Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afghanistan: Gawarwaki kwance a tituna yayin da wasu mazauna suka maƙale a Lashkar Gah
"Ƙungiyar Taliban ba ta jin tausayinmu kuma gwamnati ta ƙi daina sa abin fashewa."
Mazaunin birnin Lashkar Gah a kudancin Afghanistan na ɗaya daga cikin dubban mutane da suka maƙale ko suke tserewa yayin da rikici ke ci gaba tsakanin 'ƴan bindiga da dakarun gwamnati.
BBC ba za ta ambato sunan wasu mutanne da aka tattauna da su a wannan maƙala ba saboda dalili na tsaro.
"Akwai gawarwaki kwance a kan titi. Ba mu sani ba ko fararen hula ne ko 'ƴan Taliban," wani mutum ya shaida wa sashen Afghan na BBC ta manhajar Whatsapp.
"Gwamman iyalai ne suka tsere daga muhallansu inda suka koma kusa da rafin Helmand."
Wasu mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa sun ga gawarwaki yashe a kan titi.
Ƙwace iko da Helmand, babban birnin yankin zai zama babban abu ga masu ta da ƙayar bayan yayin da suke ci gaba da kutsawa bayan ficewar dakarun kasashen waje.
Helmand ta kasance cibiyar yaƙin sojojin Amurka da na Burtaniya.
Majalisar Dinkin Duniya da sauran hukumomi na gargaɗin cewa wannan na iya haifar da mummunar matsalar agaji.
A ƙalla fararen hula 40 ne aka kashe a Lashkar Gah cikin kwana guda, a cewar Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata.
Rundunar sojin Afghanistan ta buƙaci fararen hula su bar Lashkar Gah gabanin wani babban hari da za ta kai wa Taliban, ƙungiyar masu iƙirarin jihadi wadda sojojin da Amurka ta jagoranta ta hamɓare daga mulki shekara 20 a baya.
Can a kudanci, Taliban na koƙarin ƙwace Kandahar, birnin da suka taɓa mamayewa, kuma rikici ya karu a Herat na yammaci.
An ci gaba da gwabza faɗa a Lashkar Gah tsawon kwanaki, inda rahotanni ke nuna cewa 'ƴan bindigar na iko da mafi yawan unguwanni.
"Muna cikin mawuyacin hali," wani dalibi a birnin ya shaida wa BBC. "Ƙungiyar Taliban na kai mana hari ta ƙasa yayin da gwamnati ke kai mana hari ta sama."
Wani mutum a ranar Lahadi ya bayyana cewa: "Ana ganin 'ƴan Taliban a titunan birnin. Kasancewar 'ƴan Taliban ya bai wa mutane mamaki ƙwarai.
"An rufe kantuna, kuma an bar motocin sojojin gwamnati da aka lalata a tsakiyar tituna. Ana ci gaba da yaƙi a kusa da ofishin gwamna da Hukumar da ke sa ido kan harkokin tsaro.
"Gwamnatin tarayya ta ce kwanan nan ta aika da sabbin kwamandoji Lashkar Gah amma ba mu gan su ba."
Ɗaruruwan sojojin Afghanistan ne aka ruwaito cewa an aika da su birnin.
A ƙarshen makon da ya gabata ne, Attaullah Afghan, shugaban hukumar lardin Helman ya bayyana cewa rikicin na nema ya fi ƙarfinsu.
Ƙungiyar Taliban ta kara matsa kaimi a wannan makon, duk da hari ta sama da sojojin Afghanistan da na Amurka ke kai musu.
Akwai rahotannin da ke cewa mayaƙan Taliban sun kutsa gidaje da shaguna da kasuwanni - mutane sun maƙale a gidajensu yayin da ake ci gaba da rikici a waje.
Mayaƙan na yi wa mutane gargaɗi ta lasifiƙa cewa su fita amma kuma wani lokaci suna shiga gidajensu - mazaunan ba su da isasshen lokacin tserewa, idan ba haka ba, su samu kansu a tsakanin musayar wutar yayin da gidajensu ke kasancewa fagen yaki.
"Ƴan Taliban na ce mana idan ba mu bar gida ba cikin rabin sa'a, za su haɗa mu cikin 'ƴan sanda da sojojin Afghanistan," a cewar ɗalibin da BBC ta tattauna da shi.
Lokacin da suke da iko a ƙarshen shekarun 1990, 'ƴan Taliban sun riƙa kashe mutane a bainar jama'a kuma sun hana mata damar neman ilimi da aikin yi.
Ƙungiyar ta ce ta sauya, kuma ba za ta ci gaba da irin waɗancan munanan ayyuka ba - amma 'ƴan Afghanistan da dama na tantama.
Ƙungiyar Human Rights Watch ta tattara bayanai kan hare-haren ramuwar gayya da mayaƙan suka kai wa fararen hula waɗanda ake tunanin suna goyon bayan gwamnati.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce fararen hula ne rikicin ya fi shafa kuma tana kira ga duka ɓangarorin su ƙara ƙoƙarin kare fararen hular ko kuwa a ga mummunan sakamako.
Dubban mutanen da suka tsere wa yakin a halin yanzu na fuskantar rashin abinci da ruwan sha da magunguna.
Kungiyoyin agaji ba sa iya kai wa ga mutanen da rikicin ya ɗaiɗaita, kuma cibiyoyin lafiya da asibitoci ba su da damar kula da duka mutanen.
Wasu cibiyoyin kula da lafiya an lalata su yayin da wasu ba sa aiki.
Wani likita a Lashkar Gah, Masood Khan ya ce mutanen da suka samu raunuka na ci gaba da tururuwa a asibitinsa kuma yana fargabar cewa wasu ma ba su iya ƙarasawa ba. Ya ce magunguna da kayan aikinsa sun fara karewa.
"Muna samun mutanen da suka ji rauni a yaƙin... Ana ta yaƙi a ko ina," cewar Dokta Khan, wani ƙwararre a ɓangaren bayar da kulawa ga mutanen da ke cikin mawuyacin hali a wani asibiti na ƙungiyar agaji ta Medicines Sans Frontiers, ranar Litinin.
Ana yada hotunan bidiyo na ta'asar da Taliban ke yi a shafukan sada zumunta, kuma hakan na ƙara fargabar dawowar su.
Amurka da Burtaniya sun ce akwai yiwuwar ƙungiyar ta aikata laifukan yaki, inda suka zarge ta da kashe gwamman fararen hula a wani harin ramuwar gayya a Spin Boldak da ke kan iyakar ƙasar da Pakistan.
Haka kuma akwai rahoton cewa a ƙalla 'ƴan Shi'a 40 ne aka kashe a Malistan da ke gabashin lardin Ghazni.
Ƙungiyar Taliban ta yi watsi da zarge-zargen, kuma tana ci gaba da wallafa munanan hotunan fararen hular da yakin ya shafa a hare-haren sama na Afghanistan da Amurka.
Wadanda suka maƙale a yakin da ke ƙaruwa ba su da zaɓi.
"Ba mu da burodi da ruwa a gida, kuma an katse wutar lantarki gaba ɗaya," wani ɗan kasuwa a Lashkar Gah ya shaida wa BBC.
"Ban san inda zan je ba, akwai rikici a kowanne ɓangare na birnin."
Wani tafinta ɗan Afghanistan da ke zaune a garin ya ce rayuwarsa na cikin barazana daga Taliban saboda ya yi aiki da dakarun Burtaniya.
"Na sauya sau uku kenan. Gidana 'ƴan Taliban sun ƙwace shi kuma a nan suke zaune yanzu kuma suna ta nema na," in ji shi.
"Ba mu san abin da zai faru nan gaba ba amma suna bi gida gida suna neman mutanen da suka yi aiki da dakarun Nato."