Real Madrid: Ƙungiyar ta koma ta 'yan wasan da ba na Spain ba

An wallafa

Watakila masu tsaron bayan Real Madrid daga gefen hagu 'yan Sifaniya, su ne kadai za su dinga yi wa kungiyar wasa a kaka mai zuwa.

Dani Carvajal da kuma Lucas Vazquet ne 'yan Sifaniya da ke buga gurbin da za su taka leda karkashin Carlo Ancelotti a kakar da za a fara. Sai kuma Alvaro Odriozola, idan ya sa kwazo, cikin 11 da za su dinga fara yi wa Real tamaula.

Sergio Ramo da zai bar kungiyar a karshen watan nan ya rage yawan 'yan wasan gida da suke buga wa Madrid tamaula, wadanda a baya su ne suka mamaye kungiyar da tawagar Sifaniya.

Wadanda ake sa ran za su maye gurbin Ramos ba 'yan Sifaniya ba ne da suka hada da David Aalaba da kuma Eder Militao.

Sai dai watakila Nacho Fernandez ya samu dama duk da cewa da jan aiki a gabansa.

Sauran wadanda za su yi wa Real Madrid tamaula daga kakar badi za su kasance daga waje suke da suka hada da mai tsaron raga, Thibaut Courtois da mai tsaron baya daga gefen hagu, Ferland Mendy.

Masu buga tsakiya kuwa sun hada da Casemiro da Toni Kroos da Luka Modric, yayin da Martin Odegaard da kuma Fede Valverde za su yi ta neman damar buga gurbin.

Dan kasar Sifaniya da zai iya buga gurbin gaba na masu cin kwallo bai wuce Marco Asensio ba, amma zai yi takara ne da irin su Karim Benzema da Eden Hazard da kuma Vinicius Junior.