Zamantakewa: Tasirin abokan miji a kanka da rayuwar iyalinka

An wallafa

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashi na 13, shirin ya yi duba ne kan abota, yadda yake da yadda ya kamata maza su kula da mu'amalarsu da abokansu da tasirinsu a rayuwar gidajensu.

Kamar yadda muka fada a makon da ya wuce, kowa a duniya na bukatar aboki, domin abokai nagari tamkar duwatsun alfarma suke, don suna taimaka mana a rayuwarmu.

Yallabai kana bukatar abokai ko don inganta lafiyar kwakwalwarka, amma fa ka sani akwai iyaka ta zakewarsu a cikin rayuwarka da ta aurenka.

Wane ne aboki?

Aboki shi ne mai sonka tsakani da Allah ba don wani abu da ka mallaka ba, wanda zai tsaya maka a al'amuranka duk runtsi.

Aboki na gari shi ne wanda ba zai juya maka baya ba ko da ka samu kanka a wani sammatsi. Mai tsayawa ya taya ka bakin ciki a lokacin damuwa, ya kuma taya ka dariya lokacin farin ciki.

Aboki na gari shi ne mai rike amana, mai gaya maka gaskiya ko da tana da daci, sannan ko ka yi fushi da shi kan hakan shi ba zai yada kai ba.

To wane irin zama ya kamata ka yi da abokanka?

1. Ka tabbatar kuna tuntubar juna akai-akai, dadewa ba a hadu ba ko dadewa ba a yi magana ba kan sa zuciyoyi su yi nauyi su ji kamar kun yada juna ne.

Kownne zai dinga zargin dayan ya yada shi ko sauyin rayuwa ya sa ya manta.

2. Yin taka tsantsan da gudun wuce gona da iri

Ku dinga taka tsantsan da gudun tunzura juna, bai kamata ku dinga saurin hasala ba nan da nan. Idan kuka yi wa juna laifi, to ku warware ku sasanta ba tare da wani ya ji ba.

Sannan ku sani a kowane lamari da kowace mu'amala akwai iyakoki, kuma ya kamata a kula da su kar a ketare su kar a take su.

Kar ka zake da shiga wasu lamuran abokinka musamman wadanda bai saka ka a ciki ba, sannan kar ka dinga tunzura shi a kan abubuwan da ka san ba daidai ba ne, kamar hidimarsa da iyalinsa.

3. Ka guji bude cikinka ga sabbin abokai

Bai kamata a ce kowane zance da ya shafi iyalanka sai ka kai wa abokai ba. Ya kamata ka sani iyalinka sirrinka ne. Kar ka zama mai tona musu asiri a wajen abokai.

Idan laifi iyalinka ta yi maka ba a hana ka neman shawara ba, amma fa ka kula kar ka dauki shawarar da za ta kai ka ta baro.

4. Ku zama masu kyautata wa juna ta kowane bangare. Yi wa juna abin alheri da tsaya musu a kan lamurransu.

Kar ku sanya gasa tsakaninku, hakan na jawo kyashi da hassada da bakin ciki, lamarin da ka iya kai wa ga cin amana.

5. Kar ka yarda rudin abota ya sa ka ki mayar da hankali wajen bai wa matarka hakkokinta. Don sau da yawa wasu kan fifita abokai fiye da yadda suke fifita matayensu.

Ka kula da lokutan da za aka dinga bai wa abokai. Kar ka dinga shantakewa a majalisa wajen hira kana barin matarka ita kadai a gida ba abokin debe kewa.

Kar ka zama mai kwasar abokai a ko da yaushe kana kai su gidan babu tsari.

Hakan kan jawo wasu abokan da ba su da kan gado su mayar da gidanka majalisar shantakewa, ta yadda ko ba ka nan za su je su takurawa iyalinka, watalkila daga haka sai rashin sabani ya shiga tsakanin matarka da aboki, ko kuma a wasu al'amuran masu muni ka ga sun kai ga fara neman juna.

Kar ka bai wa aboki damar da zai yi dumu-dumu a cikin ala'muranka ta yadda har matarka za ta dinga shiga damuwa, sannan kuma kar ka bari matarka ta raba ka da abokanka domin kowa da ranarsa.

Wasu na baya da za ku so ku karanta

To ko yaya mata suke so mu'alamar mazajensu da abokai ta kasance a tsarin da hankali zai dauka?

Husnah Kamshi, wata mai sharhi ce a kan zamantakewa, kuma ga abin da ta ce:

Ni a matsayina na mace me aure bazan ce zan raba mijina da abokan sa ba, amma ina son ya kasance me kula da hakkin Allah da ke kansa.

Ya yi mu'amularsa da su wadda ta shafe su walau harkar kasuwanci, walau abokai ne tun na kuruciya, amma ya san duk wani hakkinsa da lokutan dawowarsa gida.

Ko da za su zauna a majalisa to ya tabbatar da cewar matar shi ba ta da wani muhimmin bukatar shi a kusa da ita.

Sannan ya kasance mai yawan ba ta kulawa ba sai kullum ba dare ba rana yana wurin abokai ko yawan fadar sirrin cikin gidansa wurin abokai har su dinga kallon matarsa kamar sakarya ba.

Hakan zai sa su dinga zuge shi da wasu kalamai wadanda sam ba su dace da abokan arziki ba.

To a gaskiya dai ya kamata ya zamto gurbin su daban a wurinsa na iyalin sa daban, domin duk mutumin da zai kasance ba shi da sirri tsakanin sa da iyalinsa har sai abokai sun ji, to Manzon Allah SAW ya ce wannan shi ne "Dayyus", wanda ba shi da kish,i kuma ba zai taba jin kamshin aljanna ba.

Don haka ya kamata a ce maza sun gyara tsakanin su da abokansu da kuma iyalansu, domin shi aboki na gari jigo ne a rayuwar dan adam kuma suna da matukar muhimmanci ga mazajenmu.

Duk lokacin da aka ce mutum ba shi da aboki to tabbas zai kasance a cikin wani irin yanayi , sannan ko da yau a ce mijinki ya kwanta dama zai kasance ba ki da wasu masu tallafa miki ko yaranki, don haka aboki yana da muhimmanci a tsakanin mazajen mu.

Ga wasu 'yan abubuwa da za ku rike

Kar ka bari don kana kut da kut da aboki ka ce zai zama kut da kut da matarka, za ka ji a salansa

Ka rike abokanka da zuciya daya ka zauna da su lafiya, don wata rana in ba ranka za su iya kula da bayanka

Ƙarin wasu da za ku so