Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Mbappe, Ronaldo, Haaland, Saul, Richarlison, Trippier, Van de Beek, Zouma

An wallafa

Real Madrid ta gabatar da tayin fam miliyan 137 a kan dan gaban Paris St-Germain Kylian Mbappe, amma kuma kila kungiyar ta Faransa ta yi watsi da tayin na dan wasan mai shekara 22, wanda ke da ragowar shekara daya a kwantiraginsa. (Mail)

Watakila PSG ta nemi sayen dan gaban Everton da Brazil Richarlison, mai shekara 24, a matsayin wanda zai maye gurbin Mbappe. (Eurosport)

Dan gaban Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, zai nemi tafiya Manchester City a cikin makon karshe na kasuwar sayar da 'yan wasa, domin tsohon tauraron dan wasan na Manchester United bas hi da sha'awar kamala ragowar shekarar kwantiraginsa daya a kungiyar ta Italiya. (L'Equipe)

Tuni Ronaldon ya tattauna da wakilan City 'yan Portugal - Bernardo Silva da Ruben Dias mai shekara 24, da dan baya Joao Cancelo,mai shekara 27.

Kila a sa dan wasan tsakiya Silva ko dan bayan City dan Sifaniya Aymeric Laporte, dukkaninsu masu shekara 27 a musayar da kungiyoyin za su nemi su yi

City a shirye take ta biya albashin da Ronaldo zai nema amma kuma ba lalle ba ne ta yarda ta biya yawan kudin da za a san a farashinsa ba. (L'Equipe)

Manchester United na gaba-gaba wajen damar sayen dan wasan gaba na Borussia Dortmund da Norway Erling Braut Haaland a bazara ta gaba. Dan wasan na Norway mai shekara 21 ya zama daya daga cikin wadanda kungiyoyi ke rububin nemansa bayan da ya ci wa kungiyarsa kwallo 62 a wasa 63. (Bild)

Chelsea ka iya fuskantar gogayya daga Manchester United idan ta tashi tsaye domin daukar aron dan wasan tsakiya na Atletico Madrid da Sifaniya Saul Niguez, mai shekara 26 (Guardian)

Atletico Madrid na da niyyar daukar dan wasan tsakiya na Sifaniya Pablo Sarabia mai shekara 29 daga Paris St-Germain idan Saul ya tafi. (Marca)

Arsenal ta tattauna da Atletico Madrid a game da sayen dan bayan Ingila Kieran Trippier, ko da yake dan wasan mai shekara 30 zai fi son tafiya Manchester United idan ya bar babban birnin na Sifaniya. Arsenal ba za ta yarda ta sayi tsohon dan bayan na Tottenham ba a farashin da Atletico ta yi masa fam miliyan 34 ba. (Eurosport)

Dan Brazil Willian, mai shekara 33, da dan bayan Ingila Ainsley Maitland-Niles, mai shekara 23, da dan gaban Ingila Eddie Nketiah, mai shekara 22, da dan bayan Sifaniya Hector Bellerin, mai shekara 26, da dan wasan tsakiya na Uruguay Lucas Torreira, mai shekara 25, da dan wasan gaba na gefe na Ingila Reiss Nelson, mai shekara 21, da kuma dan bayan Bosnia Sead Kolasinac mai shekara 28, dukkaninsu ka iya barin Arsenal a mako mai zuwa. (Standard)

West Ham na shirin taya dan gaban Montpellier Gaetan Laborde, mai shekara 27, amma kuma kungiyar ta Faransa kila ta bukaci akalla fam miliyan 12 da rabi a kan dan wasan dan Faransa. (Le 10 Sport)

Sai dai kungiyar ta Ingila ta fi sa ran samun dan bayan Faransa Kurt Zouma daga Chelsea bayan ci gaban da suka samu a tattaunawar sayen dan wasan mai shekara 26. (Telegraph)

West Ham na duba yuwuwar dan wasan gaba na gefe na CSKA Moscow da Croatia Nikola Vlasic, mai shekara 23, a madadin Jesse Lingard, na Manchester United, domin kila dan gaban na Ingila mai shekara 28, ya tsaya a Old Trafford. (Telegraph)

Wakilan dan wasan Holland Donny van de Beek sun yi watsi da zawarcin dan wasan na tsakiya na Manchester United mai shekara 24 da ake yi, yayin da yake kokarin ganin ya zama cikin 'yan wasan da ake sa su ko da yaushe a United. (Times )

KIla dan bayan Liverpool da Wales Neco Williams ya ci gaba da zama a Anfield saboda sha'awar da ake nunawa a kan dan wasan mai shekara 20 ta ragu a makonnin nan. (Liverpool Echo)

Kungiyar Lyon ta amince da tayin da Burnley ta yi wad an bayanta dan Ivory Coast Maxwel Cornet na fam miliyan 15. Yanzu ya rage gad an wasan mai shekara 24 idan yana son tafiya. (Sky Sports)

Dan wasan tsakiya na Uruguay Federico Valverde, mai shekara 23, ya amince da sabon kwantiragi da Real Madrid, wanda zai kare a 2027 da kuma fam miliyan 856 na na-gani-ina-so a yarjejeniyar ga duk kungiyar da za ta so shi kafin karewar sabon kwantiragin.(Goal)

Dan bayan Barcelona Sergi Roberto, mai shekara 29, da dan wasan tsakiya Sergio Busquets, mai shekara, wadanda dukkaninsu ke yi wa Sifaniya wasa na dab da amincewa a rage musu albashi a kungiyar ta La Liga. (Marca)