Ali al-Nimr: Yaron da Saudiyya ta yafe wa bayan yanke masa hukuncin rataya

Photo of Ali al-Nimr following his release from prison in Saudi Arabia

Asalin hoton, Ja'afar B Al Nemer

Bayanan hoto, Iyalan Ali al-Nimr's sun wallafa hotonsa bayan sakinsa daga gidan yari a ranar Laraba
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Hukumomin Saudiyya sun saki wani mutum da a baya aka yanke masa hukuncin kisa kan laifukan da suka shafi zanga-zanga a lokacin da yake yaro, a wani lamari da ya jawo suka da ce-ce-ku-ce daga ƙasashen duniya.

Shekarar Ali al-Nimr 17 a lokacin da aka tsare shi a shekarar 2012 yayin wasu jerin zanga-zangar da ke adawa da gwamnati da mabiya Shi'a da ba su da yawa a ƙasar suka yi.

A shekarar 2014, wata kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar "gicciye shi" - da sare masa kai inda daga bisani kuma za a bayyana wa mutane gawarsa su gani.

A watan Fabrairu ne aka soke zartar da hukuncin bayan da sarki ya kawo ƙarshen hukuncin kisa ga laifukan da yara suka aikata.

Saudiyya na daga cikin ƙasashen da suka fi aiwatar da hukuncin kisa a duniya. A tsakanin watan Janairu da Yuli an yanke wa a ƙalla mutum 40 hukunci kisa a ƙasar - inda ya fi waɗanda aka aiwatar a bara kawai yawa, ta faɗa a lokacin da ta karɓi baƙuncin shugabannin ƙasashen G20.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

1px transparent line

Ali al-Nimr ɗan ɗan uwan fitaccen malamin Shia ɗinnan nan ne Sheikh Nimr al-Nimr, wanda hukumomin Saudiyya suka yanke masa hukuncin kisa bisa laifukan ta'addanci a shekarar 2016.

Shehin malamin fitaccen mai goyon bayan juyin juya halin da aka yi a ƙasashen Larabawa ne da ya jawo aka yi irinsa a gabashin Saudiyya a shekarar 2011. Mabiya shia na yankin, waɗanda suka daɗe suna ƙorafin cewa masarautar Saudiyya na nuna musu wariya.

An kama Ali al-Nimr a ɗaya daga cikin irin waɗannan zanga-zanga a watan Fabrairun 2012 kuma wata kotun laifukan ta'addanci ta musamman ta kama shi da laifin "bujirewa shugaba," yana ci gaba da iface-ifacen nuna adawa da masarautar da kuma kai bwa ƴan sanda hari da duwatsu.

Ya yi watsi da tuhume-tuhumen tare da shaida wa kotun cewa jami'an tsaro ne suka tilasta masa amsa laifinsa ta hanyar azabtar da shi.

Wata huɗu bayan nan, wannan kotun ta sake yanke wa wasu matasa ƴan shia biyu hukuncin kisa, kan samun su da laifi irin wancan na hannu a zanga-zanga.

Abdullah al-Zaher da Dawood al-Marhoun na da shekaru 15 da 17 a lokacin da aka tsare su, sannan sun ce an yi ta dukansu har sai da suka amsa laifukan.

Duk da roƙon a yafe musu da iyalansu da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan adam suka dinga yi, an ci gaba da aijye su suna jiran zartar da hukuncin kisan har sai zuwa farkon shekarar nan, a lokacin da hukumar kar hakkin dan adam ta Saudiyya ta sanar da cewa an soke hukuncin kisan aka maye shi da ɗaurin shekara 10 a gidan yari.

Hukumar ta kafa hujja da wata doka ta 2018 da ta haramta zartar da hukuncin kisa kan waɗanda suka aikata laifuka suna yara a wasu lokutan.

Duk da cewa an saki Ali al-Nimr daga gidan yari a ranar Laraba, an ci gaba da tsare Abdullah al-Zaher da Dawood al-Marhoun, a cewar wata kungiya mai adawa da aiwatar da hukuncin kisa.

Shugaban kungiyar Maya Foa ya kira sakin al-Nimr da aka yi da wata "alama ta ci gaba," amma ya yi gargaɗi cewa har yanzu Saudiyya tana yanke hukuncin kisa kan laifukan da yara suka yi.

A watan Yuni, an yanke wa wani mutum hukunci kan laifuka masu laƙa da zanga-zanga a lokacin da yake yaro kuma an zartar da hukuncin duk da haramcin hakan da aka sanya.

Mustafa al-Darwish, wanda aka kama shi a lokacin yana ɗan shekara 17 a 2015, ya ce an azabtar da shi don tursasa masa ya amsa laifin.

Sannan akwai wani yaro Abdullah al-Howaiti mai shekara 19, da aka kama da laifin satar gwal a wani shago tare da harbe wani ɗan sanda lokacin yana da shekara 14, an yanke masa hukuncin kisa kuma yana kan layin jira a zartar da hukuncin a yanzu.