aƙalla 29 a kowace rana kuma yana iya tafiya mai tsawon kilomita 30 kowace rana.

Kasancewar Istanbul tsakanin gabar tekun Turai da Asiya, birnin na da tsarin jirgin ruwa mai sarkakiya, wanda wani bangare ne da Boji yake amfani da shi a koyaushe.

Ya na son hawan jirgin ruwa

Boji the street dog wanders around on a ferry in Istanbul

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ferries are an integral part of travelling in Istanbul

Har ma an gan shi a cikin teku yana balaguro zuwa tsibiran sarakunan da ke cikin Tekun Marmara, kusa da gabar tekun Istanbul.

Karbuwar da Boji ya samu na da alaka da shafin Twitter da aka kafa da sunansa.

Shafin @boji_ist ya tara mabiya sama da 90,000 tun lokacin da aka fara shi a watan Satumba.

"Ya san inda zai dosa. Ya san inda zai fita," in ji jami'in sufuri Aylin Erol.

"Kamar yana da manufa."

An saka masa wata na'ura

Wani ma'aikacin karamar hukuma ne ya kula da lafiyar Boji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mahukuntan birnin na bin diddigin Biji da lafiyarsa ta hanyar amfani da wata naura da aka saka masa

An yi wa Boji allurar riga-kafi domin kiyaye shi da sauran mutanen da ke kusa da shi.

Na'urar da aka saka masa tana aiki ne da manhajar waya wadda take ba mahukunta damar bin diddigin lafiyarsa.

Ma'aikatan sufuri suna tabbatar da cewa ya ci abinci sosai kuma ya sha ruwa. Haka kuma wani likitan dabbobi na gwamnati yana ganinsa akai-akai.

Wani sako da aka wallafa a ranar 11 ga Oktoba a shafinsa na Twitter ya nuna wani hoton bidiyo da ke nuna nauyinsa ya kai kilogiram 42, inda ya ce ya dan yi nauyi.

Yadda ma'aikatan sufuri suka ba shi suna

Dangane da bayanai daga mai bin diddigin, yanayin jigilar da Boji ya fi so shi ne jirgin da ke zirga-zirga a cikin birnin.

Wanda ya dace da wata halitta wadda sunanta ta fito daga fasahar dogo.

Boji ita ce kalmar Turkanci ga "bogie", wani tsari da ke da ƙafafu a ƙarƙashin jirgin ƙasa

Da alama, haka ya samu sunansa, sai ma'aikatan sufuri suka fara kiransa da Boji, bayan da aka yi ta ganinsa a saman taraguna

Ya shahara sosai

Boji ya zauna kusa da wata fasinja

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana ganin Boji shi ne karen da aka fi daukar hotonsa a Istanbul

Tunda ya zama sananniyar fuska, Boji yanzu ya samun fasinjoji da ke gaisawa da shi ta tausasawa, ko kuma daukar hoton selfie tare.

A cewar ma'aikatar kula da dabbobi ta karamar hukumar Istanbul, kyanwa da karnuka sama da 300,000, suke zama a birnin amma wasu na ganin wannan kiyasin ra'ayin mazan jiya ne.

Dabbobin da ba su da wuri zama lamari ne mai jan hankalin mazauna Istanbul.

Boji the street dog walks on a subway platform in Istanbul

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutum miliyan 15 ke amfani da fanin sufurin Istabul

A cikin shekarun 1990, mahukatan birnin sun aika da wata tawaga domin magance yawan kyanwa da karnuka.

Amma bayan da jama'a suka koka, an yi watsi da wannan aiki.

Yanzu jami'an karamar hukumar suna kama dabbobi ne kawai don a yi musu alluran riga-kafi, da kuma magance duk wata matsala ta likita.

An sanya wata shaida a kunnen su domin tantancewa kuma ana sakin dabbobin zuwa inda aka gano su.

Fasinja ne mai ladabi

Boji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Boji

Tabbas Boji na jan hakanlin mutane sosai a Istanbul.

"Kuna hau jirgin, kwatsam, kuna ganin Boji," in ji Aylin Erol.

"Murmushi kawai za ka yi a lokacin, da gaske.

"Wannan shine abin da Boji ya ke kawo wa 'yan Istanbul. Yana tunatar da mu cewa har yanzu za mu iya jin daɗin Istanbul yayin da muke harkokinmu," in ji Aylin Erol.