Fitaccen marubuci kuma ɗan wasan Hausa Kasagi ya rasu

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon hirar da muka yi da shi kwanakin baya:

Fitaccen marubuci kuma ɗan wasan kwaikwayo na Hausa, Alhaji Umaru Ɗanjuma wanda aka fi sani da Kasagi, ya rasu.

Ya rasu ne a birnin Katsina da ke arewacin Najeriya ranar Juma'a.

Marigayin ya yi fice a fannin rubutun Hausa da wasan kwaikwaiyo, kusan a iya cewa su ne na farko-farko a ƴan wasan Hausa.

Haka kuma, shi ya rubuta sanannen littafin Hausa na Kulɓa Na Ɓarna.

An haife shi ya birnin Katsina a shekarar 1950.

Ya yi karatu a Najeriya da Ingila, inda ya ware a fannin fina-finai.

Ya bar mata biyu da 'ya'ya 13.