Hotunan Afirka na mako 24-30 Satumban 2021: Bikin ibadar Musulmai a Senegal da gadar tsakiyar kogi

An wallafa

Zababbun hotuna daga nahiyar Afrika da kewaye

Short presentational grey line
Wadanda suka hada taron sun wanke masallacin Touba a ranar 26 ga watan Satumba 2021, wani babban taro da Musulmai ke yi duk shekara a Senegal, wurin da dubban mutane ke zuwa ibada a kowacce shekara.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Lahadi aka wanke babban masallacin Touba....
Wadanda suka hada taron sun wanke masallacin Touba a ranar 26 ga watan Satumba 2021, wani babban taro da Musulmai ke yi duk shekara a Senegal, wurin da dubban mutane ke zuwa ibada a kowacce shekara.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wuri mafi tsarki ga Musulman da ke bin darikar Mouride a Senegal....
Wadanda suka hada taron sun wanke masallacin Touba a ranar 26 ga watan Satumba 2021, wani babban taro da Musulmai ke yi duk shekara a Senegal, wurin da dubban mutane ke zuwa ibada a kowacce shekara.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dubban mabiya ne ke zuwa ibada wurin a duk shekara
Mutane kan gyara dawakansu tsaf domin gabatar da su ga masu ziyara a kowacce shekara, wani biki da wata kungiya mai kula da kiwon dokuna ke hada wa a Sidi Thabet a Tunisia a ranar 24 ga watan Satumba 2021. An sayar da dawakai 50 a wannan shekarar.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wani kasaitaccen dokin Larabawa da ake yi wa ado a Tunisia a ranar Juma'a........
Mutane kan gyara dawakansu tsaf domin gabatar da su ga masu ziyara a kowacce shekara, wani biki da wata kungiya mai kula da kiwon dokuna ke hada wa a Sidi Thabet a Tunisia a ranar 24 ga watan Satumba 2021. An sayar da dawakai 50 a wannan shekarar.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, An sayar da dokuna 50 a wannan bajakolin sayar da dokunan da aka yi a Sidi Thabet
Wani Jangwalagwada ya kama kwaro a matsayin abinci a wani wurin shakatawa da ake kira Tsavo a Kenya

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A wani wurin shakatawa da ake kira Tsavo a Kenya, kadangare ya yi kuri kan abin da zai samu ya sa a baki.
Yaran kasar Laberiya na wasan kwallo a wani fili mai datti a yankin Barclay da ke Monrovia a ranar 25 ga watan Satumbar 2021.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A Liberia kuwa a ranar Juma'a, yara ne ke wasan kwallon kafa a Monrovia babban birnin kasar
Simo Mdudu da ke da kafa guda ya daki kwallon Golf a wasannin da ake yi a Afrika Ta Kudu a gasar Sarki David Mowbray da ake yi ta masu bukata ta musamman a Cafe Town a ranar 27 ga watan Satmba 2021.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Simo Mdudu ya kai wa kwallo duka a wasan Golf na masu bukata ta musamman da aka yi a Cape Town.
Matafiya a kasa na tsallaka gadar da ta hada tsakanin babban yankin Kenya da kuma tsibirin Mombasa an raba tsakani ne saboda a shawo kan annobar korona 29 Satumbar 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Laraba kenan lokacin da matafiya ke haura gadar da ta hada tsakanin tsuburin Mombasa da garin Likoni.
1px transparent line
Yar kasar Swedin Greta Thunberg mai rajin kare muhalli daga hagu sai kuma tta kasar Uganda Vanessa Nakate daga dama a wani taron yan jarida da aka yi a Milan a ranar 28 ga watan Satumba 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Kwana guda kafin fara taron muhalli na Uganda masu fafutukar kare muhalli Vanessa Nakate daga dama da kuma Greta Thunberg daga Italiya
Taron magoya baya da yan jarida a Milan bayan kammala taron kare muhalli a Italiya

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Alhamis 'yar Uganda mai shekara 24 na yi wa taron manema labarai bayani, bayan kammala taron Firaiministan Italiya Mario Draghi. " Lokaci ya yi da masu bata muhalli za su biya.... babu karin alkawarin da ba za a cika ba".
Iyaye na ta yi wa yayansu siyayyar kayan makaranta a Alkahira ranar 28 ga watan Satumbar 2021, lokacin da za a fara sabon zangon karatu a ranar 9 ga watan Oktoban 2021.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, An kusa komawa hutun makarantu a Masar, inda wannan magidanci ya je saya wa yaransa kayan makaranta a ranar Talata
Mutane na yin tafiyar kasa a Khan al-Khalili bazaar a tsohon yankin Alkahira, a ranar 27 ga watan Satumba 2021. lokacin da ake bikin ranar yawon bude ido na MDD

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mutane na yin tafiyar kasa a Khan al-Khalili bazaar a tsohon yankin Alkahira....
Hoton mabiya cocin Shembe da ke girmama Mduduzi "Unyazi Lwezulu"

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kwana guda bayan kammala biki a garin Durban da ke gabar ruwa inda daruruwan mabiya cocin Shembe suka taru domin murnar bikin samun yancin kan coci a Afrika Ta Kudu, sun yi tattaki domin nuna goyon baya ga mutumin da suke kallo a matsayin waliyyi Mduduzi "Unyazi Lwezulu"
'Yar kasar Afrika Ta Kudu da ke yin fina-fina Thuso Mbedu ta je bikin kaddamar wani fim a Los Angeles a ranar Asabar a wani sabon wajen tarihi na kamfanin Picture Motion a ranar 30 ga watan Satumbar 2021.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, 'Yar kasar Afrika Ta Kudu da ke yin fina-fina Thuso Mbedu ta je bikin kaddamar wani fim a Los Angeles a ranar Asabar a wani sabon wajen tarihi na kamfanin Picture Motion.
Wata mata rike da kyandir

Asalin hoton, Amensisa Negera/BBC

Bayanan hoto, Kwana guda bayan da mabiya darikar Orthodox a Habasha a bikin Meskel da suke yi ko wacce shekara
Ranar 26 ga watan Satumba wani matashi ke tsaye a dandalin da ake gudanar da wannan biki

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani hutu da ake yi a kasa baki daya domin tunawa da ranar da gicciye Yesu inda ake nuna al'adu ciki har da wasa da wuta da addu'a a Addis Ababa babban birnin Habasha.

Duka hotunan na da haƙƙin mallaka.