Newcastle United: Me ya sa ake sukar Saudiyya kan sayen ƙungiyar?

Asalin hoton, Getty Images
Karɓe ragamar ikon ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Newcastle da wani kamfanin Saudiyya ya yi a Ingila ya faranta wa mutane da dama amma kuma masu suka da yawa sun yi Allah-wadai da matakin.
Ga wasu dalili shida da suka sa lamarin ya jawo wa babbar ƙasar ta Musulmai suka.
Gawurtaccen kisan gilla
Kimar Saudiyya ta yi matuƙar faɗuwa game da kisan Jamal Khashoggi a 2018, wani shahararren ɗan jarida mazaunin Amurka wanda ya sha sukar gwamnatin ƙasar.
Wani lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ɗauka aiki ya ce wasu ma'aikatan Saudiyya "sun yi gunduwa gunduwa Khashoggi cikin rashin tausayi" a ofishin jakadancin ƙasar na birnin Istambul da ke Turkiyya.
Rahoton ya alaƙanta Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bn Salman da kisan da kuma wasu manyan shugabannin ƙasar. Duk da cewa Yariman ya musanta hannu a kisan, kimarsa ta yi matuƙar zubewa a ƙasashen duniya.
Budurwar Jamal Khashoggi, Hatice Cengiz, ta siffanta sayen Newcastle da Saudiyya ta yi a matsayin "abin ɓacin rai".
Mohammed bin Salman ne shugaban gidauniyar Saudiyya wadda ta mallaki kashi 80 cikin 100 na hannun jarin Newcastle, duk da cewa hukumomin Premier League sun ce an ba su tabbacin cewa kulob ɗin ba zai kasance ƙarƙashin gwamnatin Saudiyya.
Garƙame mata masu fafutika

Asalin hoton, AFP
A 2018, hukumomin Saudiyya sun tsare mata 13 masu fafutikar kare haƙƙi da suka jagoranci kamfe na neman cire haramcin tuƙin mota kan mata.
An yi zargin cewa an azabtar da huɗu daga cikinsu sannan masu binciken sun ci zarafinsu.
A 2020, wata kotun musamman kan ta'addanci ta samu wadda ta fi shahara a cikin matan mai suna Loujain al-Hathloul da laifi.
Ta musanta zarge-zargen kuma masu kare haƙƙi na Majalisar Ɗinkin Duniya sun bayyana su da "na ƙarya".
Murƙushe ƴan adawa

Asalin hoton, Areej Al-Sadhan
Ba mata 'yan fafutika kaɗai ake ɗaurewa ba, har da siyasa da ƙungiyoyin 'yan kasuwa sannan kuma an haramta ƙungiyoyi masu fafutikar neman haƙƙi.
Gwamman masu fafutika da ƙwararru da malaman jami'a da malaman addini aka ɗaure tun 2017, kawai saboda sun bayyana ra'ayoyinsu, a cewar kungiyoyin kare hakki na kasashen duniya.
Da yawa daga cikinsu sun fuskanci abin da ƙungiyar Amnesty International ta kira shari'ar rashin adalci kan ta'addanci da laifuka ta intanet kuma aka yanke musu hukunci mai tsauri ciki har da na kisa.
'Yan kwanaki kaɗan kafin sayen Newcastle, wata kotu ta jaddada hukuncin shekara 20 a gidan yari kan wani ma'aikacin agajin ɗan Amurka mai suna Abdul Rahman al-Sadhan saboda ya rubuta saƙon da ke sukar gwamnati.
Areej al-Sadhan ta ce an azabtar da ɗan uwanta kafin a daure shi tsawon shekara 20 saboda sukar hukumomi a shafin Twitter
Yaƙin Yemen

Asalin hoton, EPA
Saudiyya ta sha suka game da yaƙin da ta ƙaddamar a maƙwabciyarta Yemen wanda ya haddasa bala'i mai girman gaske.
Dakarun Saudiyya sun afka Yemen ne a 2015 bayan 'yan tawaye sun karɓe iko da mafi yawan yankin kudancin ƙasar sannan suka tilasta wa shugaban ƙasar tserewa.
Rahotanni sun bayyana an kashe fiye da mutum 100,000 a yaƙin, yayin da wata ƙungiya ke cewa fararen hula kusan 8,700 ne suka mutu sakamakon hare-haren dakarun ƙawance ƙarƙashin jagorancin Saudiyya.
An ƙiyasta cewa wasu dubban ɗaruruwa sun mutu sakamakon wasu dalilai da ke da alaƙa da yaƙin kamar ƙarancin abinci, rashin tsarin lafiya, yayin da toshe ƙasar da Saudiyya ta yi ya sa aka kasa kai wa mutum miliyan 20 tallafi a yankin.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai yuwuwar ɓangarorin biyu sun aikata laifukan yaƙi duk da cewa dakarun haɗakar na cewa suna bin dokokin yaƙi.
Hukuncin kisa

Asalin hoton, Anadolu Agency
Saudiyya na cikin ƙasashen da suka fi kowa zartar da hukuncin kisa a duniya.
Tsakanin Janairu zuwa Yulin 2021, an kashe aƙalla mutum 40 a Saudiyya, a cewar Amnesty International.
A watan Yuni, an kashe wani mutum da ake zargi da aikata laifi tun yana ɗan shekara 17, duk da cewa gwamnati ta ce ta daina amfani da hukuncin kisa kan laifukan da yara suka aikata.
An kashe Mustafa al-Darwish ne bisa laifukan da ya aikata na shiga zanga-zangar adawa da gwamnati, duk da cewa ya faɗa wa kotu cewa azabtar da shi aka yi kafin ya amsa laifukan nasa.
Yadda ake ɗaukar 'yan luwaɗi
Duk da cewa Saudiyya ba ta da wata doka a rubuce game da halayyar jima'i ko kuma banbamcin jinsi, ana hukunta duk wanda aka samu da laifuka kamar zina ko luwaɗi.
Kazalika, wata dokar laifukan intanet ta haramta aikata duk wani abu da ya saɓa da "ɗabi'ar mutane da addininsu da kuma sirrinsu".
A Yulin 2020, wata kotu ta ɗaure wani ɗan Yemen wata 10 sannan aka mayar da shi ƙasarsa saboda ya wallafa wani bidiyo yana kiran a daidaita 'yanci ciki har da na 'yan luwaɗi.










