Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ba zan sake soyayya da 'yar Najeriya ba'
An wallafa
Latsa hoton sama don kallon bidiyon:
Isa Sulaiman Panshekara matashin da Ba'amurkiya ta yi takakka tun daga birnin California na Amurka ta zo wajensa a Kano, ya ce shi kam ba zai sake soyayya da mace 'yar Najeriya ba.
A wannan bidiyon cikin hirarsa da BBC Isa ya bayyana abubuwa da dama kan soyayyarsa da Janine Sanchez wadda ake sa ran zai aura a watan Maris din 2020.
Ku kalli bidiyon don jin abubuwan da masoyan biyu suka fada.