World Refugee Day: Ƙalubalen da ƴan gudun hijira suke fuskanta a Najeriya

An wallafa

A kowacce 20 ga watan Yuni ce ranar masu gudun-hijira, wadda majalisar dinkin duniya ta keɓe don nazarin halin da suke ciki da hanyoyin inganta musu rayuwa.

Wasu alƙaluma sun nuna fiye da mutum miliyon 26 ne suke gudun-hijira a duniya.

Najeriya na cikin ƙasashen da suke fama da mutanen da rikici ya raba da gidajensu, musamman ma jihar Borno wadda mahukunta suka ce fiye da mutum miliyan ɗaya ne rikicin boko haram ya ɗaiɗaita.

Mazauna sansanonin gudun-hijira a jihar Borno dai sun bayyana cewa suna samun kulawa, amma komai daɗin sansani gida ya fi shi.

Malama Amina Bulama wadda ta shafe shekara bakwai a sansanin Kawarmaila da ke jihar Borno, ta shaida wa BBC irin ƙalubalen da suke fuskanta.

'Muna fatan komawa garinmu wata rana'

A cewarta, tana da yara takwas kuma dukkansu har da mai gidanta da kuma mahaifiyarta suna kwana ne a daki ɗaya saɓanin yadda suke zaune a garinsu na asali.

Ta kuma yi fatan ganin sun koma garuruwansu na asali. Ta kara da cewa yaranta na samun kulawa a makarantun da suke zuwa sannan suna da asibiti a sansanin inda ake kula da lafiyarsu.

Shi ma Alhaji Mustapha, tsohon attajiri da ya samu karayar arziki sakamakon rikicin boko haram ya ce gida ya fi nan saboda a gida suna iya yin noma ba tare da wata matsala ba.

"Muna ganin abin ya yi sauki ba ma jin irin kamar na da, in Allah Ya yarda za mu koma bana za a yi noma sosai", in ji Alhaji Mustapha.

Mallam Bukar Alhaji Bukar, Sakataren sansanin, ya ce zuwa yanzu yawan ƴan gudun hijrar da ke Ƙawarmaila sun kai kusan dubu uku sabanin a farko da ba su wuce mutum 20 zuwa 30 ba.

Ita kuwa Fatima Muhammad wadda ta kammala karatun sakandare kuma take da burin zama likita ko lauya ta ce tana fuskantar ƙalubalen ci gaba da karatu saboda rashin damar zurfafawa.

Mahukunta a jihar Borno dai sun bayyana cewa suna daukar matakai don inganta rayuwar al`umar jihar ciki har da masu gudun-hijira.

Dr Mairo Mandara, mai bai wa gwamnan jihar shawara a kan ayyukan jin ƙai da ci gaban al`umma, ta ce "muna gina musu gidaje fiye da gidajen da suka bari tun da farko" sannan gwamnati na ba su jari.

"Kowane namiji ana ba shi jarin naira dubu 100, kowace mace a bata jarin naira dubu 50 domin (su) samu abin yi". in ji Dr Mandara.

Ƙarin haske

Sansanonin ƴan gudun-hijira sun yi wa birnin Maiduguri kawanya wadanda gwamnati da ƙungiyoyin agaji ke ɗawainiya a kansu.

Irin waɗannan sansanoni dai cike suke da marayu da matan da mazajensu suka rasu da kuma ƙananan yara da mafi yawa a nan aka haife su don haka ba su san daɗin gida ba.

Kuma idan ba su samu kulawa ba, a cewar masana, suna iya kasancewa wata babbar barazana.