Abin da shugaban Najeriya Buhari ya ce kan Maulidi

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce babban abin da musulmi za su yi domin tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad SAW shi ne su dabbaka koyarwarsa a rayuwarsu da zamantakewarsu.

Buhari ya wallafa sakon maulidin ne a shafinsa na Twitter ranar Litinin, inda ya ce satar jama'a domin neman kudin fansa da kisan jama'a da yi wa mata auren dole duk sun saba da koyarwar addinin musulunci.

Shugaba Buhari ya ce "ina yi wa daukacin musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar annabi Muhammadu SAW. Babbar girmamawa da musulmi za su yi wa annabi ita ce dabbaka halayensa na rashin son tayar da zaune tsaye da son zaman lafiya da kuma yin hakuri."

Buhari ya kuma kara da jan hankalin musulmi da su mayar da hankali wajen yakar akidojin da ke sa tsananin kishin addini da ka iya jefa mutane cikin yanayin ta'addanci.

Ya kara da cewa "A yanzu haka musulunci na fuskantar barazanar ta'addanci da ake kallon addinin da ita."

A saboda haka ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su yi abin da ya kamata wajen kawar da hankalin matasa daga tsaurin addini.

Shugaba Buharin dai ya aike wa 'yan kasar tasa sakon mauludin ne daga birnin Landan inda yake zaman radin kai har zuwa 17 ga watan Nuwamba lokacin da zai koma Najeriyar.