Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sanata Ndume: A yi bincike a kan kasafin kudin kashewa na yau da kullum
A Najeriya shugaban kwamitin sa ido a kan al'amuran albashin ma'aikatan gwamnatin tarayya da kuma ayyuka na yau da kullum a majalisar dokokin kasar, ya yi kira da a gudanar da bincike game da makudan kudin da aka ce an kebewa bangaren al'bashi da ayyuka na yau da kullum a cikin kasafin kudin shekara ta 2022.
Sanata Muhammad Ali Ndume, ya ce ba a dauki sabbin ma'aikata ba tun daga shekarar 2018 , sannan kuma ba a karawa ma'aikata albashi ba.
Amma yawan kudin da aka warewa bangaren ya karu daga naira Tiriliyan fiye da uku zuwa sama da naira tiriliyan fiye da shida.
Sanata Ndume, ya ce shi ya lura, kuma sauran 'yan majalisar ma da ya yi magana da su, sun lura cewa albashi na karuwa amma kuma ba a daukar ma'aikata.
Ya ce, "Abin da nake tambaya shi ne ya za a yi ace kudin kashewar yau da kullum sai karuwa ya ke, bayan kuma ba a daukar ma'aikata, sannan kuma tun bayan bullar annobar korona ma'aikata da yawa ba sa zuwa aiki".
Saboda mafi yawan ma'aikatan daga mataki na 12 zuwa kasa basa zuwa aiki, to dole kudin kashewa ya ragu, amma kuma sai gashi a kasafin kudin bana an kara bangaren kudin, in ji Ndume.
Dan majalisar dattijan ya ce, shi fa kudin kashewa na yau da kullum sune wadanda ake amfani da su wajen albashin ma'aikata da kudin sayen mai na motocin ma'aikatu da kudin alawus na ma'aikata da dai sauransu.
To idan har ba a daukar ma'aikata kuma da yawa daga cikin ma'ikatan basa zuwa aiki ai dole kudi suyi rara, kuma idan an kara su a kasafin kudin bana me za a yi da su, in ji Ndume.
Sanatan ya ce, dole a zauna ayi nazari aga ina kudin da aka warewa wannan fannin ke zuwa? dole ayi bincike.
Ya ce, bincike shi ne abin da yakamata ayi aga me yasa kudaden kashewa na yau da kullum ke karuwa bayan kuma an shafe shekaru fiye da uku ba a dauki ma'aikata ba?.