Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jamus: Za a fara zabe domin maye gurbin Angela Merkel
Masu zabe a Jamus na shirin fara kada kuri'a a ranar Lahadin nan domin zabar sabuwar majalisar dokoki da za ta kai ga kafa sabuwar gwamnati.
Zaben shi ne zai kawo karshen mulkin shugabar gwamnatin kasar Angela Merkel na shekara 16.
Jami'ai sun ce an samu yawan mutanen da ba su taba yin zaben ba ta hanyar aika wa da wasika da suka yi hakan a wannan karon.
Duk da cewa shugabar gwamnatin mai barin gado Angela Merkel ta fito fili tana goyon bayan dan takarar jam'iyyarta ta masu ra'ayin rikau, Christian Democrat Union, CDU Armin Laschet domin ya gaje ta, amma ana ganin zaben zai yi zafi tsakaninsu da jam'iyyar 'yan gaba dai gaba dai, masu ra'ayin kawo sauyi ta SPD mai dan takara Olaf Scholz, Ministan Kudi na Jamus din.
Wanda hakan ya sa ake ganin abu ne mai wuya a iya hasashen amsa tambayar me zai biyo bayan Merkel.
A wurin gangami na karshe na yakin neman zaben CDU a mahaifar Mr Laschet wato garin Aachen, Mrs Merkel ta yaba wa dan takarar tasu tare da bayyana shi a matsayin mutum na mutane da ke zaman gada da zai kai al'umma ga tudun mun tsira.
Mrs Merkel wadda ta mamaye siyasar Jamus tsawon shekara 16 ta yi hakan ne duk da cewa ta yi alkawarin kauce wa yakin neman zaben na Lahadi.
Tuni hadakar gwamnatinsu ta jam'iyyarta ta CDU da CSU ta rasa tazarar da take da ita a zaben abin da ya sa a yanzu take bin jam'iyyar SPD (Social Democrats) karamar cikin gwamnatin hadakar yanzu.
Batun sauyin yanayi dai ya ja hankali sosai a yakin neman zaben.
Ana kuma ganin Jam'iyyar masu ra'ayin kare muhalli ta The Green Party za ta taka muhimmiyar rawa wajen kafa gwamnati ta gaba ita ma.
Amma dai da farko sai kasar kamar yadda ake gani ta kai ga wata doguwar tattaunawar kafa gwamnatin hadaka.
Abin da hakan ke nunawa kuwa shi ne kusan an kawo karshen zamanin gwamnatin Angela Merkel a Jamus, ko da yake ba za a ce gaba daya dungurumgum ba.
Zaben na ranar Lahadi mataki daya ne kawai na kafa sabuwar gwamnati ta gaba. Mrs Merkel za ta ci gaba da kasancewa a kan kujera amma a matsayin shugabar gwamnati ta rikon kwarya.
Wannan shi ne karon farko da mai rike da mukamin shugaban gwamnatin Jamus din ba ya neman a sake zabensa a tarihin kasar na bayan yaki.
Ba shakka za a ji tasirin wannan zabe na Jamus ba a cikin kasar ba kadai hatta a kasashen waje.
Domin Jamus ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a Tarayyar Turai kuma kasa mafi tasiri da ikon fadi a ji a gamayyar.
Amurka da Birtaniya da Tarayyar Turai da China da sauran kasashen duniya ba shakka suna nan sun zuba ido su ga yadda za ta kaya a zaben, na majalisar wakilai, da ake kira Bundestag wadda za ta kasance ta 20, mai kujeru akalla 598, da mutane miliyan 60 da dubu 400 za su zaba.