Ku San Malamanku Tare da Babban lamamin Borno Imam Laisu Ibrahim

An wallafa

Babban limamin jihar Borno Sheikh Imam Laisu Ibrahim ya ce nuna ɓangaranci a tsarin shugabanci na daga cikin abubuwan da ke haifar da koma baya tsakanin kowacce al'umma.

Imam Ibrahim, ya shaida hakan ne a lokacin wata tattanawa a cikin shirin Ku San Malamanku na BBC hausa.

Ya ce bai kamata a ce shugaba na nuna bangaranci ko son rai ko zabinsa ba, akwai bukatar a tattauna a kan komai a ɗau matsaya guda.

Shehin Malamin yana bayani ne kan dalilan da suka sa ba a yawan samun rikici tsakanin malaman Borno masu banbamcin aƙida.

Limamin ya ce yana da nauyi sosai a gabanshi domin akwai dimbin malamai a karkashinsa, shi yasa yake kokarin hada kan darikoki da mutunta ra'ayoyi.

Rayuwarsa

An haife shi a Maiduguri a 1962 ya yi makarantar allo a makarantar marigayi Mallam Mahmud.

A shekara 1968 ya shiga makarantar Boko, sai dai yace wannan bai hana shi ci gaba da zuwa makarantar allo ba idan ya dawo daga Boko.

Bayan ya kammala firamare da sakandare a Yerwa, sai ya je ƙasar Masar inda har ya yi karantu a Jami'ar Al-Azhar a 1981, sai dai bai kammala digiri ba ya koma gida saboda wasu dalilai, kamar yadda ya bayyana.

Shehin malamin ya ce ya kuma yi wasu kwasa-kwasai a jami'ar American University da ke birnin Alƙahira na Masar.

Haka kuma ya ringa halartar karatuttuka a wajen wasu malamai a ƙasar ta Masar.

Bayan ya dawo gida lokacin gwamna Mala Kachalla sai aka naɗa shi a kwamitin tafiyar da harkokin shari'a.

Limanci

Tun gabanin zamansa babban limamin Bornon, Sheikh Imam Laisu ya ringa limanci a babban masallacin Maiduguri dake fadar Shehun Borno.

A lokacin yana muƙaddashin liman tare da yayansa, a lokacin mahaifinsu yana babban limamin Borno.

Imam Ibrahim ya shaida wa BBC cewa gidansu sananne ne domin akwai sarauta da limanci, a lokacin Shehu mai rasuwa Mustapha Umar Elkanam sai aka nada shi hakimi a karamar hukumar Konduga a shekara ta 2003.

Mahaifinsa ya rasu a 2014 bayan rasuwarsa ne ya maye gurbinsa a matsayin babban limamin Borno, kuma shi ne shugaban hukumar da'awa ta Borno.

Shawarar da baya mantawa da ita daga mahaifinsa ita ce "sanin darajar gida da iyaye da asali." Yace mahaifinsu ya nuna musu alfanun zaman gida da kaurcewa yawo. Sannan sun kasance masu sanya linzami a bakinsu da sanin ya kamata.

Sannan yace farin cikinsa shi ne ganin ya kyautatawa mutane ya taimake su, sannan yace yana baƙin ciki a tambayshi abin da ba shi da halin taimakawa. Burinsa kuwa shi ne ganin ya sa wa mutane farin ciki.

Abinci da Iyali

Limamin ya ce shi ba mutum ba ne mai zabin abinci domin duk abin da ya samu yana ci abinsa.

Sai dai kuma ya shaida mana cewa ya fi son abinci gargajiya irinsu miyar kuka da kubewa.

Yana da mata guda da yara.

Buri

Imam Ibrahim ya ce burinsa a duniya shi ne so wa ɗan uwansa abin da yake so wa kansa.

Yana gudun bata wa mutane rai da gudun tashin hankali. Kuma ba shi da buri ba ya kai kansa inda Allah bai kai shi ba.