Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mata a Afghanistan sun nuna goyon bayansu ga mulkin Taliban
Wasu mata ƴan Afghanistan sanye da niƙabi sun zauna a sahun gaba a aji a wata jami'a a Kabul ranar Asabar, don nuna goyon bayansu ga dokokin Taliban masu tsauri kan raba mata da maza a wurin karatu.
Kusan matan 300- rufe ruf tun daga sama har ƙasa kamar yadda sabuwar dokar sanya tufafi ta tanada- sun ɗaga tutotin Taliban a lokacin da wasu ke jawabin nuna kin jinin Yamma tare da nuna goyon bayansu ga dokokin Musulunci.
Wasu daga cikinsu sun sa shuɗin burqa, mai ɗan raga-raga a wurin idanu, amma mafi yawansu sun sa niƙabi ne mai rufe duka fuskan ban da idanu.
Da yawa daga cikinsu kuma sun sa safar hannu baƙa.
Haƙƙoƙin mata sun fuskanci koma baya sosai ƙarƙashin mulkin Taliban tsakanin 1996 zuwa 2001, amma tun dawowa mulki a watan jiya kungiyar ta ce a wannan karon ba za ta tsaurara ba.
A wannan karon, za a bai wa mata damar zuwa jami'a muddin ba za a hada su aji da maza ba ko kuma a sa labule a tsakaninsu, a cewar hukumar da ke kula da ilimi ta Taliban.
Haka kuma dole ne su sanya hijabi da niƙabi.
Matan, waɗanda ɗalibai ne sun saurari jawabai a Jami'ar Shaheed Rabbani a Kabul, babban birnin ƙasar.
An kafa manyan tutotin Taliban a babban dandamali yayin da matan da ke jawabi ke sukar matan da ke gudanar da zanga-zanga a Afghanistan a kwanakin nan.
Haka kuma, sun kare sabuwar gwamnatin ta Afghanistan, wadda ta haramta zanga-zanga sai da izinin ma'aikatar shari'a.
Daud Haqqani, wani babban jami'i a ma'aikatar ilimi ya ce matan ne da kansu suka shirya zanga-zangar bayan sun nemi izinin kuma aka ba su.
"Ba ma goyon bayan matan da ke zanga-zanga a titi ne, suna ikirarin cewa su wakilan mata ne," a cewar daya daga cikin matan wadda ke rufe daga sama har kasa.
"Ƴanci ne goyon bayan gwamnatin da ta shude? A'a ba ƴanci ba ne. Gwamnatin da ta shuɗe sun ci mutuncin mata. Sun riƙa amfani da mata saboda kyawunsu," a cewarta.
Wata ɗaliba mai suna Shabana Omari ta shaida wa taron cewa ta amince da manufofin taliban na sa mata rufe jikinsu.
Waɗanda ba sa sanya hijabi na cutar dukanmu," ta ce.
"Hijabi ba zaɓin mutum ɗaya ba ne."
Ta kammala jawabin nata da faɗin 'Allahu Akbar" inda daga baya sauran matan su ma suka ɗauka.
Bayan gabatar da jawaban a ɗakin taron, matan sun fita bakin titi riƙe da kwalaye kuma kewaye da sojojin Taliban masu ɗauke da manyan bindigogi.
Ƙungiyar Taliban ta ce tana so ta nesanta kanta daga manufofinta na baya masu tsauri, bayan kusan rabin al'ummar ƙasar ba su da damar yin aiki ko samun ilimi.
Ƙarƙashin sabbin dokokin, mata na iya aiki "ƙarƙashin tsarin addinin Musulunci", a cewar Taliban amma ba su ba da cikakken bayani kan abin da hakan ke nufi ba.