Mahdi Aliyu Gusau: Wasu 'yan majalisar Zamfara na so a tsige mataimakin gwamnan jihar

An wallafa

Wasu 'yan majalisar dokokin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun sha alwashin tsige mataimakin gwamnan jihar Mahdi Aliyu Gusau bisa zargin saba doka.

Hakan na zuwa ne bayan da mataimakin gwamnan ya ki bayyana a gaban majalisar kamar yadda ta buƙaci ya yi don amsa tambayoyi.

Mataimakin gwamnan ya kafa hujjar cewa tuni kotu ta umurce su da su dakatar da gayyatar da suke masa.

Honorabul Yusuf Alhasan Muhammad Kanoma, mai wakiltar Maru ta arewa a majalisar, ya shaida wa BBC cewa Mahadi Aliyu Gusau ya saɓa ƙa'ida shi ya sa suka ga ya dace su tsige shi.

"Da farko ya shirya taron siyasa duk da kwamishinan ƴan sanda ya ce mishi kada ya yi, saboda a jajiberin taron an kashe kusan mutum 54 a Faru da Gora, amma bai saurari wannan shawara ba ya gudanar da taron.

"Bayan nan ne muka ga ya dace mu gayyato shi ya amsa tambayoyi, kuma abin damuwa baya ga wannan ma ya tara mutane yana zage-zage. Abin kunya ne a ce mataimakin gwamna na jiha ya zo ya yi wannan," a cewar Honorabul Yusuf Kanoma.

Ya ce kamata ya yi a ce mataimakin gwamnan na alhinin kashe mutanen da aka yi.

Ɗan majalisar ya ce takardar da kotu ta aike ta dakatar da su daga gayyatar mataimakin gwamna ta daina aiki ranar 28 ga wata amma sun sake gayyatarsa ran 29, ya ce kuma Mahadi Aliyu Gusau ya sa hannu kan wata takarda da ya aike wa majalisar ta amsa gayyatarsu.

Ya ce a halin yanzu kwamitin harkokin shari'a na majalisar na nazari kan takardar kuma za su gabatar da rahotonsu ga majalisa inda daga nan ne za a ɗauki mataki na gaba.

Sai dai Honorabul Yusuf Alhassan Kanoma ya ce idan mataimakin gwamnan zai bayyana a gaban majalisar suna iya yafe masa laifin da suke ganin ya yi.

Mene ne asalin taƙaddamar?

A ƙarshen watan Yuni ne gwamnan jihar Zamfara Mohammed Bello Matawalle ya sauya sheƙa daga babbar jam'iyyar hamayya ta PDP zuwa ta APC mai mulkin ƙasar.

Sai dai mataimakin nasa, Barrister Mahdi Aliyu Gusau bai sauya sheƙa tare da ubangidansa ba ya ci gaba da zama a jam'iyyar PDP.

A lokacin, mataimakin gwamnan ya nuna cewa babu wata hamayya da za ta taso a tsakaninsu duk da cewa a yanzu ba sa jam'iyya guda.

Asali ma, mataimakin gwamnan ya bayyana cewa dama al'ummar jihar zamfara ce ta zaɓe su don su yi masu aiki kuma yana fata hakan za su ci gaba da yi.

Haka kuma, mataimakin gwamnan ya shaida wa BBC a wata hira ta musamman cewa ba shi da niyyar sauya sheƙa zuwa APC, kuma ba ya fargabar tsigewa daga majalisa.

Sai dai a farkon wannan watan na Yuli ne taƙaddama ta kunno kai bayan da majalisar dokokin jihar ta ce mataimakin gwamnan ya shirya wani taron siyasa ba tare da izinin jami'an tsaro ba.

Daga nan ne kuma ta gayyace shi ya bayyana a gabanta don amsa tambayoyi amma bai amsa gayyatar ba, sai dai ya aike wa majalisar takardar kotu wadda ta hana'yan majalisar gayyatar shi.

Amma majalisar ta sake aike masa da wata takardar gayyatar ranar 29 ga wannan watan.