Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yara sama da miliyan daya za su daina zuwa makaranta a Najeriya - MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai yiwuwar yara miliyan daya a Najeriya su daina zuwa makaranta saboda barazanar da suke fuskanta ta sace daliban makarantu da aka yi a kasar a wannan shekara.
A ranar Laraba Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wannan sanarwa inda ta ce, 'yan bindiga sun sace sama da yara 1,000 a makarantu domin karbar kudin fansa a arewacin Najeriya tun daga watan Disamba yayin da wasu da dama suke hannu har yanzu.
Asusun ba da tallafin ƙananan yara na MDD ya ce an kai hare-hare 20 kan makarantun Najeriya a wannan shekarar kuma an saci yara 1,400, yayin da aka kashe 16.
An saki mafi yawan cikinsu bayan biyan fansa bayan kwashe makwanni ko kuma watanni a hannun 'yan fashi, inda ake ajiye su a wasu sansanonin da ake yi a dazuka.
"Iyalai da al'umma sun kasance cikin tsoro da firgicin aika 'ya'yansu makaranta saboda yawan hare-haren da ake kai musu da kuma yadda ake sace daliban," kamar yadda MDD ta bayyana.
Sama da daliban Najeriya miliyan 37 ne za su shiga sabon aji a farkon wannan watan, in ji MDD, yayin da aka yi kiyasin yara miliyan daya ba za su koma ba.
Wasu jihohin kasar sun rufe makarantu na wani dan lokaci bayan sace dalibai a jihohin.
Yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya sun dade sun dauki matakin ba sani ba sabo tsakanin manoma da makiyaya da ke rikici kan kasar noma da ruwa.
Hare-hare na karuwa ne saboda karuwar makamai a hannun 'yan bindiga, wadanda ake kira da 'yan fashin daji, wadanda ke yawan kai hare-hare kauyuka tare da sace shanu da kuma mutane domin kudin fansa.
'Yan fashin dajin sun saci yaran sakandire da na kwaleji a arewacin Najeriya, sun rika shigar da su dajin tare da boye su har sai an biya su kudade.
Kimanin yara 70 aka sace kimanin makonni biyu da suka gabata, an kuma sake su a wannan makon a JIhar Zamfara, inda sojojin Najeriya suka fara kaddamar da hare-hare kan 'yan bindigar dajin.