Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya suka cimma kan matsalolin yankin
Gwamnonin jihohin yankin arewa maso gabashin Najeriya shida sun gudanar da wani taro kan batutuwan da suka shafi cigaban yankin ciki har da yadda za a magance matsalar tsaro da ke ci wa arewa maso gabas din tuwo a kwarya.
Taron da ya gudana da maraicen jiya talata a Jalingo fadar jihar Taraba inda ya samu halartar gwamnonin na yankin arewa maso gabas kama daga kan na Borno Babagana Umara Zulum da na Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri da na Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya da na Bauchi senata Bala Muhammad da mataimakin gwamnan jihar Yobe Idi Barde da kuma mai masaukin baki Darius Ishaku na Taraba.
Bayan kammala taron gwamnan jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana wa BBC cewa sun duba batutuwa da dama da ke addabar yankin, kuma sun gano bakin zaren warware matsalolin.
Ya ce ''Na farko dai kasan babban abun da ya fi zama kalubale a gare mu shine batun tsaro, don haka mun duba wannan domin mu samu matsaya guda, sannan mun duba batun sufuri a wannan yankin, kuma mun amince cewa za mu samar da kamfanin jirgin sama na wannan yanki don mutanen mu su rika zirga zirga cikin sauki''.
Gwamnan ya kara da cewa sun kuma duba batun samar da wutar lantarki ta Mambila, da kuma harkar noma da ilimi da sauran batutuwan zamantakewa.
A cewarsa batun wutar Mambila mun lura cewa aikin bai taba tsayawa cak ba tun da aka fara shi, amma tunda yanzu mun gane inda matsalolin suke za mu kai koke ga shugaban kasa da kuma majalisar dattawa.
Boko Haram.
Wani batu da gwamnonin suka maida hankali a kan a tattaunawarsu shine ganin sun yi dukkan mai yiwuwa don toshe hanyoyin da Boko Haram ke samun makamai da sauran kayan da suke amfani da shi.
A cewar gwamna Inuwa Yahaya na Gombe ''Mun san cewa ba abun da yake shigowa face sai ya biyo ta hannun mu'amala da mutane, a daga iska haka kawai yake sakkowa ba, don haka za mu hada kai da dukkan jami'an tsaron don tabbatar da cewa mun sanya ido yadda ya kamata''.
Ya ƙara da cewa tuni suka himmatu don ganin jama'a sun ci gaba danoma, musamman a wannan hali da ake ciki da fargabar hare-haren yan Boko Haram ke hana manoma zuwa gonakinsu.
Ya yi watsi da zargin da wasu mutane ke yi na cewa irin wadannan taruka da suke yi na shan shayi ne kawai, la'akari da yadda ake ta gudanar da su amma babu wani sakamakon a zo a gani, yana mai cewa suna da darakta na musamman a kungiyar gwamnonin arewa maso gabas da ke bibiyar manufofin da suke cimmawa don ganin ana aiwatar da su yadda ya kamata