Zaɓen Jamus: Sauye-sauyen da Angela Merkel ta kawo a kasarta

    • Marubuci, Daga Jenny Hill
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Berlin correspondent
  • An wallafa

A matsayinta na ɗaya daga cikin Shugabanni mafiya tasiri a duniya, Angela Merkel ta taimaka wurin saita alkiblar Siyasar Turai da ma ta duniya baki daya.

Bugu da kari a tsawon shekaru 16 da ta shafe a matsayin Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta kawo gagarumin sauyi ga rayuwar miliyoyin Jamusawa, duk da ba lalle ne manufofin nata sun gamsar da kowa da kowa ba.

Daliban makarantun sakandare da suka kammala a bana na daga cikin wadanda mulkin Mrs Merkel ya yi tasiri kan rayuwarsu sosai, kuma da dama sun gamsu da yadda Shugabar ke tafiyar da mulkin dimokuradiyya a Jamus.

A duk tsawon rayuwarsu ba su san wata gwamnati ko wani Shugaba ba, ban da Angela Merkel.

''Ba za muce mun samu kololuwar abinda muke nema a mulkin dimokradiyya ba, amma kuma ba ma fuskantar wata matsala'', in ji Ole Schroeder.

"Ina jin dadin yadda Jamus ke gudanar da tsarin shige da fice. Kowa da na damar zuwa ya zauna a Jamus kuma ya cimma burinsa a nan, a cewar Alisa Gusakov.

To amma duk da haka suna fargabar abinda zai zo gaba.

Babbar damuwar Lina Ziethen's ita ce sauyin yanayi.

"Dole ne mu tashi tsaye mu fada wa jama'a cewa mun daina tuka motoci, mu kuma daina hawa jirage don zuwa hutu saboda mu rage fitar da hayaki.

"Abu ne da ya kamata a ce mun yi shekaru 50 da suka wuce ba wai a yanzu ba."

Wannan abu ne da ke zukatan Jamusawa da dama ba wai wadannan matasa kawai ba.

To amma a karkashin mulkin Mrs Merkel, Jamus ta rage yawan hayakin da take fitarwa tare kuma da zuba kudade wurin samar da makamashi.

Sai dai kuma an yi amanna cewa har yanzu akwai jan aiki wurin cimma burin da a ke da shi, kuma har yanzu a na kona gawayi a Jamus.

Wasu na ganin hakan bai rasa nasaba da watsi da batun samar da makamashin nukiliya da Jamus ta yi, biyo bayan ibtila'in da ya faru a tashar makamashi ta Fukushima da ke Japan shekaru 10 da suka wuce.

Duk wanda ya zagaya dazukan da ke shimfide a Jamus zai iya ganin irin barnar da sauyin yanayi ke iya yi wa kasar.

Itacen da ke ba da kariya sun riga sun yi laushi, a cewar Hans Schattenberg, wanda ke aiki a dazukan da ke gabashin Harz, yanzu ta kaiga babu aikin da su ke yi shida ma'aikatansa illa sare itatuwa don takaita yaduwar barnar da ke faruwa.

"Ba mu taba tunanin sauyin yanayi zai iya yin tasiri a dazukan nan ba kamar yadda mu ke gani a yanzu.''

"Abinda ya fi firgitamu ma shi ne yadda abin ke shafar hatta tsofaffin itatuwan kaba da na bakin ruwa.'' In ji Schattenberg.

Ba shakka Jamus ta bunkasa a karkashin mulkin Mrs Merkel, kuma wadanda za su gajeta za su samu yabo saboda irin arzikin da ta samar.

Sai dai kuma masu suka na cewa irin yadda ake samun sauye-sauye a fannin fasaha, sai Jamus ta zage dantse kafin ta iya gogayya da sauran kasashe.

Zaben Jamus na 2021

Jamusawa za su jefa kuri'a a zaben 'yan majalisa ranar Lahadi 26 ga watan Satumba.

Karo hudu jam'iyar CDU ta Mrs Merkel na lashe zaɓe, amma a bana kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa ta na fuskantar babban kalubale.

Danginsu Anke Ketterer na daga cikin iyalan da su ka samu bunkasar kasuwanci a lokacin mulkin Mrs Merkel.

''A tsawon shekaru mun samu arziki, kuma Angela merkel ta yi kokari.''

''Kusan babu wani abu da za mu yi korafi a kai,'' in ji minta Phillip, wanda ke amfani da sunan iyalinta da suka yi suna a harkar kasuwanci a Jamus.

''Ba mu da matsala a Jamus, amma kuma akwai bukatar mu zage dantse mu matsa daga inda muke, in ba haka ba, za a yi gaba a barmu.'' in ji Phillip.

Wani abu kuma babba da za a rika tunawa da Mrs Merkel da shi, shi ne kekeshe kasa da ta yi ta ki rufe kofa ga daruruwan dubban masu neman mafaka a Jamus, wanda ya sa ta fuskanci matsin lamba sosai a 2015.

Jamus ta dade tana dogaro da 'yan cirani don cike gurabun ayyuka, da ganin tattalin arzikinta ya dore, da kuma cike gibin yawan al'ummarta da tsofaffi suka mamaye.

A yau fiye da daya bisa hudu na mutunen da ke zaune a Jamus na da tsatso daga 'yan ci rani.

Babban misali shi ne zuwan 'yan ci ranin 'Gastarbeiter' daga Turkiyya bayan yaƙin duniya na biyu.

Negin na daga cikin mutanen da ke zaune a Jamus ta dalilin neman mafaka daga Iran, kuma ta fadi cewa kadan ya rage ta nutse a tekun mediterranean a lokacin da kwale-kwalensu ya yi nauyi ya nemi ya nutse.

A yanzu tana sanin makamar aiki a wani asibitin hakori da ke Berlin, kuma a cikin harshen Jamusanci ta ce tana da burin zama kwararriyar likitar hakori.

A lokacin da aka matsa mata lamba saboda kwararar 'yan ci rani, Mrs Merkel ta fada wa Jamusawa cewa ''Wir schaffen das'', ma'ana ''za mu iya.''

Kuma shekaru shida bayan haka, da dama sun gazgata kalamanta lura da cewa a zahiri take matsalar ta zama tarihi.

To amma duk da haka akwai tsiraru da ke cewa har yanzu a na samun hare-haren ta'addanci daga 'yan ci rani.

Baya ga batun 'yan ci rani, masu adawa da Mrs Merkel sun ce ya kamata a ce ta kara hubbasa wurin cike giɓin bambancin albashi tsakanin ma'aikata maza da mata.

To amma a cewar Daniela Schwarzer ta gidauniyar masu fafutuka ta 'Open Society Foundation' ''Angela Merkel ta yi kokari ta wannan fannin, kuma abun koyi ce ga matasa mata da ke tasowa.''

''Idan mutane za su bai wa Mrs Merkel maki na tsawon shekaru 16 da ta shafe tana mulki, ba shakka ta yi nasara ba a ɓangaren tattalin arziki kadai ba, har da yadda ta shirya Jamus don gaba,'' a cewar Farfesa Magnus Brechtken na Cibiyar Nazarin Tarihi da ke Munich.

Daga nesa, za a iya cewa siyasar Jamus ba ta kayatarwa sosai. Ma'ana ba ta sauyawa sosai.

Kuma hakan na nufin Mrs Merkel ta bai wa kasarta abinda ta ke bukata daga Shugaba, wato wata murya mai kwantar da hankali a dai-dai lokacin da duniya ke shiga wani yanayi na rashin tabbas.