An saki shugabar Yahudawan Najeriya da hukumar DSS ta kama

    • Marubuci, Daga Raffi Berg
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Online Middle East editor
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

An saki shugabar al'ummar Yahudawan Najeriya, wadda aka daure tsawon wata daya ba tare da an tuhume ta ba tare da wasu 'yan Isra'ila uku da suka kai mata ziyara.

Hukumomi sun yi zargin cewa 'yan Isra'ilan guda uku suna da alaka da kungiyar IPOB da ke fafatukar ballewa daga Najeriya wadda ta yi maraba da zuwansu kasar.

An saki Lizben Agha, wadda 'yar kabilar Igbo ce, bayan an yi ta kiraye-kirayen yin haka ciki har da kiran da wata kasa ta yi wa mahukuntan Najeriya.

'Yan kabilar Igbo da ke bin addinin Yahudanci ba su da yawa a kasar.

Mrs Agha tana taimaka wa 'yan Isra'ilan uku, wadanda suka je garinta Ogidi domin daukar wani fim.

A cewar danta Emmanuel, an kama Mrs Agha da mahaifinta Peniel ta hanyar amfani da karfin bindiga lkacin da aka je gidansu da tsakar daren ranar 9 ga watan Yuli. Ya ce an tafi da su wani otal inda mutanen uku, wadanda wasunsu suke da fasfo na kasar Isra'ila da Amurka, yayin da sauran suke da na kasar Isra'ila da Faransa, suke zama kuma daga nan ne aka tafi da su inda aka tsare su.

Emmanuel ya ce an saki mahaifiyarsa da kakansa amma daga bisani aka sake kama ta bayan ta roki a bar ta ta tafi da bakinta domin ta zama mai shiga tsakani.

Daga nan ne aka tafi da Mrs Agha zuwa hedikwatar hukumar tsaro ta farin kaya, wato Department of State Services (DSS) da ke Abuja, inda aka tsare dukkan su hudu.

Mutanen sun ce jami'an hukumar DSS sun zarge su da kasancewa 'yan leken asirin kungiyar Ipob.

Shugabanta Nnamdi Kanu ya yi ikirarin cewa kabilar Igbo ta samo asali ne daga Yahudawa kuma ya bayyana kansa a matsayin mabiyin addinin Yahudu, ko da yake galibin 'yan kabilar Igbo na kallon wannan ikirarin a matsayin karya.

Yanzu haka dai gwamnatin Najeriya tana tuhumar Mr Kanu bisa zargin ta'addanci da cin amanar kasa. Hukumomi sun ce Ipob ce ke da alhakin kai hare-hare a ofisoshin 'yan sanda da sauran jami'an tsaro a yankin kudu maso gabashin kasar. Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sha alwashin murkushe kungiyar.

Gabanin kama mutanen, kafar watsa labaran da ke goyon bayan Ipob ta wallafa hotunan mutanen uku a shafukan sada zumunta yayin da suke ganawa da Yahudawa 'yan kabilar Igbo. Hotunan sun nuna su a dauke da wata alama ta Yahudanci wato Sefer Torah wadda suka kai wa mazauna yankin a matsayin kyauta . Kafar watsa labaran ta Ipob ta ce hakan wata alama ce da ke nuna cewa Isra'ila tana goyon bayan 'yan a-waren na Biafra.

"Mun duba wayoyinmu inda muka ga ana ta watsa wannan labari," a cewar Rudy Rochman, daya daga cikinsu, "cewa mu ma muna cikin Mossad [hukumar leken asirin Isra'ila]' da aka aika domin 'kubutar da Biafra', amma ba mu da alaka da wannan kungiya, mun zo nan ne domin mu dauki fim game da Yahudawa 'yan kabilar Igbo."

An kulle mutanen uku tsawon kwana 18 sanna aka sake su kuma aka fitar da su daga kasar.

Mr Rochman ya ce lokacin da suke tsare an kulle su a wurare daban da na Lizben Agha kuma sau daya kawai ya gan ta lokacin da aka dauke ta domin zuwa ta gana da likita.

Mrs Agha tana daya daga cikin fitattun Yahudawa 'yan kabilar Igbo kuma ta yi alkawarin taimaka wa mutanen uku domin daukar fim kan Yahudawa 'yan kabilar Igbo.

An bayar da belinta ranar Asabar bayan wasu mutane daga ciki da wajen kasar sun sanya baki - ciki har da wani babban jami'in gwamnatin wata kasar Afirka.

Sai dai an kwace fasfo dinta.

BBC ta tuntubi hukumomin Najeriya domin yin tsokaci kan batun amma ba su ce komai ba.