Hotunan Afirka na mako: 16-22 Yuli 2021 - Bukukuwan sallah da ninƙaya a teku

An wallafa

Ga wasu zaɓaɓɓun hotuna na wasu abubuwan da suka faru a sassan Afirka ko na wasu ƴan nahiyar a sassan duniya a wannan makon.

A man prays in a mosque. His silhouette is seen against the window.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani mutum yana sallah a ranar Talata a wani masallaci a Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya...
A girl has the word 'Eid' daubed on her forehead with face paint.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ita ma wannan yarinyar ta yi adon Babbar Sallah ko Sallar Layya - a wannan rana a Nairobin...
A man leads a goat to be slaughtered during Eid al-Adha in Nairobi, Kenya, on 20 July.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sallar Layya sallah ce da Musulmi a fadin duniya da suka sami iko ke yanka dabbobi don neman yardar Allah.
A family dressed in different colours attend prayers at the Central Mosque in Cameroon's capital, Yaoundé.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Waɗannan iyalan suna zaune a masallaci don yin Sallar idi a ranar Talata a Yawunde, babban birnin Kamaru.
A boy cups his ears during prayers at the mosque.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A washegarin ranar Sallah kuwa a nan wasu ne ke salla a Masallacin Massalikoul Jinaan da ke Dakar a ƙasar Senegal.
Children play at al-Azhar mosque in Cairo, Egypt, on 20 July.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A nan kuma wasu yara ne suke ta wasa da balam-balam da aka yi adon sallah da ita a Masallacin al-Azhar a Alƙahira babban birnin Masar, yayin Sallar Idin Layya.
A girl wearing sunglasses makes the V-sign at the camera.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan yarinyar ta sha ado ana ɗaukarta a hoto a Masallacin Idin da ke Kasuwar Dabbobi ta Kara a Najeriya, ranar Talata.
A view of boats in Conakry, Guinea.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masunta sun gyara tsayuwar tarin kwale-kwalensu a Conakry, babban birnin ƙasar Guinea a ranar Litinin...
A man works on a fishnet in Conakry, Guinea.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hanyar samunsu na raguwa a shekarun baya-bayan nan sakamakon haramta amfani da jiragen ruwan su daga China da sauran ƙasashe a gaɓar tekun Guinea.
Azenaide Carlos of Angola's Handball team holds the ball.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A ranar Alhamis Azenaide Carlos ta Angola ta ƙaddamar da jefa ƙwallon hannu a yayin wani atisaye na Gasar Olympics ta Toyko 2020, wacce aka ɗaga tsawon shekara ɗaya saboda annobar cutar korona.
Beach workers help a man to get into the sea.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani mutum yana shirin shiga yin ninƙaya teku a karon farko a wani gaɓar teku da aka ware don masu lalurar naƙasa a Alexandria na mAsar a ranar Asabar.
Moroccan actress Samah Baricou poses during a photocall for the film "Haut et Fort" (Casablanca Beats).

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar juma'a kuma wata ƴar fim ta Moroko Samah Baricou da ta fito a wani fim na Haut et Fort ta halarci taron Cannes Film Festival a Faransa.
Opponents of Cameroon's President Paul Biya protest against his presence in Geneva, Switzerland.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, "Switzerland na goyon bayan Biya ɗan kama karya" shi ne abin da aka rubuta a jikin kwalin da mutumin nan ya riƙe a yayin wata zanga-zangar nuna adawa da shugaban ƙasar Kamaru da aka yi a Geneva, an ce shugaban ya kan shafe tsawon lokaci a ƙasar da ke nahiyar Turai.
Supporters of presidential candidate Vila Nova celebrate the provisional results of the presidential elections, in Sao Tome, Sao Tome and Principe.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, A São Tomé da Príncipe kuma a ranar Litinin, magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa Vila Nova ke murnar yawan ƙuri'un da yake da su a zagayen farko na zaɓen.

Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka.