Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku Tare da Malam Sadiqu Siddiq
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Fitaccen alaramma a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, Shiekh Sadiqu Siddiq, ya ce bai taɓa samun farin cikin da ya kai nasarar da ya samu ta lashe musabaƙar Al Qur'ani mai girma ta duniya da aka gudanar a Saudiyya, inda ya ce nasarar da ya samu ta kasance tushen arzikinsa.
Alaramman ya bayyana hakan ne a hirarsa da BBC Hausa a shirinmu na musamman na Ku San Malamanku, kuma ya ce tun yana ɗan shekara 9 ya sauke Al Qur'ani.
"Mun fafata da Larabawa da ƴan Afrika da Turawa da Indiyawa kuma aka sanar cewa na yi na daya a matakin hizb 60 a duniya baki ɗaya."
"Farin cikin ya ƙara yawa, ga sabuwar jihar Zamfara, ga shi na yi na ɗaya a Najeriya kuma na daya a duniya," in ji shi.
Tarihin Sadiq siddiq
Malamin ya shaida wa BBC cewa shi ɗan asalin jihar Kebbi ne, kuma an haife shi ne a shekarar 1979 a ƙauyen Tafki Tara cikin ƙaramar hukumnar Shanga da ke jihar Kebbi.
Ya ce ya fara karatun addini ne a gun mahaifinsa wanda shi ne babban malami a kauyensu na Tafki Tara. "Na tashi gidan ilimi, na yi karatun Al'Qur'an a hannun mahaifina har na sauke ina ɗan shekara tara."
Malamin ya ce ya ci gaba da karatunsa na Al Qur'ani a gidan mahaifiyarsa garin Koko, inda kakansa shi ne babban malamin garin, kuma tun yana ɗarami ya yi karatun litattafai na Fiqhu.
Amma malamin ya ce daga baya hankalinsa ya karkata ne ga haddar Al Qur'ani, wanda wannan dalilin ne ya sa mahaifinsa ya turo shi yin karatu a garin Gusau wajen Malam Sanusi Balarabe.
Ya ce ya rubuta Al Qur'ani kwafi biyu, kuma ya yi wa mahaifinsa kyautar kwafi ɗaya.
Dalilin shiga musabaƙar Al Qur'an
Malam Sadiq Sadiq ya ce malaminsa Shiekh Balarabe ne ya ja hankalinsa shiga masabaƙar Al Qur'ani mai tsarki.
Ya ce kaset kaset na musabaƙar da malaminsa yake kunna wa suka fara tsuma shi, ya ja hankalinsa.
"Ba ni mantawa, karatun Maryam Nura Sharif wata ɗalibar Kano da ta yi musabaƙa a Katsina, yadda na ji mace tana karatu irin na Larabawa kuma da tajwidi, sai abin ya tsuma ni,"
"Na ce wai ni ma ya za a yi na shiga wannan musabakar ne," in ji shi.
Ya ƙara da cewa wannan ne ya sa ya dage wajen koyon tajwid. Malamin ya ce kwatsam wata rana sai aka kawo takardar gayyata ga zawiyar Shiekh Balarabe ta neman shiga musabaƙa.
Ya ce wannan ya sa aka nemi su, ɗaliban da suka yi haddar Al'Qur'ani, kuma suka shiga musabaƙar a matakin farko na karamar hukumar Gusau a 1994.
Daga nan ya ci gaba zuwa musabaƙar ƙasa da aka yi a Minna jihar Neja 1994. Kuma ya sake shiga a Kaduna inda ya zo na biyar a mataki na ƙasa.
A musabaƙar shekarar 1996 da aka yi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ya zo na ɗaya a matakin ƙasa. Wannan ne ya ba shi damar wakiltar Najeriya a musabaƙar duniya da aka yi a Makkah a ƙasar Saudiyya a 1997.
"Mun fafata da Larabawa, da ƴan Afirka kuma Allah ya sa na zo na ɗaya a matakin hizb 60 a duniya baki ɗaya."
Ya ce yana shekara 19 ya lashe musabaƙa ta duniya a Saudiyya. Kuma a cewarsa wannan ne karon farko da ya taba yin karatu gaban manyan shehunan malaman Saudiyya.
Iyali
Malamin Sadiq Siddiq ya ce yana da mata huɗu da ƴaƴa 14.
Ya ce babban ɗansa Abdullahi Sadiq ɗan shekara 18 ya haddace Al Qur'ani, tare da laƙantar ƙira'o'i 10 da ruwaya 20.
Abincin da Malam ya fi so
Malamin Sadiq Siddiq ya ce ya fi ƙaunar shinkafa da wake da miya da salat da kuma namma amma ya kasance da zafi.
Babban burin Malam Sadiq Siddiq
Ya ce babban burinsa shi ne kafa babbar makarantar mahaddata Al'Qura'ni mai girma ta yara kanana.
"Ina son ganin yara ƴan shekara bakwai zuwa 10 sun haddace Al Qur'ani mai tsarki da tajwidinsa, karatu mai inganci shi ne burin da na sa a gaba," in ji malamin.