Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Amurka za ta janye sojojinta daga Iraƙi zuwa ƙarshen wannan shekarar
Shugaba Joe Biden ya ce sojojin yaƙin Amurka za su fita daga Iraƙi a ƙarshen wannan shekarar, amma wasu sojojin za su ci gaba da horar da rundunar sojin Iraƙin.
Sanarwar tasa ta zo ne bayan da Mista Biden ya tattauna da Firai Ministan Iraqi Mustafa al-Kadhimi a fadar White House.
A halin yanzu akwai dakarun Amurka 2,500 a Iraƙi da ke taimaka wa dakarun ƙasar yaƙi da mayaƙan IS da suka rage a ƙasar.
Mai yiwuwa adadin dakarun Amurkar ya kasance yadda yake a yanzu amma ana ganin matakin a matsayin wani yunƙuri na taimakon Firai Ministan na Iraƙi.
Kasancewar Amurka a Iraƙi ya zamo wata babbar matsala tun bayan da aka kashe babban kwamandan Iran Qasem Soleimani da shugaban wata ƙungiyar Musulmi ƴan Shi'a da Iran ke mara wa baya a wani harin Amurka a Bagadaza a shekarar da ta gabata.
Jam'iyyun siyasa da ke goyon bayan Iran sun buƙaci a janye duka dakaru daga haɗin guiwar da Amurka ke jagoranta don yaki da Is, duk da barazanar da kungiyar mai iƙirarin jihadi ke yi.
A wani ɓangaren kuma, Amurka ta zargi masu ta da ƙayar baya ƴan Shi'a da kai hare-haren roka da na jirgi marar matuƙi kan sansanin sojojin Iraƙi da ke karɓar baƙuncin sojojin haɗin guiwa don matsa masu lamba su fice.
Ga shugaban Amurka, sanarwar na alamta ƙarshen wani yaƙin da aka fara tun zamanin tsohon Shugaba George W Bush. A wannan shekarar ce ya sanar da ficewar dakarun Amurka daga Afghanistan.
Dakarun da Amurka ke jagoranta sun shiga Iraƙi a 2003 don ɓarar da mulkin Shugaba Saddam Hussein da kuma kawar da makaman ƙare dangi da aka gano cewa babu su.
Shugaba Bush ya yi alƙawarin samar da "zaman lafiya a Iraƙi", sai dai hakan bai kasance ba illa mummunan yaƙi.
Sojojin yaƙin Amurka sun janye daga baya a 2011. Sai dai sun sake komawa bayan da gwamnatin Iraƙi ta buƙaci su koma bayan shekaru uku lokacin da mayaƙan IS suka ƙwace yankuna da dama na ƙasar.
Bayan da sojojin suka ci galaba a kan IS a Iraƙi a ƙarshen 2017, dakarun Amurka sun ci gaba da zama don tabbatar da cewa IS ba ta farfaɗo ba.
"Rawar da za mu taka a Iraƙi shi ne na ci gaba da horaswa da taimakawa kan ISIS idan ƙungiyar ta dawo," a cewar Mista Biden.
"Amma kawo ƙarshen shekarar nan, ba za mu kasance a ƙasar don yaƙi ba."
Sharhi daga Frank Gardner, wakilin BBC kan tsaro
Tun da aka yi juyin juya hali a Iran a 1979, ta ci gaba da koƙarin fitar da dakarun Amurka daga maƙwabtanta don ta zama mai ƙarfin faɗa a ji a yankin.
Ta yi ƴar nasara a ƙasashen yankin Gulf inda har yanzu a ke cike da ƙin jinin Iran kuma inda rundunar sojin Amurka ke da sansanoni a duka ƙasashen shida.
Amma hamɓarar da gwamnatin Saddam Hussein da Amurka ta jagoranta a Iraƙi ya kawar da barazana mafi girma ga faɗaɗa Iran. ƙasar ta yi nasarar cusa mayaƙan 'yan Shi'a cikin jami'an tsaron Iraƙi kuma ƙawayenta na da ƙarfin faɗa a ji a majalisar dokoki.
Yaƙin basasar Syria ya bayar da kafa ga sojojin Iran su shiga Iraƙi, yayin da a maƙwabciyarta Lebanon, ƙawar Iran, Hezbollah ta zama babbar jigo a kasar.
Iran na ganin idan ta ci gaba da matsa lamba, za ta mayar da yankin Gabas ta Tsakiya ya kasance yankin da bai ishi Amurka kallo ba idan aka zo batun sojoji.
Shi ya sa ta ke yawan kai hare-haren roka kan sansanonin sojin Amurka.
Don haka ga mutane da dama a Iran, yarjejeniyar janye dakarun Amurka daga Iraƙi wani babban mataki ne da ya yi dai-dai.