Masu tiyata a Amurka sun gwada sanya wa mutum kodar alade

    • Marubuci, Daga Michelle Roberts
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Editan BBC ta Lafiya
  • An wallafa

Wani kwararre a fanni tiyata a Amurka ya ce sun samu nasarar dasa wa wani mutum kodar alade wanda suke fatan hakan zai taimaka wajen kawo karshen karacin taimakon koda da ake samu.

Wanda aka sanya wa kodar mutum ne da kwakwalwarsa ta daina aiki, kuma da taimakon na'ura yake iya rayuwa, wanda aka cire tsammanin warkewarsa.

Kodar da aka yi mafani da ita ta wani alade ce da aka jirkita domin ta dace da halittar jikin dan adam ta yadda jikin ba zai kalle ta a matsayin wani bakon abu ba, balle kwayoyin kariya su yake ta.

Har yanzu ba a yi wa aikin kallo na tsanaki ba, ko kuma a wallafa shi a mujallu da jaridu, amma akwai shirin yin hakan.

Masana sun ce wannan ne aiki mafi girma da aka yi a wannan fanni ya zuwa yanzu.

An yi irin wannan gwajin kan birai, amma gwajin bai zo kan mutane ba.

Ba wani bako abu ba ne, amfani da sassan jikin alade domin dasa wa dan adam. Tuntuni an jima ana dasa wa dan adam bututun da ke kai wa zuciya numfashi.

Akwai kuma wasu sassan da za su dace da dan adam musamman a bangaren girma.

Yayin tiyatar da aka yi ta awa biyu a jami'ar New York masu tiyatar sun hada kodar aladen da ake bayar da jijiyoyin jinin kwakwalwar mutum domin tabbatar da ko za ta yi aiki yadda ake bukata, ko kuma ba zai yi ba.

Sama da kwana biyu suka yi suna nazarin yadda kodar ke aiki, suna ci gaba da gwaje-gwaje iri-iri.

Wanda ya jagoranci aiki Dr Robert Montgomery ya shaida wa BBC cewa "Mun rika bibiyar yadda kodar ke aiki na awanni, kuma tana aiki kamar ta dan adam, duk abin da kodar mutum ke yi haka wannan take.

"Tana aiki sosai, kuma babu alamun za ta kawo wata matsala a nan gaba."

"Zamanin da aka yi a baya ta kashe wani a raya wani ya wuce, ba zai taba dawowa ba.

"Zan iya cewa kimanin marasa lafiyar kashi 40 cikin 100 da suke asibiti za su rayu ta hanyar kodar alade.

"Muna amfani da alade a matsayin abinci, yanzu kuma za mu rika amfani da shi a matsayin magani - alade yana da ma'ana a rayuwarmu."

Ya ce har yanzu binciken bai yi karfi ba, kuma ana bukatar a yi nazari a kai: "Ya ba mu wani sabon kwarin gwiwa kan wani gagarumin abu da za mu iya kai wa dakin bincike.

Iyalan mutumin da za a dasawa kodar yan gayawa masu tiyatar sun amince a yi wannan aiki.

Hukumar da ke lura da irin wadannan ayyuka ta Amurka ta amince a yi amfani da bangaren jikin aladen da aka jirkita halittarsa domin yin irin wannan bincike.

Dr Maryam Khosravi, da ke aiki a bangaren koda da kuma bangaren kulawar gaggawa na hukumar lafiya ta Birtaniya NHS ta ce sun dade suna nazartar yadda za a rika yin amfani da wasu sassan dabbobi a jikin dan adam, amma jin dadinta a yanzu yadda wannan tawagar suka nuna cewa abu ne mai yiwuwa.

Amma a bangaren dokokin aiki, sai ta ce "don za mu iya yin wannan aikin baya nufin kawai mu ta yin hakan har sai al'umma sun amsa wannan tambaya.

Kakakin bangaren jini da na dashe-dashe na NHS ya ce, yadda sassan dabbobi za su rika yi wa dan adam daidai yanzu muka sa a gaba: "yadda za a rika yin wannan aikin dashin a yauda kullum shi ne abu na zahiri.