Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hikayata 2021: Alƙalan gasar sun fara aikin fitar da gwarazan gasar
Alƙalan gasar rubutun ƙagaggun labarai ta mata zalla wato Hikayata na tafka muhawara domin fitar da labaran da suka yi nasara daga cikin labaran da aka shigar a bana.
Hakan na nufin alƙalan na tattaunawa domin fitar da labarin da ya yi na ɗaya, sannan za su zaɓi wanda ya yi na biyu da na uku. Haka kuma za su fitar da labarai 12 da suka cancanci yabo.
An turo mana ɗaruruwan labarai a gasar ta Hikayata a bana.
Alƙalan gasar na bana su ne Dokta Hauwa Muhammad Bugaje, masaniyar adabin Hausa kuma malama a sashen nazarin Harsuna a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya; Malam Is'haq Idris Guiɓi, masharhanci kuma masanin harshen Hausa kuma malami a Kwalejin Fasaha na Tarayya da ke Kaduna; sai kuma Zahra'u Ibrahim Waya, masaniyar al'adu da harshen Hausa a Jami'ar Bayero da ke Kano.
Idan an jima a yau ne ake sa ran alƙalan za su sanar da labarai uku da suka yi zarra wadanda kuma a cikinsu ne za a fitar da marubuciyar da za ta zama Gwarzuwar Hikayata ta 2021.
Za a sanar da gwarzuwar ne a wani biki da BBC za ta gudanar a Abuja a ƙarshen watan Nuwamba.
Wannan ne karo na shida na gasar ta mata zalla wadda aka fara a shekarar 2016.
A shekarar da aka fara gasar, Aisha Sabitu ce ta zama gwarzuwar gasar, a 2017 Maimuna S Beli ce ta amshi kyautar, a shekarar 2018 Safiyya Jibril Abubakar ce ta yi nasara sai a shekarar 2019 inda Safiyya Ahmed ta zama gwarzuwar Hikayata.
A shekarar 2020, Maryam Umar ce ta karɓi lambar yabo ta gwarzuwar Hikayata da labarinta mai suna 'Rai da Cuta' inda BBC ta ba ta kyautar dalar Amurka 2,000.
Ga labarai 25 ɗin da alƙalan suke muhawara a kansu:
- Halacci
- Buɗaɗɗiyar Wasiƙa
- Ramin Ƙarya
- Sanin Ya Kamata
- Ɗan Hakin Da Ka Raina
- Daga Allah Ne
- Haƙƙina
- Baƙin Haure
- Ramat
- Uwar Marayu
- Lanti
- Butulci
- Rai Da Buri
- Tambari
- Kuɓuta
- Ba Maita Ba Ce
- Duniyar Sama
- Mataccen Alƙawari
- Yadda Dillin Ta Kan Yi Dillin...
- Wanda Bai Ji Bari Ba...
- Tun Ran Gini...
- Darasi
- Sai A Lahira!
- Uwar Jahilai
- Fagen Daga
Ƙarin haske
A cikin waɗannan labarai 25 da alƙalan za su duba, za su fitar da guda uku da suka yi zarra wato wanda za su yi na ɗaya da na biyu da na uku.
Sannan za su fitar da labarai 12 da suka cancanci yabo. Wannan na nufin cewa a cikin labari 25 ɗin guda 15 ne kawai za su tsallaka kuma su ne za a riƙa karantowa a shirye-shiryen BBC na rediyo, a makonnin da za su biyo bikin karrama gwarazan da za a yi a Abuja.