Kayatattun hotunan Afrika 22-28 Oktoba 2021: Zakin da aka ceto da kuma kyaututtuka

An wallafa

Mun zaƙulo muku ƙayatattun hotunan abubuwan da suka faru a Afrika da na wasu ƴan Afirkan a wasu sassan duniya.

Short presentational grey line
Boys run past a bright mural of children wearing face masks.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Laraba kenan inda wasu yara ke guje-guje a gaban zanen Senzart911 da ke Soweto
A woman stands next to a large mesh sculpture of human hands.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A nan kuma an sassaka hannaye da suka yi kama da tullayen Giza da ke Masar inda za a yi wani bikin zane-zane na duniya.
Nigerian officials place their hands on the bronze cockerel.

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, A ranar Laraba lokacin da jami'an Najeriya ke karbar zakaran tagulla da dakarun Burtaniya suka sace a shekarar 1897 a Benin
Visitors look at doors of King Glele's Palace (1880-1889).

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A nan ma ranar Talata ne a wani gidan yawon bude da ke Paris, inda wasu ke kallon wata kofar gidan sarautar Dahomey a karni na 19. Yanzu haka ana shirin mayar da kofar da aka sace.
A young boy plants a tree seedling in the ground.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan yaron ya shiga sahun sauran mutanen da ke dasa itatuwa a dajin Mau da ke Kenya.
A woman holds the Golden Stallion of Yennenga trophy at the Palais des Sports in Ouagadougou.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Burkina Faso kenan yayin da aka dauko kambun fim mafi shahara na Fespaco, wanda fim din The Gravedigger's Wife ya lashe.
Tsitsi Dangarembga and her husband Olaf Koschke chat and smile.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Marubuciyar nan ƴar Zimbabwe Tsitsi Dangarembga tare da mijinta a birnin Frankfurt a ranar Lahadi, inda ta lashe kyautar bikin ƙayatattun litattafai ta German Book Trade's Peace Prize.
A lion is seen behind the bars of the cage it is travelling in.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani zaki kenan da aka ceto daga Rasha aka kuma kai shi Tanzania ranar Talata don duba lafiyarsa.
The owner inspects the damage at his house in Mossikro, Abidjan, after flooding caused by heavy rains, which left at least 4 people dead.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Barnar da ta auku kenan bayan mummunar ambaliya a Abidjan ranar Asabar.
Sudanese people block roads and protest against Monday's coup.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Talata dubbai sun cigaba da zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi a Sudan, inda ake shirin gudanar da gagarumin gangami a ranar Asabar.