Covid-19: Halin da yara 51,000 da cutar korona ta mayar marayu ke ciki a Iran

Asalin hoton, Family of Eliza
- Marubuci, Daga Rana Rahimpour
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian
- An wallafa
Fiye da yara 51,000 ne suka rasa iyayensu sakamakon annobar cutar korona a Iran, a cewar hukumomin kula da jin daɗin jama'a na ƙasar.
Ɗaya daga cikin irin waɗannan yara ita ce Eliza, ƴar shekara huɗu.
Eliza ta shaƙu matuƙa da mahaifinta. Suna karatu tare, su yi waƙa tare, kuma ko yaushe shi ke lallashinta ta yi barci.
Amma kwatsam wata rana sai ya tashi da tari aka kai shi asibiti. Mahaifin nata mai shekara 40 ya rasu sakamakon cutar korona.
"Ta kan shiga halin fargaba a duk lokacin da ba ta ganni ba ko da na minti ɗaya ne, ta kan yi zaton ni ma ba zan dawo ba kamar mahaifinta," a cewar Afrooz, mahaifiyar Eliza.
Eliza na daga cikin dubban yaran da ke cikin tsananin maraicin iyayensu da suka mutu sakamakon cutar korona a Iran.
Da yawan yaran nan suna karatu ne daga gida a tsawon wata 18 da suka gabata kuma ba sa samun tallafi sosai saboda dokokin kulle da aka sanya. Ana fargabar cewa tasirin abin na iya ta'azzara.
"Yaran da suka rasa iyayensu na jin cewa rayuwa ba ta da tabbas," a cewar Dr Samineh Shaheem, Farfesa kan ilimin halayyar ɗan adam da shugabanci a Landan.
"Suna jin cewa sun rasa wani babban abu kuma ba su da iko kan rayuwarsu. Hakan na da illar da za ta daɗe tana tasiri, sannan zai ƙara girman fargabar da suke fuskanta wacce za ta yi mummunan tasiri kan lafiyarsu."
Yanayin da Eliza ke ciki da ɗan sauƙi idan aka kwatanta da na sauran dubban yaran, saboda mahaifiyarta malama ce kuma tana iya samar mata da abubuwan buƙata.
Rayuwa ta yi tsanani sosai ga iyalai da dama - musamman wadanda suka rasa iyayen da suke musu komai a rayuwa.
'Tsananin buƙata'
A lokacin da annobar ta ɓarke, tattalin arzikin Iran dama yana cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi saboda takunkuman da Amurka ta ƙaƙaba wa ƙasar, da cin hancin da ya zama ruwan dare da kuma rashin tsari.
A shekarar farko ta wannan matsala da aka shiga ƴan Iran miliyan ɗaya ne suka rasa ayyukansu, a cewar Cibiyar Bincike kan Majalisar Dokokin Musulunci ta Iran, inda suka shiga cikin mummunan yanayi.

Asalin hoton, EPA
"Rashin tabbas kan halin tattalin arziki da matsanancin yanayi na babu da ake ciki zai iya sa yara da dama da suka ɗan girma su bar karatunsu, saboda su samu damar mayar da hankali kan nemar wa ƙannensu abin rufin asiri, lamarin da ka iya jefa tasu rayuwar cikin ƙaƙa-ni-ka-yi, inda a ƙarshe dukkan iyalan za su shiga cikin matsala," a cewar Dr Shaheem.
Iran ce ƙasar da annobar cutar korona ta fi yi wa illa sosai a yankin Gabas Ta Tsakiya.
Yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar korona a hukumance ya kai 120,000, amma hukumomin Iran sun ce yawan ya fi haka.
Iraniyawa da dama sun ɗora alhakin yawan mace-mace sakamakon cutar korona kan Jagoran Addini na ƙasar Ayatollah Ali Khamenei, kan haramta shigar da alluran riga-kafin korona da aka yi a Amurka da Birtaniya ƙasar a lokacin hunturun bara.
A yanzu ana shigar da alluran riga-kafin, amma kashi 20 cikin 100 na ƴan ƙasar ne kawai suka yi cikakkiyar riga-kafin sau biyu zuwa yanzu.
Shugaban ƙasar Iran Ebrahim Raisi, ya yi alƙawarin cewa za a yi wa kashi 70 cikin 100 na al'ummar ƙasar riga-kafi zuwa ƙarshen watan Satumba - alƙawarin da har yanzu ba a cika ba.
Duk da wannan yunƙuri, mai afkuwa ta afku ga mahaifin Eliza da sauran dubbai da suka riga suka mutu.
Mahaifiyar Eliza ta ce: "Eliza na yawan cewa idan cutar korona ta tafi, baba zai dawo."
Wannan wani fata ne da ba zai taɓa yiwuwa ba. Yara da dama irin ta za su girma da tunanin wataƙila da za a iya yin wani abu don hana cutar kashe musu iyaye, da ba a hana shigar da riga-kafin ba.










