Yadda Afghanistan ta kaɗa hantar Asia sannan ta ƙarfafa gwiwar China

Mataimakiyra shugaban Amurka Kamala Harris

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kamala Harris a lokacin ziyararta a Asiya ta nemi tabbatar wa da kawayen Amurka goyon baya
    • Marubuci, Daga Tessa Wong and Zhaoyin Feng
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilan BBC a Singapore da Washington
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

Kamar sauran mutane a fadin duniya, miliyoyin 'yan nahiyar Asiya sun girgiza daga irin halin matsananciyar damuwar da ke fitowa daga Afghanistan - inda wasu ke nuna tabada da shakku kan ko Amurka abin yarda ce.

A yammacin ranar Litinin - mako daya kacal bayan da Kabul babban birnin kasar Afghanistan ya fada hannun kungiyar Taliban - Mataimakiyar shugaban kasar Amurka Kamala Harris ta sauka a kasar Singapore don fara wani gagarumin rangadin kasashen yankin Asiya.

Tuni ta fara kokarin kwantar da hankali ta hanyar bayyana cewa yankin shi ne ''mafi muhimmanci'' ga Amurka.

Amma kuma, shin wannan ya isa bayar da tabbaci ga wadanda lamarin ya shafa a yankin na Asiya? Kuma shin Amurka za ta iya kare duka yunkurin kasar China kan abin da wasu ke cewa amu babbar damar yaɗa farfagandar adawa da Amurka?

Guna-guni na damuwa

A ranar Litinin ne Firaministan kasar Singapore Lee Hsien Loong ya yi gargadin cewa da dama a yankin na kallon yadda Amurka ta sauya matsayinta a lokacin rugujewar kasar Afghanistan.

Kamar yadda manyan kawayen Amurka a yankin, kasashen Korea ta Kudu da Japan, abubuwan da suka faru ba su shafi amincewar jama'a da Amurka ba - amma akwai gunaguni na nuna damuwa daga wasu bangarorin.

Wasu masu ra'ayin rikau sun yi kira ga rundunonin sojinsu da su daura damara, tare da yin amannar cewa ba za su iya yarda da alkawarin Amurka na mara musu baya a tashin hankalin ba.

Yanzu haka Amurka na da dubban daruruwan dakaru da aka girke a duka kasashen biyu, amma kuma manufar gwamnatin kan kasashen waje ta farko lokacin tsohon shugaban kasar Donald Trump ta sa dangatakar ta dakushe.

A wata hira da y yi da kafr ABC, shugaban Amurka Joe Biden ya jaddada cewa ''akwai banbanci mai yawa'' tsakanin Afghanistan da kuma kasashe kawaye kamar su Korea ta Kudu da Japan da kuma Taiwan tare da cewa '' ba zai yiwu a kwatanta su ba ma''.

Kwace ikon Afghanitan da Taliban ta yi ya razana ƙasashen Asiya da dama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kwace ikon Afghanitan da Taliban ta yi ya razana ƙasashen Asiya da dama

Kwararru sun amince, tare da nuni da cewa kasar Afghanistan ba daya ta ke da sauran kasashen da suka ci gaba kamar na yankin Asiya ba, da suke da wadatar kayyakin ayyukan soji da gwamnatoci masu nagarta.

Saboda harkokin dimokaradiyyar kasashen yankin Asiya suna da nagarta kamar na Amurka, kuma sun zama muhimman abokan hulda a fannin kasuwanci da na soji.

Haka ma wasu masu sa ido sun yi nuni da cewa kasashen irin su Korea ta Kudu da ke kafa tsare-tsaren dabarun aikin soji na Amurka a yankin Asiya, ba zai yiwu a ce Amurkar za ta janye dakarunta nan kusa ba.

'Amurka kafar angulu ce'

Amma a yayin da ake cikin rashin tabbas, kasar China na kara sauya maganganunta.

A makon jiya ne minstan harkokin wajen China Wang Yi ya bayyana cewa janyewar da Amurka ta yi cikin gaggawa daga Afghanistan ya haddasa ''mummunan tasiri''.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Zhao Lijian ya nanata kwatanta shi da faduwar Saigon, a yayin da abokin aikinsa Chunying ya yi wa hakan lakabi da suna Amurka ''mai kafar angulu.''

Ya ƙara da cewa "a duk inda Amurka ta sa kafa…. babu abin da muka gani sai tangal-tangal, da rarrabuwar kawuna, da rarrabuwar iyalai, da mace-mace da yanayin rashin jin dadi da ta bari.''

A sharhin editanta Jaridar Global Times ta yi kira ga Taiwan da ta dakatar da "kokarin hade kansu da Amurka mai adawa da yankin kasar China mai cike da takaddama ", tare da jaddada cewa Amurka ba za ta damu ba wajen haddasa mummunan yaki tsakaninta da China a kan Taiwan.

Babban editanta ne wanda wallafa wannan a shafinsa na Twitter:

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Bayan rushewar mulkin Kabul, mahukuntan kasar Taiwan yanzu haka suna rawar dari. Ba su kuma tunanin Amurka za ta taimake su. Akwai bukatar mahukuntan Taipei cikin ruwan sanyi su aike da jar tuta mai alamun taurari biyar daga tsakiyar yankin China. Wata rana zai musu amfani a lokacin da suka mika wuya ga PLA.

White space

Taiwan, wacce ke sayen makamai daga Amurka, na daukar kanta a matsayin kasa mai cin gashin kanta, amma kuma China na yi mata kallon wani lardin da ya balle ne wanda dole a sake karbe shi ko da kuwa da karfin soji ne.

A cikin kwanaki kadan da suka gabata ne tsibirin ya mayar da martani ta hanyar yawan jaddada kalamanta na kamanta kasar China da Taliban.

Firmiya Su Tseng-chang ya bayyana a makon jiya cewa an ''yaudari'' ''dakarun kasashen waje'' wanda ke son mamaye kasar Taiwan", yayin da ministan harkokin waje Joseph Wu ke cewa:

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Muna godiya da kuma jajirce a kan muradu da kuma bukatun jama'ar #Taiwan.

Sun hada da dimokaradiyya da 'yanci daga mulkin kwaminisanci, da mulkin mallaka da aikata muggan laifuka kan biladama. Burin kasar #China na kwaikwayon kungiyar #Taliban, amma bari in fito karara: Muna da karfin zuciya da kuma halin da za mu iya kare kanmu.

White space

Biden bai taimaka wa halin da aka shiga ba, wanda a hirarsa da kafar yada labarai ta ABC ya hada Taiwan da Korea ta Kudu, da Japan, wadanda Amurka ke da yarjejeniya a hukumance ta kariya muddin yaki ya barke.

Ba kamar sauran ba, Taiwan ba ta da yarjejeniyar kan tsaro da Amurka, sai dai kawai tabbaci kan samar da tsaron.

Daga bisani mahukuntan Amurka sun ce manufofinsu na ''tsarin dabarun yaki'' game da kasar Taiwan ba su sauya ba, amma kuma hakan ya kawai bai wa kafar yada labaran karin wata dama.

Rushewar Afghanistan, ta wani gefen ya kasance wata babbar dama ga kasar China ta ja hankalin mutanen kasashen yankin Asiya cewa Amurka ba wacce za a yarda da ita ba ce, in ji masana.

"Duka maganar da ake yi game da wannan farfaganda shi ne, don jama'a su kara yin matsin lamba ga gwamnatocin da suke da dangantaka mai karfi da Amurka, kuma su sanyaya wannan dangantaka,'' in ji Ian Chong, wani farfesan kimiyyar siyasa a Jami'ar Kasa ta Singapore.

Bin hanya madaidaiciya

Amma kuma, har ila yau Afghanistan ba ta kasance wata garabasa ga kasar China ba.

Bonnie Glaser, wata kwararriya a yankin na Asiya da ke tare da wata gidauniyar Jamus ta German Marshall Fund, ta yi amanna cewa Beijing na kallon sauye-sauyen baya-bayan nan a Afghanistan a matsayin mafiya hadari fiye da zama mai amfani.

"'Yan kasar China sun damu matuka game da yiwuwar rashin kwanciyar hankali da kuma ci gaba da kasancewar Afghanistan wata matattarar 'yan ta'adda,'' in ji ta.

A wani maaki, a watan da ya gabata ne kasar China ta gayyaci Taliban don tattaunawa, inda ta yi tayin ba su tallafin tattalin arziki ga kasar Afghanistan amma ta kuma yi nuni da cewa kada kasar ta kasance wacce za a yi amfani da ita a matsayin wata matattarar 'yan ta'adda.

wang yi with mullah baradar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ministan harkokin wajen China Wang Yi (daga dama) ya tsaya daukar hoto shi da shugaban kungiyar Taliban Mullah Baradar (daga hagu)

Amma kuma a harkokin cikin gida, ta yi ta kokari game da wannan mataki na kawance wajen jan hankulan 'yan kasar ta China da ke yin dari-dari da Taliban.

Lokacin da Taliban ta sake karbe iko a makon jiya, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China Hua Chunying ta ce China na mutunta ''zabin mutanen Afghanistan".

Cikin sauri wadannan kalamai suka haifar da zafafan martani da zarge-zarge kan kasar ta China a shafukan sada zumunta.

A daidai lokacin da aka kara zafafa wayar da kan jama'a game da 'yancin mata a kasar China, kafafen sada zumunta da dama na sukar lamirin Taliban kan yadda suke yi wa matan Afghanistan.

Akwai kuma batun cewa yanzu dole Beijing ta shawo kan matsalolin kungiyar masu tsattauran ra'ayin addinin Islama da ta runguma, a daidai lokacin da China ke ci gaba da mummunan gallazawa Musulman kasarta 'yan tsirarai da sunan shawo kan matsalar ayyukan ta'addanci.

Yayin da ta ke gallaza wa Musulman Uighur, "gwamnatin China na ta yi wa mutane huduba kan su kiyayi kungiyoyin addini. Don haka wannan hadin kai da kungiyar Taliban ka iya zama babbar matsala saboda ya saba wa manufofin gwamnatin," in ji Dakta Chong.

Duniya ta sa ido kan Amurka

Wasu masu sa ido kamar Mis Glaser, sun yi amanna cewa janyewa daga Afghanistan ba ta zama ''gazawa ce a shugabancin Amurka ba'', kuma za a sake bai wa kawayen Amurka tabbaci cewa yanzu Washington za ta mayar da hankali sosai kan yankin da kuma gogayya da kasar China.

A jawabinta ranar Talata a kasar Singapore, Mis Harris ta bayyana burin Amurka na kasancewa amintacciya ga kasashen yankin na Asiya.

Ta ce '' ko shakka babu muna matukar kaunar yankin da kuma kokarin cika duk wasu alkawura…. wadannan alkawura kuma sun hada da na tsaro'', tare da yin alwashin cewa Amurka za ta dauki "lokacinmu da karfinmu'' wajen karfafa dangantakar.

Kamala Harris

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mis Harris a kasar Singapore ranar Talata tana karbar dashen tarin furannin da aka yi wa lakabi da sunanta

James Crabtree, babban daraktan hukumar sa ido ta -SS Asia, ya yi nuni da cewa ziyarar Misa Harris daya daga cikin ziyarce-ziyarcen kasashen yankin ne da manyan jami'an gwamnatin Amurka ke kai wa.

"Amurkawa sun amsa tambayoyi game da sukar lamari da dama irin sa na farko wadanda su ne '' Kun manta da mu' - yanzu kuma suna zuwa gare mu,'' in ji shi.

"Yanzu daya tambayar ita ce, da duka wadannan maganganu na hadin hadin guiwa, me hakan zai haifar?"

Wasu sun yi amanna Amurka za ta bukaci karin yin wasu alkawura. Dakta Chong ya ce hakan na nufin samun taimako daga Amurka, sa hannu a kan dokar harkokin sufurin jiragen ruwa na Majalisar Dinkin Duniya, da sake shiga yarjejeniyar hadakar kasuwancin kasashen yankin Pacific wacce Amurka ta janye a karkashin shugabancin Donald Trump.

A cewar Mr Crabtree: "Mutane za su sa ido sosai kan abin da Amurka za ta yi a yankin Asiya daga yanzu, saboda Afghanistan ta zaburar da su wajen duba alamun cewa ba su da tabbas,

Duk da cewa Amurka za ta san cewa mutane na a shakku game da yanayin takunta, don haka za ta yi kokarin ganin ta nuna cewa ba haka batun yake ba.''