Ku San Malamanku tare da Sheikh Muhammad Mustapha a Borno

Bayanan bidiyo, Ku San Malamanku tare da Shiekh Madu Mustapha
An wallafa

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar Borno Sheikh Muhammad Mustapha wanda aka fi sani da Sheikh Madu Mustapha Ibrahim ya ajiye son zuciya a gefe da rashin sanya ra'ayi a cikin al'amuran da suka shafi al'umma sune suka sa ba a fiya samun rikici tsakanin malaman addinin Musulunci a jihar ba.

Sheikh Madu Mustapha, wanda ya tattauna da BBC Hausa a cikin shirin Ku San Malamanku ya ce a ko yaushe malaman Borno na fifita masalahar al'umma fiye da banbamcin fahimta da ɓangaranci.

Malamin wanda babban jami'i ne a ma'aikatar addinin Musulunci ta jihar ta Borno ya ce "idan aka samu wasu ayyuka da za a yi wanda ake buƙatar wata manufa guda, misali a ce ga wani abu wanda ya shafi zaman lafiya ko aikin hajji da sauransu sai ka ga ba wanda yake sa ra'ayinsa ko fahimtarsa a cikin duk malaman.

"Da wanda yake tafarkin sunna da wanda yake tafarkin ɗariƙa duk za su duba mece ce maslahar abin da aka sa a gaba, ba mene ne ra'ayina ko me ya sa na wa bai samu ba."

Ya ce haka kuma ba su taso sun ga malamansu suna da irin wannnan hayaniyar ba.

"In mun kawo hayaniyar ke nan son zuciya muka yi," in ji Sheikh Madu Mustapha.

Tarihin Malamin

An haifi Sheikh Muhammad Mustapha Ibrahim a unguwar Mafoni da ke birnin Maiduguri, kuma ya fara karatun allo a unguwar, a makarantar Gwani Ibrahim dan Gwani Asharambe har zuwa lokacin da ya yi sauka biyu.

Ya koma karatun litattafai a wajen malamai daban-daban kamar Malam Makinta da Malam Muhammad Zubair da Sheikh Abba Aji.

Daga nan ya fara karatun zamani a 1985, inda bayan kammala difloma ya samu tafiya zuwa Jami'ar Musulunci ta Madina, inda ya yi digiri a fannin hadisi, sannan ya koma Najeriya a 2001.

Malamin ya ce a lokacin da yana kuruciya wasanni sun dauke masa hankali, abin da ya sa iyayensa suka ringa hana shi fita domin ya yi karatu.

A lokacin dai wasannin langa da kwallon kafa ne suka dauke masa hankali, kuma a kwallon kafa ɗin ya fi buga tsakiya.

To amma Sheikh Madu ya ce daga baya Allah ya sa masa son karatun a zuciyarsa, abin da ya sa ya mayara da hankali sosai.

Wasu na baya da za ku so

Babban tashin hankali da farin ciki

Shiekh Madu Mustapha ya ce babban tashin hankalin da ya haɗu da shi a rayuwa wanda bai taɓa haɗuwa da shi ba shi ne mutuwar mahaifinsa, da kisan gillar da aka yi wa Sheikh Ja'afar Mahmud Adam.

Amma abin farin cikin da ba zai manta da shi ba shi ne lokacin da ya samu damar yi wa mahaifinsa aikin hajji bayan rasuwar mahaifin na sa wanda bai samu damar sauke ibadar ba a rayuwarsa.

Sai kuma lokacin da ya sauke Alkur'ani bayan rasuwar mahaifinsa.

Wani abin farin cikin kuma shi ne lokacin da ya samu damar zuwa karatu a jami'ar Musulunci ta Madina.

Iyali

Sheikh Madu Mustapha ya ce yana da mata huɗu da ƴaƴa 13, biyu sun rasu, yayin da 11 suke raye.

Dangane da abinci kuma Sheikh Madu Mustapha ya ce ya fi son biski da miyar yakuwa.

Babban burin malamin ya ce shi ne ya ga ya samu damar taimaka wa mabuƙaci.