Hotunan dabbobin dawa: Shin wannan ne sauron da ya fi kowanne kyau a duniya?

Asalin hoton, Gil Wizen/WPY
- Marubuci, Daga Jonathan Amos
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Science Correspondent
- An wallafa
Mutum zai cika da mamakin abin da ya gani. Wato hoton macen sauro, da kafafunta masu kyawu kuma cike da gashi.
Tana ɗaya daga cikin nau'ikan sauro da aka gano a yankin tsakiya da kudancin Amurka.
Abin kunyar a nan shi ne, wannan nau'i na sauro shi ne ya ke haddasa zazzabin cizon sauro a ƙasashe masu zafi.
Kamfanin Gil Wizen da ke birnin Ontario na ƙasar Canada ne ya dauki hoton macen sauron. An jinjina wa aikin kamfanin a yayin bayar da lambar yabo ta gasar hotunan halittun daji ta Wildlife Photographer of the Year da aka gudanar a wannan shekarar.
Idan kuka ci gaba da duba kasa za ku ga kyayatattun hotunan da aka yaba wajen daukarsu a wajen bikin gasar hotuna karo na 57.
Gil masani ne kan ƙwari, don haka ya san muhimmancin daukar hoton wadannan halittu. Kuma ana bukatar cikakken shiri da hakuri - wasu lokutan kuma da juriya kafin daukar irin wadannan hotuna.
Ya bayyana nau'in sauro na Sabethes a matsayin wadanda suke da wahalar daukar hotunansu, musamman a yankunan da ke da zafi na dajin Amazon da ke Ecuador, inda aka dauki wannan hoton.
"Sauron yana jin motsi komai kankantarsa kuma nan da nan zai tashi kafin kiftawa da bismillsah," in ji shi.
"Hakan dole ka tsaya cak ba tare da ka yi motsi ba yayin da kake son daukar hotonsa, kuma ka shirya sarai domin sauron zai iya guduwa. Abin jin dadi shi ne, yawancin ba sauro daya ba ne, don haka za ka ga sauro da yawa suna yawo a kanka.
"Wadannan saurayen suna daga cikin wadanda suka fi yada cutukan da ke da alaka da wurare masu zafi, irin su shawara da zazzabin cizon sauro. Lokacin da nake daukar hoton, wannan sauron da ma wasu sun cije ni, lamarin da yake kara hatsarin kamuwa da cutukan zazzabin cizon sauro. Amma dai ga shi ina raye!"

Hoton dila da Jonny Armstrong, daga Amurka, ya dauka

Asalin hoton, Jonny Armstrong/WPY

Idan kuka lura da yadda kafar sauro ta sauka kan kumatun Gil abin yana da kaikayi. Akwai butar sauron ya yi matukar lura da abubuwan da ke wakana a kusa da shi idan akwai bukatar ya yi saurin gudu.
Kuma tabbas akwai gashi a sauran kafarsa. Har yanzu ba a tabbatar da yadda macen sauro take jan hankalin namiji ba.
Akwai nau'ikan sauro 3,300 a duniya. Kuma masu sonsu ba su ba yawa.
Galibinmu muna lura da su sosai idan muna so mu buge su. Kuma idan muka yi kokarin yin hakan, muna ganin yadda da yawansu suke yin sauri su gudu, a cewar Erica McAlister, wata babbar masaniya gidan tarihi na Natural History Museum da ke London, wanda ya jagoranci gasar WPY.
An yi wa hoton Gil lakabi da Beautiful bloodsucker. Ga karin hotunan da aka yabawa

Hotunan Mushroom na Juergen Freund, daga Jamus/Australia
Hoton yadda mushroom take a jikin bishiyar da ke kungurmin dajin Queensland, Australia. Latsa bidiyon don kallonta

Hotunan damusa na Buddhilini de Soyza, daga Sri Lanka/Australia

Asalin hoton, Buddhilini de Soyza/WPY
Yadda damusa suke ninkaya a Kogin Talek da ke yankin Maasai Mara na kasar Kenya.

Hotunan gurbatar muhaalli na Gheorghe Popa, Romania

Asalin hoton, Gheorghe Popa/WPY
Wannan hoton da jirgi maras matuki ya dauka ne na gurbatar muhalli a Kwazazzabon Geamana da ke yankin Apuseni da ke cike da tsaunuka a ƙasar Romania.

Ranar 12 ga watan Oktoba za a sanar da hoton da ya lashe gasar shekara ta Wildlife Photographer of the Year .












