Muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a wannan makon.

An wallafa

Yayin da ake shirin shiga sabon mako, bari mu duba wasu muhimman abubuwa da suka faru a wannan makon daga ranar Lahadi 19 ga watan Satumba zuwa Asabar 25 ga watan.

Buhari ya gabatar da jawabi a gaban shugabannin kasashe a Majalisar Dinkin Duniya

Ranar Juma'a 24 ga wannan watan ne Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabi a gaban shugabannin duniya sama da 80 da ke halartar taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 76 a Birnin New York na Amurka.

A jawabin nasa, shugaban ya yi magana kan batutuwa da dama da suka kunshi tsaro da cutar korona da tattalin arziki da sauyin yanayi.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida cewa yana samun nasara a kokarin murkushe mayakan Boko haram da suka addabi yankin arewa maso gabashin ƙasar.

Haka kuma, shugaban ya jero batun rashin shugabanci na gari da baya kan turbar dimokuradiya da keta hakkin bil'adama da talauci da rashin adalci da daidaito a matsayin manyan batutunwan da ke bukatar a duba.

Fara amfani da fasahar 5G a Najeriya

Ranar Alhamis 23 ga watan Satumba ne ministan sadarwa da tattalin arzikin Isa Pantami ya ce nan da watan Janairu 2022 za a fara amfani da 5G a Najeriya, wanda hakan zai taimaka wajen sanya idanu kan masu lalata kayan gwamnati.

Ministan ya bayyana hakan ne a Maiduguri yayin wani taron tattaunawa don lalubo bakin zaren matsalar masu lalata turakun sadarwa da wutar lantarki

Malam Ubale Maska, wanda ya wakilici ministan ne ya ce kwamitin kolin tarayyar Najeriya ya amince da fasahar ta 5G wanda kuma hakan zai iya habbaka harkokin sadarwa a kasar.

Za a dauki 'yan banga aiki saboda matsalar tsaro

Gwamnonin jihohin arewa maso yammaci da kuma tsakiyar Najeriya na niyyar ɗaukan ɗaruruwan ƴan bijilanti ko ƴan banga na musamman don taimaka wa jami'an tsaro a yaƙin da ake yi da ƴan fashin daji.

Ranar Talata 21 ga watan na Satumba ne Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ne ya sanar da cewa shi da takwarorinsa na wasu jihohin yankin suka amincewa da matakin ɗaukar 'yan banga dubu uku don tunkarar 'yan fashin.

Jihohin sun hada da Zamfara da Sokoto da Kebbi da Kaduna da Neja da kuma Nasarawa.

Waɗannan jihohin sun daɗe suna fama da matsalolin yan fashin daji da masu garkuwa da mutane don kuɗin fansa da dai sauransu.

Soja ta ci zarafin 'yar hidimar kasa a jihar Cross River

An ta yada wani bidiyo a shafukan sada zumunta wanda ya nuna wata soja mace tana sheka wa wata mace mai sanye da kayan 'yan hidimar kasa, ruwa mai datti.

Bidiyon ya janyo muhawara kuma 'yan Najeriya da dama sun yi alla wadai da cin zarafin. Sun kuma bukaci da a sake duba irin al'adar da mafi yawan 'yan Najeriya masu mukami ke da ita ta tozarta mutanen da suka fi matsayi.

Rundunar sojan Najeriya ta fitar da sanarwa tana tir da tozarcin da aka yi wa mai yi wa kasar hidima kuma ta ce ta ƙaddamar da bincike kan lamarin sannan za a hukunta sojar yadda ya dace.

Ƴan Najeriya da dama dai na ta kira da a bi wa matar haƙƙinta kuma a biya ta diyyar tozarcin da aka yi mata.

Karin labaran da za ku karanta: