Tokyo Paralympics: Shekaru 60 da soma gasar da ta sauya rayuwar masu larurar nakasa

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Peter Ball & Pooja Chhabria
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
A bikin bude wasannin motsa jiki na masu nakasa na shekarar 2020 a birnin Tokyo da za a soma ranar Talata, za kuma a yi bikin tunawa da cika shekara 60.
Amma a zahiri shekarar 61 saboda annobar korona tun bayan da aka kirkiro wasannin da ke samun halartar manyan 'yan wasan motsa jiki tare da taimakawa wajen kawo sauyi ga rayuwar masu larurar nakasa.
Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da wasannin, BBC ta tattauna da masu shiga wasannin daga fadin duniya wadanda suka wakilci kasashensu a manyan matakai cikin shekaru 60.
Sauyin rayuwa

Asalin hoton, Getty Images
"Zan iya cewa [nakasassu 'yan wasan motsa jiki] sun bayar da gagarumar gudunmawa, sun hada kan mutane daga sassan daban-daban na duniya, wanda ba su iya yi a baya ba," in ji Baroness Masham ta Ilton, wacce ta taba wakiltar Birtaniya a wasannin motsa jiki ta masu nakasa na farko da aka gudanar a birnin Rome a shekarar 1960.
Ta kara da cewa: "Zan iya cewa sun kawo gagarumin sauyi."
Bayan gamuwa da hadari lokacin sukuwar dawaki a shekarar 1958 wanda ya sa dole ta bukaci yin amfani da keken guragu, mutumin da ya taimaka wajen kirkirar wasannin masu nakasar Dakta Ludwaing Guttmann ne ya yi mata magani.
"Da zarar mutum ya koma zama a cikin keken guragu, wasanni su ne hanyoyin farfadowa da kuma dawowa cikin hayyaci," in ji ta. "Bangare ne na rayuwa. Bangare ne na tsarin komai na rayuwarsa."
Dakta Guttmann ya fara shirya gasar wasannin Stoke Mandeville Games a Birtaniya (sunan asibitin da yake yi wa wadanda suka samu rauni a kashin gadon baya aiki) wanda daga baya ya juye ya zama gasar wasan masu nakasa.
Baroness Masham, wacce mai kaunar wasannin motsa jiki ce kafin ta gamu da hadarin, na ganin samun damar da ta yi na shiga gasar ta farko wata muhimmiyar dama ce.
"Shiga gasar ta yi mini dadi kwarai, kasancewa gasar kasa da kasa ya sa ta kara armashi," a cewarta. "Kuma na kaunaci haduwa da mutane daga kasashe daban-daban."
Batan lambar yabo
Lokutan da ta shiga gasar wasan masu nakasa a birnin Rome, kuma bayan wasaannin da aka yi a birnin Tokyo da Tel Aviv, ta samu nasara sosai - ta samu lambobin yabo uku a fannin gasar wasannin ninkaya, da kwallon tebur, duk da cewa ba duka ne "na iya tafiya da su gida ba."
"Mun shiga wani gidan cin abinci na Trevi Fountain a birnin Rome," in ji ta
"Wani ya tambaye ni yana son ya ga lambar yabona, sai muka nuna musu nawa lambobin yabon, daga nan sai na mayar da su gefen keken guraguna, amma lambar zinari na ta sullube ta fadi."
Kafafen yada labaran yankin da suka samu labari, sai suka fara yadawa, amma kuma bangare (marar sahihanci) na aninihin abin da ya faru cewa da gangan ta jefar da ita cikin wani sanannen ruwa mai toroko.
Ta kara cewa "Abin da ban aikata ba, amma ba a sake ba ni wata wacce za ta maye gurbinta ba." "Wannan abin bakin ciki ne."
Daga tuta

Asalin hoton, Getty Images
Har wa yau shiga gasar wasan nakasassu ta yi wa rayuwar Anne Wafuka Strike gagarumin tasiri.
"A nawa bangaren samun shiga gasar wasan ya bani wata sabuwar rayuwa."
Ta bukaci amfani da keken guragu tun bayan da ta kamu da cutar shan-inna ko kuma Polio a lokacin tana da shekara 30.
"Wasannin motsa jiki sun sake dawo da ni cikin hayyacina - zan iya wasan tsere, da motsa jiki, yin horo tare da sauran mutane masu lafiyar gabobi. Na rika jin ina daidai da su kana n afara ji da kai na."
Anne ta wakilci kasar Kenya a gasar wasan na shekarar 2004 a birnin Athens.
"Abin kamar a mafarki, tsananin farin cikin da ya biyo baya, gamsuwar da na ji ba karama ba ce."
Abin mamaki, duk da irin sunan da yankin ya yi wajen lashe gasar wasan motsa jikin, ita ce 'yar gasar wasan tseren keken guraju ta farko daga yankin gabashin Afirka da ta shiga gasar ta nakasassu.
"Daga zama saniyar ware a cikin al'umma zuwa tsayawa a kan wancan dandamali kana ina daga tuta - wannan karfin wasanni kenan."
Anne ta kuma shigar wa Birtaniya gasar wasan, inda ta koma ta kuma cigaba da wasannin bayan da ta yi aure.
Amma kuma a can din ma ta gamu da bacin rai kan yanayin kawo sauyi game da rayuwar masu fama da nakasa - an biya ta diyya kan wani babban abu da ya faru ga kamfanin zirga-zairagr jiragen kas ana Birtaniya kan rashin samar da ban-dakunan nakasassu a cikin jiragen.
"Nakan ji bacin rai a lokacin da kasar da ta ci gaba ta gaza jagorantar duniya yadda ya kamata.''
Bayan da ta daina wasan tseren, ta yi aiki a matsayin darakta a hukumar kula da wasan motsa jiki ta Birtaniya kana a matsayin mai shigewa gaba wajen neman daidaito a gasar wasannin kasashe rainon Ingila.
"Ni ce bakar fata ta farko da ta fara aiki a hukumar kula da wasannin ta kasa (a Birtaniya) kuma lallai hakan ya nuna yadda al'umma ta kasance da kuma yadda za mu yi wajen farfadowa.''
Daga yaki zuwa wasanni

Asalin hoton, Getty Images
Murlikant Petkar dan wasan motsa jiki na masu nakasa na farko ne daga wata kasa daban - India.
"Kasancewata wanda ya samu lambar zinari ta farko a gasar wasan masu nakasa ya zama lokaci mafi kyau da b azan taba mantawa da shi ba a rayuwata,'' ya ce.
Murlikant ya samu munanan raunuka ne daga hari ta sama lokacin yakin Indiya da Pakistan a shekarar 1965, kuma wasan ninkaya ya kawo gagarumin sauyi wajen samun warakarsa.
"Kasancewa mai nakasa da farko ya zama wani bangare na matukar damuwa da bakin ciki na rayuwata, wanda na zabi in mance da shi da zarar na fahimci matsayina na dan wasan motsa jiki ga kasata da ni kai na.
"Da a ce ban kasance a cikin gasar wasan masu nakasa ba, da yanzu na durmuya cikin bakin cikin gaza tabuka komai.''
Ga wannan cigaba, wacce har ila yau ta hada da shiga gasar wasan a shekarar 1968, Murlikant ya samu kyutar yabo ta Padma Shri daga kasar India - daya daga cikin manyan kyaututtuka na kasar.
Yana da yakinin karin wasu 'yan wasan motsa jiki na kasar India za sus amu nasara a Tokyo.
"Na yi amanna cewa 'yan gasar wasan nakasassunmu na yanzu da masu tasowa za sus amu nasarori tare da samun karin kyaututtukan lambobin zinari ga kasar India tare kara mana lokuta yin alfahari a garemu duka.''
Kokarin kawo sauyi
Duka 'yan gasar wasan nakasassun na jiran su ga lokacin wasannin na Tokyo, wanda a baya aka daga saboda annobar korona.
"Na ji dadi cewa za a gudanar, saboda duka horarwar da ak yi - ina cike da fata komai zai tafi daidai,'' in ji Baroness Masham.
Anne ita ma hankalinta ya kwanta cewa duk da rashin tabbas din, daga karshe ga shi za a gudanar da gasar nakasassun a ranar Talata.
"Ina farin cikin cewa za a gudanar da wasan. Za ka iya tunanin yadda 'yan wasan motsa jikin suka shafe shekaru ana horar da su?
"Tunani game da tara iyali, da sauya sana'oi - da duka wadannan sun sauya saboda annobar.''
Amma tana ganin 'yan wasan motsa jikin za su kara daura damarar wajen fuskantar kalubalen.
''A lokacin da aka gwada kowa, abu mai ban sha'awa ga masu nakasa shi ne suna da jajircewa, kuma muna yin hakan ne saboda akwai kalubale da dama a gabanmu.
"A kullum ka tashi, akwai sabon kalubalen da dole sai ka yi ta kokarin kaucewa tare da kokarin shawo kai.
Kuma kan hakan ne Anne ta yi amanna zai iya kawo sauyi.
"Wasanni kawai ba za su iya kawo hadin kai ba - wasanni na karfafa gwuiwa, da karfafa buri. Ina fatan za su yi amfani da wadannan taurarin wasanni bayan sun koma gida, za su yi amfani da wadannan taurari a matsayin wata babbar hanya ta kawo sauyi.''











