Zababbun hotuna masu kayatarwa daga Afrika da sauran sassan duniya.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Abokai na wasan kwallon maraice a ranar Alhamis a Soweto, da ke Afrika ta kudu.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, A wannan ranar ne, mai zane yar kasar Congo mai suna Sandra Mujinga ta gabatar da aikinta mai taken, Reworlding Remains yayin baje kolin zane a Jamus
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Tauraruwar fina-finai 'yar kasar Kenya Lutipa Nyong'o ta isa birnin New York don halartar bikin kayan kawa na Meta Gala a ranar Litinin da maraice.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Mai sayar da kayan kawa yar kasar Somali Iman na sanye da kaya masu samfurin zinare itama ta halarci taron.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Kamar yadda ita ma jaruma 'yar kasar Canada da Uganda Whitney Peak tayi, wacce ta fito fim ɗin Gossip Girl.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Haka kuma a birnin New York , jakadiyar majalisar dinkin duniya Victoria Sulimani ita ma ta bi sahun a taron kayan kawa na Rise Survivors' Fashion show.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Vegedream ya yi wa wata waka a wajen taron mawaƙa na Urban Music of Anoumabo (Femua) a Ivory Coast a ranar Asabar.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Mawakin yana cikin manyan mashahurai a taron baje kolin da aka yi na kwana biyar.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Hakanan tauraron kasar Kongo Koffi Olomide shi ma ya gabatar da tasa wakar.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Kamar yadda wata 'yar rawa 'yar kasar Kamaru Daphne itama ta yi.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Sama da mako kenan bayan da aka yi masa juyin mulki, hoton Shugaba Alpha Conde na rataye a kofar shiga People's Palace inda gwamnatin wucin gadin za ta gana da yan siyasa da ma'aikatan gwamnati a ranar Litinin.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Haka kuma a babban birnin kasar Konakry, wannan hoton shugaban rikon kwarya Col Mamady Doumbouya ke manne a kan titunan kasar.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Kusan kimanin gidaje hamsin ne ambaliyar ruwan ta rutsa da su a kudancin Sudan, inda Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutun dubu sittin da biyar ne suka rasa gidajensu, ciki harda da 'yan gudun hijira daga kudancin Sudan.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, A ranan Lahadi ne Ranar Lahadi, ƴan Tunisia sun hada wata sarka ta mutane a lokacin wata zanga-zanga kan karuwar gurbatar tekuna a Tunis, babban birnin kasar.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, A Habasha ranar Talata, wani dan bindiga na yankin Amhara ya daga bindigarsa don a dauke shi hoto.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, A Addis Ababa, mutane na gudanar da addu'o'i don kawo karshen yakin da ake yi a yankin Tigray, gabanin bukukuwan sabuwar shekara...
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Mutane na shan lemun Tej a wata kasuwa a Addis Ababa. Lemo ne da ake sha a lokacin bikin sabuwar shekara a Ethiopia kuma ana hada shi ne da zuma da ruwa da ganyen bishiyar Gesho.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Wata akuya na leƙowa daga cikin wata mota a Hargeisa, babban birnin Somaliland ranar Laraba
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, A lokaci guda kuma, wannan mutumin na tare da rakumansa a wata kasuwar sayar da dabbobi
Asalin hoton, EPA
Bayanan hoto, Wani mutum yana hawa bishiyoyin dabino a Masar.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Wadannan gumakan a wani wurin ajiye kayan tarihi a Paris, mai suna Royal Treasures of the Abomey Kingdom, na cikin wasu gumaka 26 da za a mayar Benin a karshen shekarar nan.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Ranar Talata, wani mutum na fitowa daga wata makabarta da aka gama gyarawa wadda kuma aka gina tun karni na 27 kafin haihuwar Annabi Isa
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Nan ne kabarin wani tsohon sarkin Masar Pharaoh Djoser wanda sunansa ke rubuce a jiki.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Wannan hoton da aka dauka ranar Lahadi na nuna daji mafi girma a Najeriya- dajin Oban a garin Calabar - wanda ke da tarin giwaye da birrai.