Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Kane, Ronaldo, Mbappe, Coutinho, Locatelli da Rudiger
Manchester City ta shirya sayen ɗan wasan gaban Ingila Harry Kane daga Tottenham a kan fam miliyan 127, a cewar jaridar (Guardian).
Kane mai shekaru 28 na fatan sanin makomarsa a Tottenham daga nan zuwa mako mai zuwa, bayan sun buga wasansu na farko a gasar Premier League din ta bana da Manchester City da ke son sayensa. (Telegraph, subscription required)
Ita kuwa jaridar (AS - in Spanish ta ce Paris St-German na duba yiwuwar sayan ɗan wasan gaban Portugal Cristiano Ronaldo daga Juventus, a kasuwar cinikin yan wasa ta 2022.
PSG na fatan Ronaldo, mai shekaru 36, ya maye gurbin Kylian Mbappe da Real Madrid ke nema.
Ana rade-radin tsohon ɗan wasan Liverpool Philippe Coutinho da yanzu ke wasa a Barcelona zai dawo tsohuwar ƙungiyar tasa. (Liverpool Echo)
Haka kuma Liverpool na da sha'awar ɗauko Jeremy Doku daga Rennes na Faransa, da ake sa ran su nemi wajen fam miliyan 38 ga ɗan wasan mai shekaru 19, in ji (Voetbal24 - in Dutch).
Jaridar Sky Sport ta ruwaito cewa Real Madrid da PSG na duba yiwuwar ɗauko Antonio Rudiger na Chelsea da kwantiraginsa ke dab da ƙarewa a Chelsea.
Manchester United ta shirya ba da matashin ɗan wasanta Amad Diallo mai shekaru 19 a matsayin aro.
A Italiya kuwa Juventus na dab da kammala kulla yarjejeniyar ɗauko ɗan wasan tsakiyar Sassuolo wato Manuel Locatelli da Arsenal taso saye.
Sai dai mai horar da Arsenal Mikel Arteta ya ce yana da kwarin gwuiwa za su sayi ƙarin yan wasa kafin a rufe kasuwa.
Ɗan wasan gaban Sfaniya Diego Costa mai shekaru 32 ya shirya komawa Atletico Mineiro da ke Brazil.
Akwai yiwuwar golan Barcelona Neto zai je Arsenal a matsayin aro ko kuma zama din-din-din.