Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Arsenal za ta bai wa Sevilla Lacazetta a ba ta En-Nesyri
Leeds United ta fara tattaunawa da dan kwallon tawagar Ingila, Kalvin Phillips kan tsawaita kwantiraginsa, domin kada Manchester United ta dauke dan kwallon. (Star)
Tottenham na son daukar mai tsaron ragar West Brom da tawagar Ingila, Sam Johnstone, mai shekara 28. (Football Insider)
Haka kuma Tottenham ta ce a shirye take ta bar dan kwallon Ingila, Harry Winks, a watan Janairu idan aka bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai. (Caughtoffside)
Manchester City na son sayen dan kwallon Bayern Leverkusen mai shekara 18 dan wasan tawagar Jamus, Florian Wirtz. (Bild via Sport Witness)
Chelsea na duba yiwuwar daukar mai tsaron bayan Villarreal, Pau Torres. Manchester United ma na sha'awar wasannin dan kasar Sifaniya. (90min)
Declan Rice ya ce yana jin dadin wasa a West Ham zai kuma cika burinsa a kungiyar.
Ana ta alakanta dan wasan mai shekara 22 da cewar zai koma ko dai Chelsea da kuma Manchester United. (Sky Sports)
Inter Milan ba ta da sha'awar daukar mai tsaron ragar Arsenal, Bernd Leno.
Kungiyar da ke buga Serie A tafi son ta sayi golan Ajax, Andre Onana. (Fabrizio Romano via Twitter)
Leno ya ce ya tabbata dalilin da ba a sakashi a wasannin Arsenal ba saboda rashin kwazonsa ba ne, saboda haka yana fatan barin Emirates a watan Janairu. (Bild via Mirror)
Dan kwallon tawagar Faransa, Jules Kounde ya ce ya mayar da hankali kan bunkasa Sevilla, bayan da Chelsea ta kasa cimma yarjejeniyar daukarsa kafin fara kakar bana. (Star)
Shugaban Fiorentina, Rocco Commisso ya ce suna ta rarrashin Dusan Vlahovic wanda Arsenal da Chelsea ke son daukar, domin ya saka hannu kan kwantiragin ci gaba da taka leda a Serie A.
Dan kasar Sevbia ya ci kwallo 21 a kakar bara a Italiya. (Express)
Everton na ci gaba da bibiyar dan wasan Roma, Gonzalo Villar, bayan da dan kwallon baya cikin 'yan wasan da Jose Mourinho ke cikin tsarinsa a kungiyar. (Fichajes - in Spanish)
Arsenal za ta bayar da Alexandre Lacazette ga Sevilla, ita kuma ta karbi dan wasan tawagar Morocco, Youssef En-Nesyri. (La Razon - in Spanish)