Hotunan Afirka na mako 17-23 Satumban 2021: Rawa a Sahara da dokunan karfe

Wasu matasa yan Jamhuriyar Nijer daga Fouduk da suka dauki kayatattun hotuna a wani bikin al'ada na Cure Salee da a ka saba yi a Nijer.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu matasa yan Jamhuriyar Nijer daga Fouduk da suka dauki kayatattun hotuna a wani bikin al'ada na Cure Salee da a ka saba yi a Nijer.
An wallafa
Dubbai ne suka halarci bikin kwanaki uku na makiyaya da suka hada da sukuwa kan rakuma.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Dubbai ne suka halarci bikin kwanaki uku na makiyaya da suka hada da sukuwa kan rakuma.
Gungun wasu maza ke hutawa bayan sun kwashi rawa a lokacin bikin Cure Salee a arewacin Jamhuriyar Nijer.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Gungun wasu maza ke hutawa bayan sun kwashi rawa a lokacin bikin Cure Salee a arewacin Jamhuriyar Nijer.
Nan ma dai bikin Cure Salee ne inda wasu mata ke tikar rawa. Biki ne da ke zuwa karshen daminar kowace shekara

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Nan ma dai bikin Cure Salee ne inda wasu mata ke tikar rawa. Biki ne da ke zuwa karshen daminar kowace shekara
Ba mazauna yankin da bikin Cure Salee ke faruwa ba kawai hadda baki sun baje kolinsu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ba mazauna yankin da bikin Cure Salee ke faruwa ba kawai hadda baki sun baje kolinsu.
A Najeriya mai makwabtaka wani makeri Anjorin Jimoh a bakin aiki a birnin Lagos.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A Najeriya mai makwabtaka wani makeri Anjorin Jimoh a bakin aiki a birnin Lagos.
Nan kuma wani mai fasahar kere-kere ne Mohamed al-Sharaiti ya sassaka dokin karfe ta amfani da lalatattun kayan motoci.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Nan kuma wani mai fasahar kere-kere ne Mohamed al-Sharaiti ya sassaka dokin karfe ta amfani da lalatattun kayan motoci.
Wasu makada da ake kira 'Fulu Miziki daga Afrika ta Tsakiya a lokacin da suka halarci wani bikin al'ada a Sfaniya ranar Talata.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu makada da ake kira 'Fulu Miziki daga Afrika ta Tsakiya a lokacin da suka halarci wani bikin al'ada a Sfaniya ranar Talata.
Yar wasan fina-finan Afrika a Kudu Thuso Mbedu a lokacin da takwararta yan Amurka Mychal-Bella Bowman yayin bikin kyaututtukan gwarazan shekara na Emmy Awards a Los Angeles ranar Juma'a.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Yar wasan fina-finan Afrika a Kudu Thuso Mbedu a lokacin da takwararta yan Amurka Mychal-Bella Bowman yayin bikin kyaututtukan gwarazan shekara na Emmy Awards a Los Angeles ranar Juma'a.
Ditebogo Ledwaba yayin da ta lashe kyautar matashiyar yar wasa a bikin Royal Soapie a Afrika ta Kudu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ditebogo Ledwaba yayin da ta lashe kyautar matashiyar yar wasa a bikin Royal Soapie a Afrika ta Kudu.
A ranar Laraba ne Somaliya ta fara nuna fina-finai a gidan kallo bayan shekaru 30. Da dama sun yi maraba da hakan kuma suna fata ya zama silar farfadowa da al'ada duk da shafe shekara da shekaru a na fama da rashin tsaro a kasar. Amma a na yi wa masu kallo binciken kwa-kwaf kafin su shiga gidan kallon na Mogadishu saboda tsaro.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Laraba ne Somaliya ta fara nuna fina-finai a gidan kallo bayan shekaru 30. Da dama sun yi maraba da hakan kuma suna fata ya zama silar farfadowa da al'ada duk da shafe shekara da shekaru a na fama da rashin tsaro a kasar. Amma a na yi wa masu kallo binciken kwa-kwaf kafin su shiga gidan kallon na Mogadishu saboda tsaro.
A birnin Cairo na Masar, Taha Obied yana ciyar da kazarsa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A birnin Cairo na Masar, Taha Obied yana ciyar da kazarsa.
Nan ma Masar ne inda a ka fara cire auduga. Kamar yadda ku ke gani yara ne a nan su ke wasa kan auduga da a ke aiki a kanta.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan ma Masar ne inda a ka fara cire auduga. Kamar yadda ku ke gani yara ne a nan su ke wasa kan auduga da a ke aiki a kanta.
Dan wasan damben Kamaru Tafon Nchukwi ya kai wa Mike Rodriguez naushi, a wasan damben UFC a birnin Las Vegas na Amurka ranar Laraba.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dan wasan damben Kamaru Tafon Nchukwi ya kai wa Mike Rodriguez naushi, a wasan damben UFC a birnin Las Vegas na Amurka ranar Laraba.
Yar wasan tseren Burundi Francine Niyonsaba ta dawo gida ranar Talata inda ta samu kyakkyawar tarba, bayan kafa sabon tarihin tseren mita 2000 na mata.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Yar wasan tseren Burundi Francine Niyonsaba ta dawo gida ranar Talata inda ta samu kyakkyawar tarba, bayan kafa sabon tarihin tseren mita 2000 na mata.
A Italiya kenan ranar Asabar, inda dan wasan tseren Kenya Clement Langat Kiprono ya lashe gasar Tsere ta Rome a ranar 19 ga watan Satumba

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Italiya kenan ranar Asabar, inda dan wasan tseren Kenya Clement Langat Kiprono ya lashe gasar Tsere ta Rome a ranar 19 ga watan Satumba
A ranar Laraba yan Kamaru suka bukaci a dawo musu da kayan tarihinsu da Jamus ta wawashe a lokacin mulkin mallaka.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Laraba yan Kamaru suka bukaci a dawo musu da kayan tarihinsu da Jamus ta wawashe a lokacin mulkin mallaka.
Sauran tattakar hoton tsohon Shugaban Algeria AbdelAziz Boutaflika wanda ya mutu ranar 17 ga watan Satumba yana da shekaru 84.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sauran tattakar hoton tsohon Shugaban Algeria AbdelAziz Boutaflika wanda ya mutu ranar 17 ga watan Satumba yana da shekaru 84.
A nan kuma yan Guinea ne ke murnar dawowar wani jagoran adawa a kasar bayan kifar da gwamnatin Alpha Conde.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A nan kuma yan Guinea ne ke murnar dawowar wani jagoran adawa a kasar bayan kifar da gwamnatin Alpha Conde.
Ranar Talata kenan a dai-dai lokacin da rana ke faduwa a kogin Blue Nile da ke arewacin Khartoum a Sudan

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Talata kenan a dai-dai lokacin da rana ke faduwa a kogin Blue Nile da ke arewacin Khartoum a Sudan