Ƴan Najeriya da suka yaudari mata 100 da sunan soyayya a ƙasashen waje - FBI

    • Marubuci, Daga Karen Schoonbee
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC, Cape Town
  • An wallafa

An gurfanar da wasu maza takwas ƴan Najeriya bisa zargin yaudarar mata ta intanet a Afirka ta Kudu bayan wani gagarumin bincike da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka,FBI, da hukumar ƴan sanda ta duniya suka yi.

Hukumomi a Amurka inda binciken ya samo asali kuma mafi yawan matan suke zaune sun nemi da a tasa keyar mutanen zuwa can.

An zargi mutanen da zambatar mata sama da 100 kusan dala miliyan bakwai kwatankwacin fam miliyan biyar a cikin shekara goma da ta gabata.

Mutanen ba su ce komai ba game da tuhumar.

Wannan ita ce bankada irin wannan mafi girma da aka taba yi a Afirka ta Kudu, in ji kakakin rundunar ƴan sanda Kanar Katlego Mogale.

An kama mutanen ne wadanda shekarunsu suka kama daga tsakanin 32 da 52 a Cape Town ranar Talata bayan taimakon shari'a da aka samu daga Amurka.

Ana ganin hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI da hukumar leken asiri ta Amurkar ne suka jagoranci binciken tare da hadin guiwar hukumomin Afirka ta Kudu wadanda suka hada da sashen zaratan ƴan sandan kasar da ake kira Hawks.

Ana neman mutanen ne a Texas da New Jersey kan laifuka daban-daban, da suka hada da hada baki domin yin zamba ta waya da ta intanet da batar da sawun kudaden Haram da kuma shigar burtu ta hanyar batar da kama ta shafukan intanet na wasu.

Da take gabatar da bukatar kin bayar da belin mutanen, mai gabatar da kara, Robin Lewis ya zarge su da kasancewa ƴan wata kungiya da ake kira Black Axe, wadda kungiya ce ta kasa da kasa ta masu aikata zamba da ke da cibiya a Najeriya, wadda ta kware wajen aikata zamba ta hanyar amfani da asusun banki daban-daban.

Mai gabatar da karar ta ce mutanen hadari ne a bari su shiga jirgi saboda har yanzu suna da hanyar shiga asusun bankuna kamar yadda ya yi zargi.

Wadanda ake zargin na fuskantar daurin shekara 20 a gidan yari idan aka same su da laifi.

'Wadanda ake zargin na kirkirar labaran ban tausayi'

Ana zargin suna dana tarko ne ga wadanda suke zambata ta hanyar amfani da shafukan mu'amulla da mata na intanet, inda suke shigar burtu.

Yawancin wadanda ke fada wa tarkon nasu, mata ne da mazajensu suka rasu ko zawarawa wadanda suka rabu da mazajensu daga sassan duniya, inda matan ke dauka suna soyayya ce ta gaskiya da su.

Kanar Mogale ta ce da zarar matan sun kulla alaka da su ta soyayya wato sun fada tarkonsu, sai mazajen su kirkiri wasu labarai na ban tausayi ko halin kunci da suka shiga inda za su nuna suna bukatar taimakon kudi, misali wani haraji da za su biya domin karbar gadonsu, ko yin wata tafiya mai muhimmanci zuwa waje, ko biyan wani katutun bashi da sauransu, daga nan sai matan su aika musu kudi.

"Mazambatan sukan takura tare da cutar da rayuwar matan, daga nan sai kawai su bace bat'' in ji ta.

Wani makwabcin biyu daga cikin mutanen da ake zargi su biyu, a hirar da ya yi da BBC bisa sharadin ba za a bayyana sunansa ba ya ce ya yi mamakin yadda ƴan uwan biyu suka kasance ƴan kungiya ta mazambata, da ke aikata wannan laifi.

Ya ce, "Suna zaman lafiya da lumana da kuma faram-faram da kowa, ba su taba kawo wani mugun laifi yankin ba. Daya daga cikinsu ma yana auren ƴar Afirka ta Kudu ne.''

"Sau daya a sati kusan motoci masu tsada goma za su zo, kuma su tafi bayan dan wani lokaci. Motoci ne masu tsada kamar su samfurin Marsandi 2021, da Jif (Jeep) da kuma Ferrari. Yadda suke sa kaya kai da ka gansu za ka ce masu kudi ne."

Haushin karnuka ne ya tashi makwabcin nasu a lokacin da jami'an tsaro suka je kama su a ranar Talata.

Kusan jami'ai 60 ne daga ofisoshin ƴan sanda daban-daban suka shafe kusan sa'a shida suna tattara sheda a gidajen. An kai irin wannan farmaki na binciken a wasu gidajen bakwai da ke wannan unguwa.

Mista Lewis ya ce wasu daga cikin mutanen ba a ka'ida suke zaune a Afrika ta Kudu ba saboda fasfo dinsu ya kare. Haka kuma ya ce muddin aka bayar da belin mutanen to kuwa za su iya jirkita wata shedar ta intanet

An tsayar da ranar Talata da Alhamis masu zuwa domin sauraren bukatar bayar da belinsu kafin a saurari bukatar tasa keyarsu zuwa Amurka.

Shafin jaridar Afirka ta Kudu ta TimeLive ta bayar da rahoton cewa rundunar zaratan ƴan sandan kasar (Hawks) na neman mutum na tara da ke da alaka da laifin.