Tokyo 2020: Alkaliyar wasa mai sanya hijabi ta farko a gasar Olympics

Sara Gamal on the court

Asalin hoton, Sara Gamal

Bayanan hoto, Sara Gamal ita ce alkaliyar wasa mai sanya hijabi ta farko a gasar Olympics
    • Marubuci, Daga Lebo Diseko
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Religion Correspondent
  • An wallafa

Sara Gamal na da tarin abubuwa na gagarumin ci gaba da ta samu a baya.

Yanzu injiniyar 'yar kasar Masar kuma 'yar wasan kwallon kwando da ta koma alkalancin wasa na shirin kafa tarihi.

Za ta kasance mace Musulma mai saka hijabi ta farko mai alkalancin wasan kwallon kwando a gasar wasan Olympics.

Ba haka kadai ba, ita kan ta tawagar wasan kwallon kwandon da take yi wa alkalancin, shiga gasarta zai kasance na biyu a birnin Tokyo cikin wannan watan na Yuli.

Ana daukar wasan kwallon kwando na 3x3 a matsayin wanda aka fi bugawa a cikin wasannin duniya, wanda ya bunkasa zuwa wasan da akan buga a fadin duniya a lambu da wuraren shakatawa da ake fi sani da Streetball, da Blacktop or Playground Ball.

An kididdige cewa kasashe 182 da mutane fiye da 430,000 a fadin duniya ne ke buga wasan kwallon kwando na 3x3.

Sara kuma za ta kasance Balarabiya ta farko kuma mace 'yar Afirka da ta jagoranci tawagar wasan kwallon kwando a gasar Olympics.

Sara Gamal

Asalin hoton, Sara Gamal

Bayanan hoto, Sara ta ce addininta ya yi tasiri a aikinta na alkalancin wasa
1px transparent line

'Ina iya bakin kokarina'

Sara ta ce zuwa gasar wasan Olympics "cikar buri ne".

Annobar korona na nufin babu alamar samun damar gudanar da gasar wasanni.

"Mun damu matuka kan ko za a gudanar da gasar ko kuma a'a, amma daga karshe ga shi za a yi.''

Iyalanta suka sun cika da alfahari, in ji Sara. Amma ta san cewa ta wannan gagarumin cigaba akwai babban nauyi a kan ta.

"Babban nauyi ne a lokacin da ka wakilci ka bai kan ka kadai ba, amma har da (Afirka da kasashen Larabawa).

"Ba abu ne mai sauki ba, amma ina son ina son yi musu wakilci mai kyau, don haka ina iya bakin kokarina a kai''.

Sara mai sanyin zuciya ce, da murmushi ga kowa. Tana magana da ni ne sa'oi kadan bayan dawowarta gida a kasar Masar daga alkalancin buga wasan kwallon kwando a kasar Romania.

Ta shaida min cewa "a duk lokacin da na samu nasara a kan wani abu kana na yi tunanin cewa babban abu ne, Allah yakan sake bude min wasu sabbin kofofin alkhairi da suka fi na baya.

"A kakar wasan bara, an zabe ni na jagoranci wasan kusa da na karshe ga tawagar wasan kasar Masar ta maza. Wannan wani cigaba ne na karan kan shi.

Wannan kakar wasan kuma Sara ta kara samun cigaba, lokacin da ta yi alkalanci a gasar wasan karshe ta cin Kofin kasar Masar na maza da kuma na Gasar Wasan Kwallon Kwando ta Afirka na mazan.

"Wadannan manyan matakai ne a gare ni, da duka sauran mata masu alkalancin wasa a kasar Masar, saboda shi ne karon farko da mace mai alkalancin wasa ke jagorantar gasar wasan karshe ta maza a kasar.''

Sara Gamal and other referees pose for a picture

Asalin hoton, Sara Gamal

Bayanan hoto, Sara Gamal za ta zama mace Balarabiya kuma 'yar Afrika ta farko da za ta yi alkalancin wasan kwallon kwando a gasar Olympics

Cin tudu biyu

Duk da nasarorin baya-bayan nan da Sara ta samu, shiga cikin gasar wasan Olympics din ta ya dade.

Ya fara tun tana karama, tana kallon yadda 'yayarta ke buga wasan kwallon kwando kana ta kan raka ta zuwa horo. Tana da shekaru biyar kacal Sara ta fara buga wasa, kuma lokacin da ta kai shekara 15 ne ta fara alkalancin wasan.

Sara ta kasance 'yar wasa kuma mai alkalancin wasa har na tsawon shekaru takwas. Ta ce yanke shawarar da ta yin a daina buga wasa kana ta mayar da hankali wajen alkalancin daya daga cikin manyan kalubalenta ne.

"Ba abu ne mai sauki ba idan ka kasance na farko a irin wannan - dole ka nuna hazaka da jarumtaka idan za ka yi.

"Amma idan ka yi Imani da wani abu, dole kuma ka yi Imani da cewa idan ka yi niyyar yin abu, za ka samu nasara".

Sara ta saba daidaita yin ayyuka da dama a lokaci guda, Har yanzu tana aiki a matsayin injiniya, kuma ta yi karatu na tsawon shekaru biyar yayin da ta ke kokarin cimma burinta na wasan kwallon kwando.

Akwai kalubale, ta bayyana, ''amma na samu goyon bayan iyalaina wadanda suka koya min yadda zan daidaita lokacina tsakanin hanyoyi guda biyu''.

Yanzu abokan aikinta na cikin wadanda ke kara karfafa mata gwuiwa.

"Suk an kalli wasannina kana ko shakka babu suna b ani goyon baya a gasar wasan Olympics."

Sara Gamal on the court

Asalin hoton, Sara Gamal

Bayanan hoto, Sara ta ce zuwa Tokyo wani "cikar buri ne"

Taimakon Allah

A daukacin al'amuranta, Sara ta ce addininta ne ke saka ta kasancewa cikin natsuwa.

"Na yi ammana cewa idan na iya bakin kokarina, zan samu kyakkyawan sakamako.

"Dole sai ka yi aiki tukuru. Kana ka ce, '' Na yi iya bakin kokarina'', sauran sai ka bar wa Allah, Shi zai yi maka jagora abinda ka saka a gaba.''

Abinda ta kan yi kenan kafin buga ko wane wasa.

"Na kan yi addu'a in ce,'' Allah ka taimaka min ya zama wannan shi ne wasa ko kuma gasa mafi kyau''.

Imanin da ta yi da addininta ne ya bata damar yanayin yadda take saka kaya a filin wasa.

Sara ita ce mai alkalancin wasan kwallon kwando ta farko da ke saka hijabi a matakin gasar wasan kasa da kasa, bayan sauya doka a shekarar 2017.

Sakamakon, in ji Sara daukacinsa mai kyau ne.

"Wasu 'yan wasan kan ce kayana suna da kyau,'' ta ce.

"Ya yi matukar kyau a gare ni cewa na bude wata hanya ga mata masu alkalancin wasa su kasance masu gaskatawa da jajircewa ga addini da kuma burinsu.''

Ta ce yaran mata masu alkalancin wasan a kasarta sukan rubuta mata, suna cewa sun yi tsammani '' bas u da wata samar zuwa su shiga gasar manyan wasannin ko zagaya fadin duniya''.

"Na kan fada musu za su iya yi fiye da ni. Za ka iya cimma duka burinka a ko ina kake so. Kana da karfin zuciyar da za ka iya yi.

"Babban abin cigaba ne cewa su kan iya yin tunani game da makomarsu a matsayinsu na masu alkalancin wasa tare da ganin cewa muddin suka yi aiki tukuru za su cimma duka burinsu."

Wannan shi ne abinda ta ke so yaran mata Musulmai da suke kallonta a fadin duniya su koya daga irin nasarorin da ta samu, a yayin da suke ganin filin wasanta a Tokyo.

"Mayar da hankalinka wajen kasancewa kan gaba kana ka sa babban buri a gabanka, ta hakan za ka kai ga kololuwar cigaba.

"Na yi amanna cewa mu mata muna da wata mu'ujiza. Muna da karfin zuciya matuka."