'Yan canji: Karancin dala na neman durkusar da mu

Kudaden Dala da Naira

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manya da kananan 'yan kasuwar musayar kudade a Najeriya na ci gaba da bayyana damuwarsu kan yadda karancin dala a kasuwannin bayan fage ke nenan durkusar da kasuwancinsu.

'Yan canjin dai sun ce kashi biyu bisa hudu na wadanda ke harkar canji a kasar sun rasa jarinsu, yayin da wasunsu kuma suka karkatar da dukiyoyinsu zuwa bangaren noma.

Kasuwar 'yan canjin kudi ta Wafa dake birnin Kano a arewacin Najeriya, na daya daga cikin irin kasuwannin musayar kudi ta bayan fage da ta yi suna kuma anan ma ana wannan koke.

Wakilin BBC a Kano, Khalifa Shehu Dokaji, ya ziyarci kasuwar ta Wafa, inda ya tarar 'yan kasuwar sun yi jugum-jugum a bakin shaguna da kuma gefen titi ana jiran masu bukatar canji.

A baya dai kasuwar kan cika makil da masu siya da sayar da kudaden ketare ba bu masaka tsinke saboda hada-hada.

Wasu da wakilin BBC ya tattauna da su a kasuwar wadanda suka je siya ko sayar da dala sun bayyana cewa, dala ta yi karancin sosai a kasuwar.

Mutanen sun ce 'yan kasuwar su kan ce musu ai dala ta yi karanci a kasuwa saboda yanzu gwamnati ta dakatar da bayar da dalar.

Su kuwa masu sayar da kudaden kasashen waje a kasuwar ta wafa, sun shaida wa BBC cewa, a yanzu dan canji ya shiga halin ha'ula'i.

Nasiru Salisu Kura, daya ne daga ciki masu sayar da kudin a Wafa, ya ce," A yanzu muna cikin wani yanayi saboda canjin kudaden da muke samu dominu ciyar da kanmu da iyalanmu na neman gagararmu, sakamakon a yanzu gwamnati ta dakatar da bayar da kudin. A don haka ina ganin yanzu zan karkatar da jarina na koma gona, don ba zan zauna a kasuwa babu ciniki ba, sai hamma,'' in ji dan canjin.

Shi kuwa wani dan canjin Abdullahi Iya Wafa, da tuni ya cinye jarinsa ya shaida wa BBC cewa, ya gaji sana'ar canji ne tun kaka da kakanni, amma gashi yanzu tuni ya cinye jarinsa, da ganinsa ka ga ya yi zuru-zuru in ji shi.

Ya ce ba shi kadai ne ya cinye jarinsa ba, mutane da dama sun cinye na su, abin dai sai godiyar Allah.

Wannan koke na 'yan canjin na zuwa ne a dai-dai lokacin da 'yan Najeriya ke kokawa da yadda darajar Naira ke ci gaba da faduwa, wanda hakan ya fara haifar da tashin wasu daga cikin kayan masarufi a kasar.