Harajin VAT: Muhawara ta barke tsakanin 'yan Najeriya kan daina raba harajin jihohi

Buhari, Wike and San Olu

Asalin hoton, BBC/Gov

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Ana ci gaba da musayar yawu tsakanin 'yan Najeriya kan tsarin karbar kuɗaɗen harajin kayayyakin more rayuwa a faɗin kasar VAT.

Da yawa daga cikin 'yan kasar da suka fito daga yankin kudu na nuna goyon bayan kan tsarin da jihar Legas da Rivers suka fito da shi inda suke so su rika karbar harajin da jihohinsu suka karba maimakon bai wa gwamnatin tarayya.

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ne yake kan gaba a kan wannan fafutika ta neman ba su damar rike harajin da jihohinsu suke samarwa.

Alkaluma sun nuna cewa jihohin kudancin Najeriya sun fi samar da kudaden shiga wadanda gwamnati ke rarrabawa jihohi a karshen ko wanne wata, idan aka kwatanta da abin da jihohin arewaci ke tattarawa.

Wasu Jihohin kudancin sun bukaci a ba su damar karɓar kuɗaɗen haraji a matakin jihar domin kara musu kuɗaɗen shiga.

A kafafen sada zumunta, ra'ayoyi sun sha bambana game da batun.

Mutane da yawa sun nuna goyon bayan a sauya fasalin karbar kudaden harajin, wasu kuma sun nuna rashin amincewa da tsarin.

Wani da ake kira Hydra a Twitter ya ce "Idan Wike ya samu nasara a yakin da yake da hukumar tattara kudin harajin ta kasa, hakan zai bude wata hanya ga jihohin kasar wajen samun 'yancin cin gashin kai na bangaren kudi a karkashin mulki federaliyya.

Ya kara da cewa "Me ya sa zinaren da ake hakowa a Zamfara ya zama mallakin Zamfara amma man da ake hakowa a Bayelsa ya zama na gwamnatin tarayya?

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

A take wani mai amfani da Twitter da ake cewa Promisejob ya mayar masa da martani inda ya ce," Jihar Rivers na daga cikin jihohin da ke samar da mai, amma hakan ba zai yiwu ba, ba tare da hadin kan 'yan Najeriya ba, kamata ya yi kasa ta amfana da arzikinta. Lokaci zai zo da mai zai zama ba shi da wata daraja, lokacin kasar za ta mayar da hankali kan zinare ko kuma wasu albarkatun kasa, Wannan ita ce Najeriya daya.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Tsohon mataimaki na musamman kan kafafen yada labarai ga gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasai, ya nuna goyon bayansa ga Gwamnan jihar Rivers Wike, a wani sakon Twitter da ya wallafa.

Ya ce "Duk mutumin da yake sukar Wike kan maganar haraji ba ya son ci gaban yankin. A kan wannan maganar ina tare da Wike 100 bisa 100. Wannan wani lokaci ne da ya kamata mu nutsu mu yi wani bincike kan yadda za a kara farfado da harkokin tattalin arzikin kasarmu. A gani na wannan wata zaburarwa ce da kuma yin kira ga shugabannin arewa da masu bibiyarta.

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Yusuf Tukur ya tambayi Dawisu, "Shin Malam Dawisu ka fahimci me ake nufi da kuɗaɗen haraji? Masu sayen kayayyaki ne suka samar da haraji. Misali, idan Kano tana sayen mafi yawan abun da aka samar a jihar Rivers, hakan na nufin mutan Kano sun fi taimakawa wajen tara kudaden haraji sama da na Rivers. Saboda wanda ya sayi abu a karshe domin amfani da shi, shi ne ke samar da kudin shiga.

Haka dai masu amfani da kafafen sada zumunta a Najeriyar ke ta musayar ra'ayi, amma salon ce-ce-ku-cen da ake yi 'yan Kudu na kare yankin haka zalika yan Arewa suma na kare yankinsu.

Mene ne Asalin wannan jayayya?

Najeriya na tsarin karbar haraji da ake kira VAT, wanda haraji ne kan kayayyakin more rayuwa da ake iya ganinsu wanda gwamnati ke karɓa karkashin tsarin karɓar harajin haɗin-gwiwa tsakanin gwamnatin Tarayya da na jihohi da kananan hukumomi.

To sai dai Jihohin irin su Rivers da Legas da wasu sauran jihohi hudu na Najeriya ne kawai ke samar wa kasar kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen harajin VAT a faɗin ƙasar, wani tsari da a yanzu suka ce cutarwa ce fal cikinsa.

Gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya yi korafi kan yadda ake yin kudin goro tsakanin jihohin da ke samar da mafi yawan haraji da wadanda ba sa wani taka rawar azo a gani wajen samar da kudaden haraji.

Abin da ya sa Rivers ta shigar da gwamnatin Najeriya kara gaban wata kutun tarayya kan wannan batu, kuma ta sami hukuncin da ya yarje mata hakkin karbar harajin na VAT da sauran haraje-haraje a jihar.

Jihar Legas ta bi bayan Rivers kan wannan batu. Jihohin kudancin Najeriya na son duk wani kaya ko ciniki da aka yi tsakanin yankunansu ko kuɗaɗe ya zama mallakar gwamnatin jihar domin gudanar da ayyukan ci gaba.

Inda suke ganin karba a raba tsakanin jihohi 36 na kasar ci da guminsu ne.

Wasu jihohin da ke fafutikar ganin tsarin ya sauya na cewa hakan ya saɓa dokar tattara kuɗaɗen haraji na VAT, saboda akwai take hakki a ciki.

Me masana shari'a ke cewa?

Barista Abdullahi Muktar, wani mai karatun digiri na uku a jami'ar Walton ta Ingila, ya yi wa BBC karin bayani game da hukuncin kotun kan irin bukatun da mai shari'ar ya amince wa jihar ta Rivers.

"Wannan hukunci abu ne mai girma, domin a fahimta ta wannan rikicin ba rikici ne kawai na hukumar tara haraji ta kasa ko da gwamnatin tarayya ba, ni ina ganin cewa dukkan sauran jihohi da suke amfana daga wannan haraji na VAT da sauran haraji da ake tattarawa na sauran kaya wanda ake raba wa na asusun tarayya ya kamata su shigo wannan batu.

"Domin da zarar an kai FIRS ko gwamnatin tarayya kasa to suma jihohin durkushewa za su yi, wasu ko an kira sunansu ba za su iya amsa wa ba," in ji Barista Muktar.

Ko da aka tambaye shi to mecece mafita game da wannan hukunci da aka yanke sai ya ce "Mafita shi ne hukumar FIRS da gwamnatin tarayya su daukaka kara, domin kuwa wannan kotu ba ta da hurumin sauraren wannan shari'a.

"Gwamnatocin da wannan hukunci zai cutar su tashi tsaye, su nemi 'yan majalisarsu su yi wa abin taron dangi, domin yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya garambawul, ya zama cewa kawai gwamnatin tarayya ce ke da wannan hurumin."

Ya kara da cewa idan ka yi duba na tsanake kan jihohin da suke hada-hada a Najeriya ba su da yawa, to hakan na nufin sauran sai su durkushe kenan?

Wannan batu dai zai ci gaba da jan hankalin 'yan Najeriya duk da yake a ranar Juma'a da yamma wata Babbar Kotun Tarayya ta dakatar da jihohin Rivers da Lagos daga karbar harajin na VAT.