Ikigai: Kalmar da ke tasiri wajen farin ciki a rayuwa da wurin aiki a Japan

    • Marubuci, Yukari Mitsuhashi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Travel
  • An wallafa

Ga ma'aikatan kasar Japan a manyan birane, rana takan fara da wani yanayi da ake kira sushi-zume, wani salo da ake kamanta yadda masu shiga ababen hawa ke cunkushewa wuri guda a cikin jiragen kasa makare da jama'a da kuma irin yadda ake cusa shinkafa a abincin kwalamar nan na sushi.

Wahalhalun ba a nan suka tsaya ba.

Sananniyar al'adar wuraren aiki a kasar na tattabar da cewa mutane da dama kan shafe tsawon sa'o'i a ofis, da ake tafiyarwa cikin dokoki masu tsanani.

Aiki fiye da kima ba sabon abu ba ne kana a cikin ranakun mako, jiragen kasa na karshe da ke jigila da tsakar dare sukan cika makil da mutane. Wane irin fama 'yan kasar suke yi?

Sirrin hakan na iya kasancewa wani abu mai alaka da abin da 'yan kasar ta Japan ke kira ikigai. Babu fassararsa kai-tsaye da harshen Turanci, amma kuma wani salo ne da ke yin nuni da batun farin ciki na rayuwa. A gaskiyar magana, ikigai shi ne dalilin da ya sa kake tashi da sassafe.

Wadanda ke Yammacu da suka kuma san wannan ra'ayi na ikigai, ana danganta shi da zanen da'irori uku da ke kunshe da abubuwa hudu a hade da juna: abin da kake kauna, da abin da ka fi iya yi, da abin da duniya ke bukata, da kuma abin da za a iya biyanka a kai.

Amma ga 'yan kasar ta Japan, ra'ayin yana da bambanci kadan.

Ikigai daya ba shi da alaka da albashin da mutum ke samu. Ko shakka babu, wani bincike kan mutanen kasar Japan 2,000 maza da mata da hukumar ayyukan bincike ta kasar ta gudanar a shekarar 2010, ya nuna cewa kashi 31 bisa dari ne kacal na mutanen suka dauki aiki a matsayin ikigai.

Darajar wani a rayuwa ka iya zama aiki - amma tabbas ba a nan ne kadai ba.

Kallon kusa da kusa

A wata kasidar bincike ta shekarar 2001 kan ikigai, daya daga cikin marubutan, Akihiro Hasegawa, wani masani kan lafyar kwakwalwa da halayyar dan adam kana farfesa a Jami'ar Toyo Eiwa, ya danganta kalmar ikigai a matsayin bangaren ko wane abu na harshen Japananci. Yana kunshe da kalmomi biyu: iki, da ke nufin rayuwa da kuma gai, da ke nufin daraja ko kuma martaba.

Kamar yadda Hasegawa ya bayyana, asalin kalmar ikigai ya fito ne daga zamanin Heian (karni na 794 zuwa 1185).

"Gai ya samo asali ne daga kalmar kai("kwanso" da harshen Japananci) wanda ake dauka a matsyin mai daraja, kuma daga ikigai aka samu kalmar da ke nufin daraja a rayuwa.''

Akwai kuma kalmomi da ke amfani da kai: yarigai ko hatarakigai da ke nufin darajar yi da kuma darajar aiki.

Za a iya saka kalmar Ikigai a matsayin wani muhimman ra'ayin da ke hada wadannan darajoji a rayuwa.

Kama da "farinciki"

Akwai litattafai da dama a Japan da suka martaba ikigai, amma akwai guda daya musamman da aka dauka a matsayin mafi inganci: Ikigai-ni-tsuite (Game da Ikigai), da aka wallafa a shekarar 1966.

Mawallafin littafin, likitan kwakwalwa Mieko Kamiya, ya bayyana cewa a yayin a matsayin kalma, ikigai na kama da "farin ciki" amma tana da bambanci a irin yanayin sauyawarta.

Ikigai shi ne abin da ke sa ka rika tunanin makoma mai kyau, ko da kuwa a halin yanzu kana cikin halin kunci.

Hasegawa ya yi nuni da cewa a cikin harshen Turanci, kalmar rayuwa na nufin lokacin rayuwar mutum da kuma rayuwar yau da kullum. Don haka, ana fassara ikigai a matsayin dalilan rayuwa gagarumin abu ne.

"Amma a kasar Japan muna da jinsei, wanda ke nufin lokacin rayuwar mutum da kuma seikatsu, da ke nufin rayuwar yau da kullum," in ji shi.

Ra'ayi game da tsawon rai?

Japan na da mutane mafi tsawon rai a duniya - shekaru 87 ga mata da kuma shekaru 81 ga maza, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya da Kwadago da Jin Dadin Jama'a ta kasar ta bayyana.

Shin wannan ra'ayi game da ikigai ya taka rawa wajen tsawon rai?

Mawallafi Dan Buettner ya yi amanna haka ne.

Shi ne mawallafin littafin Blue Zones: Darussa kan tsawon rayuwa daga mutanen da suka dade suna rayuwa a duniya, kana suka zagaya duniya suna duba al'umomin da suka dade a duniya, wanda ya yi wa lakabi da "blue zones" wato ''shuwadan yankuna''.

Daya daga cikin wadannan yankuna shi ne Okinawa, wani tsibiri mai nisa da ke da yawan al'ummar da suka kai shekara 100 zuwa sama. A yayin da akwai yiwuwar irin nau'in abinci na musamman na da alaka da yanayin tsawon rayuwar mutanen, Buettner ya ce shi ma ikigai ya taka rawa.

"Ana alfahari da tsofaffi, suna jin cewa suna da nauyin da ke kan su na ilmantar da 'yan baya irin basirar da suke da ita," a cewarsa. Wannan yana ba su dalilai na rayuwa wajen bautawa al'ummarsu.

Kamar yadda Buettner ya bayyana, ikigai bai zama wani sabon abu ba ga mutanen tsibirin Okinawan ba

Ya ce: "Ba lallai ba ne ya kasance a cikin kalma amma kuma a duka yankunan blue zones hudu kamar Sardinia da Nicoya Peninsula, ana amfani da irin wannan ra'ayi a tsakanin mutanen masu tsawon rai".

Buettner ya bayyana cewa rubuta jerin sunayen abubuwa uku: darajarka, da abubuwan da kake son yi, da abubuwan da ka fi iyawa - tsakiyar abubuwa ukun shi ne ikigai dinka.

Ka dauki mataki

Amma kuma, sanin ikigai dinka kadai bai wadatar ba. Abu mai sauki, kana bukatar wata hanya. Ikigai shi ne "dalili na daukar mataki," in ji shi.

Mai shekaru 92, Tomi Menaka, ta ce ikigai shi ne yin rawa da waka da sa'anninta a cikin kungiyar masur awa ta KBG84, ta shaida wa jaridar Mainichi. Ga saura kuwa, zai iya kasancewa shi kansa aiki.

A cikin al'adar da darajar tawaga da zarta ta mutum daya, hankulan ma'aikatan kasar Japan sun riga sun karkata ga kasancewa masu yi wa sauran amfani, da samun godiya, da kuma kasancewa masu martaba a wurin abokan aiki, in ji Toshimitsu Sowa, Jagoran kamfanin HR Jinzai Kenkyusho.

Jagorar kamfanin daukar ma'aikata na Probity Global Search Yuko Takatota ta shafe kwanaki da mutanen da suka samu gogewar aiki da suka sauki aikin a matsayin ikigai, kamar yadda Takato ta bayyana, duka suna da abu guda iri daya: sun samu karfin gwuiwa da kuma saurin daukar mataki.

"Idan kana son fara kafa kamfani amma kana fargabar fadawa cikin abin da ba ka da tabbas a kai, ka je ga wani wanda ya riga y afara yin wani abu mai kama da abin da kake da shi ran ka."

Ta hanyar ganin yadda abin da kake son yi ke tafiya, in ji Takato, "zai ba ka karfin gwuiwa cewa kai ma za ka iya yi".

Ka yi karamin tunani

Hakan ba yana nufin cewa aiki tukuru kuma na tsawon lokaci su ne kashin bayan ra'ayi mai karfi game da ikigai ba - kusan rubu'in ma'aikatan kasar Japan na aiki na fiye da sa'oi 80 na karin lokutan aiki a ko wane wata, amma da sakamako mai muni - abubuwan na karo (mutuwa saboda aiki fiye kima) kan yi yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 2,000 a ko wace shekara.

Dalili shi ne, ikigai wani tunani ne na cewa aikinka na kawo sauyi a rayuwar mutane.

A kasidar binciken hukumar gudanarwar Wharton farfesa Adam Grant ya bayyana cewa abin da ke karfafa gwuiwar ma'aikata shi ne "gudanar da aikin da zai shafi ci gaban rayuwar sauran mutane" kana su duba ko hadu da mutanen da yanayin aikinsu ya shafa."

Hakan na nuni da daukacin rayuwa. A maimakon ka yi kokarin shawo kan matsalar yunwa, za ka iya fara da kadan ta hanyar taimaka da wani na kusa da kai, kamar kungiyar sa-kai ta yanki.

Ka raba kafa wajen zabar yin ikigai

Murabus daga aiki kan zama wani babban ab una jin kewa da rashi ga wadanda suka dauki ikigai a cikin aiki.

Wannan musamman gaskiya ne ga masu wasan motsa jiki, wadanda suke da takaitaccen lokaci a sana'arsu.

Dai Tamesue, wanda ya yi murabus daga aiki a shekarar 2012 ya bayyana a wata hira cewa tambaya mafi muhimmanci da ya yi wa kan sa bayan barin aiki ita ce: ''Shin wane buri nake son cimma daga sana'ar yin wasanni?"

"A wurin na, burin da nake son cimma ta hanyar gasar wasannin tsere shi ne in sauya tunanin mutane," "Bayan yin murabus, ya kafa kamfanin da ke tallafawa kasuwanci da ke da nasaba da wasanni.

Labarin Tamesue ya nuna yanayin yadda ikigai yake da kuma yadda ya kamata a yi amfani da shi. A lokacin yin murabus, yana da amfani ka fahimci dalilan da suka saka kake son yin abin da ya wuce karbar albashi.

Ta hanyar yin la'akari da wannan tunani, yana iya taimaka maka wajen yin cikakkiyar rayuwar jin dadi.