Kwalara ta kashe kusan mutum 50 a Maradi

An wallafa

A Jamhuriyar Nijar, kusan mutum 50 ne hukumomin lafiya a ƙasar suka ce sun mutu sakamakon cutar amai da gudawa a jihar Maraɗi.Sai dai, mahukuntan sun ce duk da haka ana samun ci gaba a yaƙin da ake yi da annobar.Sama da mutum 2,700 ne dai cutar ta kwantar a jihar ta Maraɗi, mafi yawansu kuma a yankin Mada-Rounfa. Lafiya Zinariya: Rawar da mata za su taka wajen yaki da cutar kwalara

Jami'in kula da lafiya a ma'aikatar kiwon lafiya ta jihar Maradi Malam Tsayyabu Lawwali, ya shaida wa BBC cewa rashin zuwa asibiti a kan kari ne ya janyo yawan mace-macen.Ya ce,"Ba a saurin kawo mutanen da suka kamu da cutar amai da gudawa asibiti da wuri don a basu kulawar data dace, yawanci sai marassa lafiyar sun galabaita ake kawo su asibiti.

Sannan kuma akwai wadanda dama can suna dauke da wata cuta kana kuma kwalara ta shige su".

Jami'in kula da lafiyar ya ce to amma duk da haka a yanzu ana samun raguwar masu kamuwa da cutar saboda matakan kariyar da aka dauka, ciki har da raba kwayoyin da ke tsaftace ruwan sha wato wanda ke kashe kwayoyin cuta a dukkan yankunan da annobar tayi kamari, haka kuma an je gidajen wadanda suka kamu da cutar an yi feshin kashe kwayoyin cuta.

Malam Tsayyabu Lawwali, ya ce haka wuraren da ake kwantar da marassa lafiyar ma a kodayaushe ana tsaftace su.

Jami'in kula da lafiyar ya kuma ja hankalin shugabannin al'ummaa yankunan da cutar tafi kamari dama inda cutar bata bulla ba a kan su ci gaba da wayar da kan jama'a a game da yadda za a kare kai daga kamuwa da cutar amai da gudawa, da kuma yadda da zarar mutum ya kamu za a hanzarta kai shi asibiti mafi kusa.