Ku San Malamanku tare da Malama Zahra'u Muhammad Umar

An wallafa

Wata fitacciyar malamar addinin Musulunci, Malama Zahra'u Muhammad Umar ta ce ba ta da wani buri a rayuwa kamar ganin ta sa farin ciki a fuskokin marasa galihu.

Malama Zahra'u da ke aiki da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce tana takaicin ganin mutane cikin wahala, domin har hawan-jini ta kamu da shi saboda ganin wasu yara cikin akuba.

Malamar ta bayyana hakan ne a lokacin wata tattaunawa cikin shirin Ku San Malamanku na BBC.

Malam Zahra'u ta ce Suratul Ma'ida na ba ta wuya a lokacin hadda, sannan ta fi son Suratul Yasin.

Rayuwa

Malama Zahra'u ta ce an haife ta a unguwar Fagge da ke Kano, kuma ta yi makarantu daban-daban har ta kai matakin digiri na uku a fanin ilimin addinin Musulunci.

Sannan ta yi karatu mai zurfi a fanin fafutikar mata wajen yaye musu matsalolinsu musamman a Hukumar Hisbah.

Malama Zahra'u tana da aure da ƴaƴa bakwai.

Abin koyi

Malama Zahra'u ta ce ta kasance mai girmama kowanne malami, kuma tana kokarin laƙantar kowanne malami da take ganin akwai abin da za ta koya daga wurinsa.

Amma wadanda suka fi tasiri a kanta akwai Farfesa Ibrahim Muhammad na jami'ar Bayero da Dr Ahmed da Malam Abubakar Jibril wanda limamin jami'ar BUK ne.

Malamanta na da yawa kowanne akwai abin da ta koya daga wajensu.

Aiki da rayuwar aure

Malama Zahra'u ta shaida cewa aikinta akwai matukar wahala saboda tana hada ayyukan ofis da na kula da iyali ga kuma masu yi mata kira daidaiku domin neman mafita kan matsalolin rayuwa.

Ta ce matsalolin aure ta fi karo da su, kullum akalla tana karbar wayar mace 10 kan matsaloli ko tambayoyin da ya shafi zamantakewar aure.

Mata na yawan kiranta suna neman shawarwari da yadda za su gyara zaman aurensu, tafiyar da maigida da addu'o'in neman mijin ya so su.

Ta ce tana shan wuya sosai a gwamnatance aiki na tafiya daidai amma tafiyar da aikin gwamnati da kuma na yawan kiranta ana neman taimako da abu ne mai sauki ba.

Malamar ta ce wani lokaci har ciwon-kai take yi, kuma ba ta jin dadin a kirata ba ta dauka ba, gudun ba ta san gararin da mutum ke ciki ba.

Ta ce kasancewa mijinta mai wayewa ne da ilimi baya korafi, yana bata damar ayyukanta kuma yana karfafa mata gwiwa da shi mata albarka.

'Tashin hankali da na shiga'

Malama Zahra'u ta ce a hukumar Hisbah ta yi karo da hawan jini saboda dimbin matsaloli da korafe-korafe da suke karba.

Ta ce akwai lokacin da aka kwaso yara kanana daga wani makarantar mari, inda wani 'makirin mutum' ke lalata da yara mazan.

Ta ce abin takaici ne ganin a ce yawan wannan yara sama da 30, mutum guda duk ya yi lalata da su. Da aka kawo su ofishinsu, yaran na cikin tsananin akuba, saboda ko ina a jikinsu ciwo ne da karzuwa.

"Yanayi ya kadaita ni ya sa jini na ya hau har 180, saboda abin takaici ne da tashin hankali ganin ka tura yaronka neman ilimi amma ya kasance an lalata masa rayuwa."

Sannan ta shaida cewa an taba kawo mata karar wani mutum da ya farfasa jikin dansa mai wata 7, yanayi ba dadin gani.

"An gayyaci mahaifin ya zo ya yi bayanin dalili, amma zuwansa ke da wuya sai ya soma ihu ya rinka ihu, har ya taso kamar zai doke ni, ni kuma na rinka karanta ayatul kursiyu."

"Ai kuwa nan take ya rike bango ya farfasa jikinsa ko ina jini, daga baya da na zauna da matarsa na ji ta bakinsa, sai na ce ta koma gida kar ta koma gidan iyayenta."

Malama Zahra'u ta ci gaba da cewa: "Nan kuma take ba ni labarin ai wai ya taba kashe ɗansa, na tsorata, saboda tana zaune da mutumin da zai iya hallakata.

"Amma wani abin mamaki ina cewa ta tafi gidansu sai ta sunkuya ta soma kuka, ta shaida mun cewa idan ta tafi gida babu inda za ta zauna. Mahaifiyarta ta yi aure kuma mijinta daki ɗaya suke haya."

Farin ciki da Bakin ciki

Abin da ke bata farin ciki shi ne akwai yara 'yan mata guda 9 da ke cikin halin talauci ko sun yi ciki ko kwaya dangi sun koresu. To ta ɗau nauyin kula da su da sauya musu hali da tarbiyyartar da su har ta kai ga ta musu aure, kuma suna zaune lafiya.

Sannan wani abin da ke sake sa ta farin ciki shine, raba abinci ko kudi da kanta, tana son taimakon mai rauni kuma ta fuskanci yana murna.

Sannan abin da ke sa ta bakin ciki shi ne rashin tarbiyya, bata son ganin rashin tarbiyya a gida.

Abinci da Buri

Malama Zahra'u ta ce ta fi sha'awar abinci mai ruwa-ruwa don haka tana son farfesu shi ne ya fi mata dadi da kwantar mata da hankali.

Babban burinta kuma shi ne neman cikawa da imani.