Shari'ar Maina: Kotu ta umarci a tsare Sanata Ndume bayan kasa kawo Maina

An wallafa

Wata babbar kotun tarayya a Najeriya ta bayar da umarnin tsare Sanata Mohammed Ali Ndume a gidan yarin Kuje saboda kasa kai tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho na Najeriya garambawul, Abdulrasheed Maina.

Ndume, wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawan kasar, shi ya tsaya wa Maina aka bayar da belinsa bisa tuhumarsa da laifin almundahana. Amma Maina ya kasa bayyana gaban kotu domin ci gaba da shari'arsa.

Alƙalin kotun Justice Okon Abang ya bayar da umarnin a tsare Ali Ndume har sai ya cika sharuɗan belin.

Kotun ta kuma umarci gwamnatin tarayya ta sayar da gidan Sanata Ndume da ke Asokoro a Abuja domin fitar da kuɗin da aka ƙayyade na belin naira miliyan 500.

Lauyan Ndume Marcel Oru ya ce za su ƙalubalanci hukuncin na kotu. An ɗage shari'ar Maina zuwa ranar 24 ga watan Nuwamba.

Waiwaye

Sau uku kenan a jere ana ɗage shari'ar zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban kwamitin fansho a Najeriya na Pension Reformed Task Force (PRTT) - wanda aka rusa shi.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Maina a gaban Babbar Kotun Tarayya bisa zargin almundahanar kuɗi da suka kai kusan naira biliyan biyu.

An ɗage shari'ar ne karon farko ranar Litinin 5 ga watan Oktoban 2020 sakamakon rashin halartar Abdulrasheed Maina da kuma Mai Shari'a Okon Abang na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda rajistira ya sanar da cewa kotun ba za ta samu zama ba.

A rana ta biyu (Talata) bayan an taru domin ci gaba da sauraron shari'ar, rajistiran kotun ya sake bayyana cewa kotu ba za ta zauna ba sakamakon rashin halartar Maina da Mai Shari'a Abang, inda ya ce shari'ar za ta ci gaba a rana ta gaba.

Shari'ar dai ba ta yiwu ba a yau Laraba sakamakon dalilan farko.

Daga bisani Sanata Ali Ndume ya shaida wa kotun cewa bai san inda Abdulrasheed Maina ya shiga ba a matsayinsa na wanda ya karɓi belinsa.

Sai dai Ali Ndume ya ci gaba da halartar zaman kotun a duk waɗancan ranaku domin saka hannu kan shaidar halartar zaman a matsayin ɗaya daga cikin sharuɗan karɓar belin Maina.